Daren Farko Kamar yadda aka saba a al’adance, bayan ‘yan - TopicsExpress



          

Daren Farko Kamar yadda aka saba a al’adance, bayan ‘yan rakon Amarya sun gama ‘yan nasihohinsu suka tashi suka fita, na bi bayansu na rufe qofar gida, gabana yana faduwa haka na juyo na taho wajen Amaryata Ummul Adfal, wacce har yanzu kanta yake qunshe cikin mayafi tun lokacin da ‘yan rakon ango suke nan. Jin motshin shigowa ta yasa ta dago kai dan ta tabbatar sun riga sun tafi, ‘Assalamu Alaikum’ nace da ita ina mai murmushi a gareta, ‘amin wa alaika assalam’ ta amsa mini itama tana mai rama lallausan murmushi a gareni. Naje na zauna kusa da ita, sannan muka fara gabatar da abinda mukayi watanni muna koyawa kanmu domin wannan rana, ga maganganun da muka yi: Ummul Adfal: O ni ‘yar gidan babana, wannan shine Daren Farko, na kasance ina mai tsoron daren da zai kaini zuwa ga wani ‘dan Adam daban, zuwa wata rayuwa sabuwa! Abul Adfal: Daren farko kenan, na canji mai alkhairi a rayuwata, wannan shine darena da naki, saboda haka kada ki tasar mana hankalin daren, bari in sa hannuna a kan goshinki dan inyi mana addu’a kuma in roqa mana Allah SWT da addu’o’i masu yalwa, kamar yadda yazo daga Manzon Allah S.A.W inda yake cewa: “Idan ‘dayanku ya auri mace, to ya dafa goshinta ya roqi Allah SWT kuma yayi addu’ar samun albarka, kuma yace “ALLAHUMMA INNI AS’ALUKA MIN KHAIRIHA, WA KHAIRI MA JABALTAHA ALAYYA, WA A’UZU BIKA MIN SHARRIHA, WA SHARRI MA JABALTAHA ALAYYA” “YA ALLAH INA ROQONKA ALKHAIRIN DA YAKE TARE DA ITA, DA ALKHAIRIN ABINDA KA DORATA A KAINA DASHI, KUMA INA NEMAN TSARINKA DA SHARRIN DAKE TARE DA ITA, DA KUMA SHARRIN ABINDA KA DORATA A KAINA DASHI” Ummul Adfal: Ina roqonka da ka tafiyar da wannan dare tare dani cikin nutsuwa a matsayina na wacce kake qauna, kuma matarka tunda wannan dare ba irin sauran darare bane, dare ne wanda zaiyi wahala na mance dashi, kuma zanso daren yakasnce mai cike da so da qauna Abul Adfal: Abu mafi muhimmanci a gareni shine da ki zamo cikin farin ciki, saboda haka bari in lullubeki da kalamai masu dadi, sannan in baki wannan kayan marmarin da waccan kazar, saboda haka ki nutsu kuma ki tuna fadar Allah SWT “Kuma da ambaton Allah ne zuciyoyi suke nutsuwa” Ummul Adfal: “Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21) Abul Adfal: Sadaqallahul Aziim. Kuma Allah ya albarkaceki gareni, ya ke wacce hankalina da zuciyata da tunanina da ruhina suka zabar min, duk abinda na mallaka ya zama mallakarki, haka ne ko? Da fatan komai zai daidaitu zuwa gareki ki samu nutsuwa. Sannan yake jarumata kuma matata, tun daga wannan dare da kuma sauran darare, za muyi Sallah raka’ biyu gajeru, kuma mu roqi Allah Mai Girma da Daukaka, dan kuwa kusanci daga Allah yake, rabuwar kai kuma daga shaidanne Ummul Adfal : Ina neman tsari da shaidan la’ananne, wanda yake son yasa mu qi abinda Allah ya halatta mana. Abul Adfal: Kinyi gaskiya, saboda haka tashi muyi Salah sannan muyi wannan addu’ar: “Yaa Allah kayi albarka a gareni cikin iyalina, kuma ka albarkace ni ma iyalina” Ummul Adfal: Abinda ya kwantar min da zuciyata da raina a wanan dare shine da mijina ya kasance daga cikin muminai masu tsoron Allah, kuma shiryayyu da shiriyar Allah SWT da Manzonsa Muhammad S.A.W, kuma zuciyarsa mai umarni da hasken da baya kuma bazai gushe ba. Abul Adfal: Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya sauwaqa mini al’amarina ni da matata a cikin wannan dare namu na farko, ba abinda zance daya wuce fadar Annabi S.A.W “Idan dayanku ya tara da iyalinsa, to yayi mata adalci ya kyautata mata, idan ya biya buqatarsa kafin ta biya tata, to kada ya barta har sai itama ta biya buqatarta” Ummul Adfal: Ya Allah ka sa wannan dare nawa DAREN FARKO a cikin rayuwata da rayuwar mijina ya zamo mai albarka, kuma shine daren da ya hada ruhinmu waje daya, kuma muna qoqarin samar da iyali masu tarbiyya da taimakonka ya Ubangjijn talikai Abul Adfal: Ya matata mai albarka, zaki kasance cikin jin dadi a wannan dare da yardar Allah SWT, kiyi buri a tare dani na Allah ya rubuta mana farin ciki da annashuwa a cikin sauran shafukan rayuwarmu kuma ya qara kusanci da hadin kai a tsakaninmu Ummul Adfal: Amin yaa Rabbal Aalmin, ya Allah kasa mu zama masu jure duk wani abin qi da damuwa da suke zuwa a cikin rayuwar aure, kuma ka bamu ikon kyautatawa da farantawa juna, da bada haqqoqin aure yadda ya kamata Abul Adfal: Da taimakon Allah SWT ni dake muna kan hanyar alkhairi da so da qauna, zanyi iya qoqarina wajen ganin na tsallakar da jigin ruwan rayuwarmu zuwa gabar AMANA DA GASKIYA, kuma kin gama kyautatawa a cikin komai , Allah yayi miki albarka Ummul Adfal: Amin!!! Daga nan muka tashi muka yi alwala, nayi mana jagaba muka yi Sallah raka’a biyu tare da addu’o’in neman alkhairi. Daga inda nake a zaune na juyo wajen Ummul Adfal dake kan dardumar da muka idar da Sallah, a hankali na bi da hannuna ta kan dardumar na riqe hannunta; wani irin kallo mai gusar da hankali da Ummul Adfal tai mini yasa daga nan ban qara sanin abinda ke faruwa ba! . . .mu hadu a kashi na biyu! ==========admin 001
Posted on: Thu, 03 Oct 2013 19:44:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015