*************** ********** Daga muadh dan jabal (R.A) - TopicsExpress



          

*************** ********** Daga muadh dan jabal (R.A) kuma daga Annabi [S.A.W] Ya ce:> Babu wata mace da za ta cuci mijinta a duniya face sai matarsa ta cikin hurulaini (wato matarsa ta aljannah) ta ce: kada ki cuce shi yake laananniya, shi bako ne kedai ya kusan rabuwa dake zuwa garemu. BAYANIN WANNAN HADISINN 1-Yana nuna mana haramci mace ta cuci mijinta. 2-Matan Aljannah suna bakin ciki da kishi akan ganin an cuci mijin da Allah zai hada su dashi a aljannah. 3-Kuma matan Aljannah suna marmarin zuwan mazajensu. 4-Kuma Ishara ga cewa zaman duniya zama ne na bakunta, saboda haka ya kamata mutum ya dauki guzuri a cikinta domin zaman gidan lahira. Ya ALLAH muna roqanka kashiryi mata masu musgunawa mazajansu, suma mazan kataimake su wajan taimakawa iyalinsu da kuma basu hakkin su yadda ya kamata.
Posted on: Thu, 31 Oct 2013 17:30:22 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015