DAREN (15) SHINE DAREN NISFU RAMADAN DA RANAR (15) GA RAMADAN DUK - TopicsExpress



          

DAREN (15) SHINE DAREN NISFU RAMADAN DA RANAR (15) GA RAMADAN DUK SUNADA FALALA. Daren yau shine Daren Nisfu Ramadan akwai ayyuka a cikinsa 1- Wanka 2- Ziyarar Imamu Husain 3- Sallah Raka‘a (6) anaso a Karanta Fatiya da Yaseen da Tabara da Kulhuwallahu kafa daidai a kowace Raka‘a 4- Sallah Raka‘a (100) Fatiya (1) Kuhuwallahu kafa(10) a kowace Raka‘a RANAR (15) GA RAMADAN, tayi daidai da Ranar da aka haifi Imam Hasan Almujtaba (AS) Dan Aley bn Abey Dalib Yar‘Fatima Yar‘ Manzan Allah (S) Sadaka tanada Dimbim Lada Musamman a wannan hali da ake ciki ana iya duba Raunana daga cikin Makota ayi musu Alkhairi Allah (T) zaiyi kyakkyawan Sakamako A Duniya da Lahira Allah ya sadamu da Alkhairan dake cikin wannan Dare da Gobe yabiya mana bukatummu wadanda duke maslahane a garemu, ina yimuku Barka da shan Ruwa.
Posted on: Mon, 22 Jul 2013 19:49:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015