DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA - TopicsExpress



          

DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI Wallafar: Shaikh Prof. Umar Muhammad Labdo *** Darasi Na (17) *** ========================= HAKIKANIN ALAKAR AHALUL BAITI DA SAHABBAI: Abinda Ahalus Sunna suka sani, kuma suke quduri da shi, shi ne cewa babu abinda yake tsakanin Ahalul Baiti da Sahabbai sai soyayya da kauna da ban girma. Kuma wannan kuduri na Ahalus Sunna shi ne yake dacewa da abinda Allah ya ba da labari da shi a cikin littafinsa mai tsarki da abinda yake cikin littafan Hadisi ingantattu da sauran littafan magabata na gari. Littafan Ahalus Sunna suna cike da bayanin girmamawar Abubakar da Umar, Allah ya yarda da su, ga Ali(RA), da ma sauran dangin Annabi Banu Hashim da Banul Muddalib baki daya, da yadda suka fifita shi, suka kwarzanta shi, suka sanya shi gaba da kowa a wajen martabawa da darajantawa. Kuma abu ne da ya tabbata a tarihi cewa Sarkin Musulmi Umar ya fifita Ahalul Baiti a tsarinsa na rabon ganima da dukiyar kasa ga al’umma. A lokacin da ya rattaba sunaye a Diwani don wannan manufa, ya gabatar da Banu Hashim, sa’an nan Banul Muddalib. Ya gabatar da Abbas baffan Annabi, da Ali da Hassan da Hussaini, kuma ya ba su kaso sama da na kowa. Ya ma fifita Usama binu Zaid binu Harisa, wanda da ne na bawan Annabi da ya ‘yanta, a bisa dansa Abdullahi. Wannan duka saboda girmamawa ga Annabi(SAW) da kiyaye hakkinsa. Haka nan Ahalus Sunna baki dayansu, tun daga zamanin Sahabbai har ya zuwa yau, babu mai kin Ali(RA) ko wani daga alayen Annabi(SAW). Maimakon haka, dukkaninsu suna kaunar su, suna daraja su, kuma suna bautawa Allah da son su. Idan mai karatu yana bukatar hujja a kan wannan, sai ya duba yadda sunayen Ali da Fatima da Hassan da Hussaini suka bazu a cikin al’ummarmu, ina nufin Musulmin Nijeriya. Har ma ya zama al’ada a wajen mu inda duk aka haifi tagwaye maza to ba wata magana sunansu Hassan da Hussaini. Kamar yadda Hausawa suka kware wajen nau’anta sunan Fatima saboda yawansa. Su ce Fadima, Fati, Binta, Batulu, Zahra ko Zahara’u, da sauransu. Babu wani suna da ya samu haka a tsakanin Musulmin Nijeriya Ahalus Sunna. Wannan kuma yana nuna karyar ‘yan Shi’a, kuma ya isa ya sa su kunya in da suna da kunya. Kuma kamar yadda sauran Sahabbai suke son Ahalul Baiti, haka su ma Ahalul Baiti suke son Sahabbai baki dayansu kuma suke girmama su, musamman dai Khalifofi guda uku, watau Abubakar da Umar da Usman, da kuma uwayen muminai, matan Manzon Allah(SAW), Allah ya yarda da su baki daya. Ya tabbata cikin littafan Ahalus Sunna cewa Ali da ‘ya’yansa Hassan da Hussaini, Allah ya yarda da su, suna matukar nuna so da kauna da girmamawa ga Abubakar da Umar da Usman, kuma daga alamun sonsu gare su duka sun sawa ‘ya’yansu sunayensu domin tunawa da su, kamar yadda za mu fayyace a nan gaba a cikin wannan littafi, in Allah ya yarda. Kamar yadda sonsu da kaunarsu ga uwayen muminai ya shahara kuma suka sanya sunayensu ga diyansu mata. Mai son ya tabbatar da wannan sai ya koma ga littafan Ahalus Sunna ingatattu, kamar Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Kitabus Sunna na Abdullahi binu Ahmad binu Hanbal da Kitabus Sunna na Khallal da Kitabus Sunna na Ibnu Baddata da Kitabus Sunna na Ajuri da Kitabus Sunna na Lalika’i da Kitabul Asma’i was Sifat na Baihaqi da Kitab Fada’ilis Sahabah na Imam Ahmad da Albidaya wal Nihaya na Ibnu Kathir da Minhajus Sunnah na Ibnu Taimiya, da gomomi da daruruwan littafan Hadisi da Tafsiri da Sirah wadanda suke tabbatar da kyawawan halaye na Ahalul Baiti da Sahabbai da soyayya da kauna da rahama da jin kai da ban girma dake tsakaninsu wanda yake tabbatar da cewa lallai tabbas su almajiran mafificin annabawa ne wadanda suka tsarkaka da koyarwarsa. Amma masu sukan Manzon Allah(SAW) ta hanyar sifanta manyan almajiransa da mabiyansa da sifofin ‘yan daba masu kin juna da keta ga juna da wulakanta juna, to muna rokon Allah ya turmuza hancinsu a kasa, ya maida musu da mugun nufinsu a kansu. Mu tara a darasi na gaba, in sha Allah.
Posted on: Thu, 16 Jan 2014 20:58:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015