Dan Sanda VS Lauya. Wani dan sanda ne ta hado shi da - TopicsExpress



          

Dan Sanda VS Lauya. Wani dan sanda ne ta hado shi da wani lauya, a Banki a lokacin kowannensu yana son cire kudi a akwatin kudi me amfani da kati (ATM). Dan sanda yazo da bindigarsa ya shige gaban lauya zai cire kudi, sai lauya yace dashi baka isa ba, domin nine a gabanka. Sai rigima ta kaure a tsakaninsu, wanda takai har gaban (DPO), da DPO ya tambayi dan SANDA me yake faruwa? Dan SANDA yace Wannan mutumin ne ya ganni a layin (ATM) naje ni cire kudi, sai yake kokarin kwace min bindiga ta DPO, ya tambayo lauya anyi haka? sai yace eh anyi haka, kuma nayi hakanne domin nace dashi kada ya shige gaban mutanen da ya tarar, domin ni Lauya ne me kare hakkin Biladama, budar bakinsa yace dani Alkalin alkalai (Chief Judge) Yaci Babarsa. Dan haka ni yanzu a tura mu kotu, domin a matsayin mu na lauyoyi baza mu taba barin a zagi (Chief Judge) ba. Waye ne yafi iya SHARRI? Muhsin
Posted on: Sat, 16 Nov 2013 16:35:48 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015