DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA - TopicsExpress



          

DANGANTAKA DA AURATAYYA TSAKANIN AHALUL BAITI DA SAHABBAI Wallafar: Shaikh Prof. Umar Muhammad Labdo *** Darasi Na Ashirin Da Uku (23) *** ========================= NASABA DA AURATAYYAR ANNABI(SAW) (3) Cigaba: (8) JUWAIRIYYA DIYAR HARITH(RA) Juwairiyya diyar Harith dan Abu Dirar dan Habib dan Juzaima ta fito daga Banul Musdaliq, wani reshe na Banu Khuza’a. Mahaifinta Harith da mijinta na farko Musafih binu Safwan shugabanni ne a cikin wannan kabilar. Kabilar tana da karfi ainun kuma ta nuna matukar adawa ga Musulunci. Lokacin da Allah ya ba Musulmi galaba a kanta, a yakin da aka fi sani da Gazawatu Banil Musdaliq, an kashe mijin Juwairiyya da ubanta kuma aka kame da yawa daga cikin ‘yan kabilarta maza da mata a matsayin ganima, ciki har da ita kanta. Bayan da Ma’aiki(SAW) ya raba ganima, Juwairiyya ta fada a rabon Thabit binu Qais wanda ya yi mata mukataba, watau ya ba ta dama ta fanshi kanta. Sai ta zo wurin Annabi(SAW) ta yi masa bayanin kanta da matsayinta a cikin mutanenta. Sai Manzo(SAW) ya biya fansarta, sa’an nan ya aure ta. Kuma wannan aure ya zama alheri ga Musulunci; domin lokacin da labarinsa ya watsu sai dukkanin Sahabbai suka ‘yanta wadanda suke hannunsu daga mutanenta. Suka ce ba za mu bautar da surukan Annabi ba. Wannan karamci da Ma’aiki ya nuna tare da Sahabbansa ya faranta ran ‘yan kabilar Banul Musdaliq, don haka sai suka shiga Musulunci baki dayansu, kuma gabar da take tsakaninsu da Musulmi ta juye ta zama ‘yan uwantaka da soyayya. Annabi(SAW) ya auri Juwairiyya a shekara ta biyar bayan hijira kuma ta rasu a shekara ta 56, tana da shekaru hamsin da shida a duniya. Marwan Binul Hakam, gwamnan Madina a zamanin Sarkin Musulmi Mu’awiyya, shi ya sallace ta. (9) SAFIYYA DIYAR HUYAYYU(RA) Safiyya diyar Huyayyu dan Akhdab ta fito daga kabilun Yahudawan Madina. Lokacin da Annabi(SAW) ya yi hijira, akwai gidaje uku fitattu na Yahudawa a Madina. Su ne Banu Qainuka’a da Banu Quraiza da Banu Nadir. Safiyya ta fito daga Banu Quraiza. Da isowar Ma’aikin Allah(SAW) Madina ya kulla yarjejeniyar zaman lafiya da wadannan Yahudawa, amma sai suka karya yarjejeniyar kuma suka saba alkawari. Don haka Annabi(SAW) ya fitar da su daga Madina, sai suka koma wajen ‘yan uwansu a Khaibar, inda suka ci gaba da kullawa Musulunci makarkashiya da makirci. Wannan ya sa a shekara ta bakwai bayan hijira, Annabi(SAW) ya yake su kuma ya yi galaba a kansu a mashahuriyar gwabzawar da ake cewa Yakin Khaibar. A wannan yakin aka kashe mijin Safiyya kuma aka kame ta a matsayin ganima. Da aka raba ganima sai ta fada a rabon Dahiyya binu Khalifa Alkalbi, amma kasancewarta diyar shugaba ce kuma matar shugaba, sai Manzo(SAW) ya saye ta daga wajen Dahiyya, ya ‘yanta ta kuma ya aure ta a matsayin wata hikima ta siyasa domin ya jawo hankalin danginta su shiga Musulunci. Kafin Ma’aikin Allah, Safiyya ta auri mazaje biyu: Salam binu Mishkan Alkhuza’i, wanda ya sake ta, da Rabi’u binu Abil Hakik Alnadiri wanda aka kashe shi yana tare da ita. Wannan aure ya hada dangantaka tsakanin Annabi(SAW) da kabilun Yahudawa na kasar Larabawa kamar yadda ya rage kaifin kiyayya tsakanin Yahudu da Musulmi. Safiyya, Allah ya kara mata yarda, ta rasu a shekara ta 52 bayan hijira a Madina. (10) UMMU HABIBA DIYAR ABU SUFYAN(RA) Sunanta Ramla diyar Abu Sufyan dan Harbu dan Umayya na gidan Banu Umayya. Mahaifiyarta, Safiyya diyar Abul As dan Umayya, goggon Sarkin Musulmi Usman binu Affan ce. Mijinta na fari shi ne Ubaidullahi binu Jahash, kuma ta haifa masa diya, Habiba. Ubaidullahi ya musulunta tare da matarsa kuma ya yi hijira da ita zuwa Habasha. Amma a yayin da suke can, sai ya yi ridda ya shiga addinin Nasara, ita kuwa Ummu Habiba ta tabbata a kan Musuluncinta. Wannan dalili ya raba su aure. Lokacin da Annabi(SAW) ya ji labari, sai ya aike wajen Sarkin Habasha, Najashi, ya umarce shi da ya aura masa ita. Najashi ya daura auren, ya ba Ummu Habiba sadaki dinare dari hudu. Mai karatu zai tuna cewa Najashi ya musulunta kuma shi ne a lokacin da ya rasu, Annabi(SAW) ya yi masa Sallah daga nesa (salatul ga’ib) a Madina. A lokacin da Ma’aiki(SAW) ya auri Ummu Habiba, ubanta Abu Sufyan shi ne yake jagorantar mushirikan Makka a yakinsu da Musulunci. Uban nata ya zo Madina a wani yunkuri na neman sulhu jim kadan kafin Annabi(SAW) ya ci Makka, kuma ya shiga wajen diyarsa don ya gaisa da ita. Lokacin da ya so ya zauna kan shimfidar Annabi(SAW), Ummu Habiba ta yi wuf ta janye shimfidar, ta fada masa cewa shi mushiriki ne don haka bai kamata ya zauna bisa shimfidar Annabi. Ummu Habiba, Allah ya kara mata yarda, ta rasu a shekara ta 44 bayan hijira, a zamanin khilafar Mu’awiyya dan uwanta. In sha Allah, a darasi na gaba za mu ji cigaba.
Posted on: Thu, 23 Jan 2014 21:17:16 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015