Bismillahir Rahamanir Raheem Alhamdulillahi Rabbil - TopicsExpress



          

Bismillahir Rahamanir Raheem Alhamdulillahi Rabbil alamin Walaqibatu lil muttaqeen Wala wuduwana illa alazzalimin Wassalatu Wassalamu ala kairi khalqil Lahi ajmain Assalamu Alaikun Ayyuhal ikhwa Ina mana fatan alkhairi a wannan ranar ta 10th ga watan Zulhijja, ranar da dukkan musulmin Nijeriya Ke farincikin ganinta, domin itace ranar sallar idin layyah. Allah Ubangiji Ya karba mana dukkan ayyukanmu na alkhairi, Ya yafe mana kurakurenmu. Tunatarwa Ya yanuwa musulmi. Sayyidil waara (SAW) yace : MUTUM BAKWAI SUNA CIKIN INUWAR ALLAH, ARANAR DA BABU WATA INUWA SAI TA ALLAH MADAUKAKIN SARKI: 1. Shugaba mai adalci. Asamu shugaba wanda yadamu da damuwar alumarsa dayake mulka, Ya kasance mai kwatanta adalci ga mitane, kada yazama dan handamization da baba kere, kada yazama azzulumi ga alummar dayake mulka, yazama mai jin tausayin talakawa domin neman niimar wanda Ke sama dashi a mulki Shine Allah Madaukakin Sarki. Koda a gidane a naso mutum yazama adali akan matansa da yayansa, kada ya nuna wariya garesu. Manzon Allah (SAW) yace: kullukum raI wu kullu rain masulun an raiyatihi. Dukkanku masu kiwone kuma kowani mai kiwo zaa tambayeshi gameda abinda aka bashi kiwon 2. Da Matashi wanda ya rayu cikin bautar Allah har ya mutu yana cikin bautan Allah Madaukakin Sarki . Shin haka matasanmu suke yanzu? Duk wayancin matasaanmu kam sai a slow wallahi cuz basuson yin sallah musamman in suna kallon ball, ko kuma suna wani aikinsu na neman duniya. Zakaga matashi maji karfi yana wasa da sallah akan neman duniya, toh wallahi kada yabari duniyar tazamto babu yaje caanma yasamu babu. Allah Ya shiryemu baki daya. 3. Da mutumin da ko yaushe zuciyarsa take taallake da Masallaci. Wanda daga yaji kiran sallah kome yakeyi bari yakeyi yatafi masallaci. Yawancin irin kin sallah a lokutanta yafi yawa ga yankasuwa da maaikatan office. Saikaga dankasuwa indai akwai customer wallahi sai kaga ana sallah a kofar shagonsa ammana shi yana ciki yana damin mutane da surutu. Wallahi hakan bai dai dai bane. Kuma kada muzama kamar tsuntsu a keje lokacinda muke masallaci. Baban Qaseem (SAW) yace: shi munafiki a masallaci kamar tsuntsune acikin keje jira yakeyi kawai yasamu kofa yayi wuf yafita Ammana shi mumini kullun yana son zaman masallaci, yana azkar yana tasbihi da salati ga Annabin Rahama, da kuma yawaita nafilfili 4. Da Mutum biyu wadanda sukayi soyayyar Juna domin Allah. Suka hadu akan haka, kuma suka rabu akan haka. Rabuwa anan bawai sunyi fada bane sabida mace ko wani team ko abin duniya. Aa sai dai kawai ka guji abokinka domin bashi son yin ibada, kuma yayi iya kokarinsa yabari yaki. Ko kuma abokin yazama fasiqi, wanda bashida kunya. Toh kamar yadda mai ahalari yace wa yajibu hijaranahu yazama wajibi a kauracemar. Idan zaa soyayya a yita tsakani da Allah bawaii don kwadayin wani abun duniyaba 5. Da Mutumin da wata Mace Kyakyawa, maabociyar Matsayi ta kirashi Izuwa Fasikanci, amma bai bata hadin kai ba yace: NI INA JIN TSORON ALLAH. Yanzu haka muke? Yawancin yanzu kamma muke zuwa mu nemi matan bada sonsuba, gayu suna fyade, kwartanci. Gayu a gyara hali don Allah 6. Da Mutumin da zaiyi sadaka ya boyeta, har sai da hannunsa na haggu bai san abinda hannunsa na dama ya bayar ba. Toh wallahi mitanenmu sun zama masu yi don a gani, riya tayi yawa, inzaayi sadaka sai dai ayi don ganin idon mitane 7. Da Mutumin da ya tuna Allah, shi kadai aboye, Har idanunsa suka zubar da hawaye. (aduba Sahihul bukhary hadisi na 660, sahihu Muslim, hadisi na 1,031). Allah Yadarta damu Yasa muna cikin wadanda Allah Yayi gafara a wannan shekarar, Yasa kuma kwanakinmu nagaba su zamto sunfi na baya albarka. Ya Allah Ka karemu daga aikata duk wani kabaira dazai jawo mana fuskantar fushinKa.
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 06:39:57 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015