Dr. Mansur Sokoto ME YA FARU A KARBALA 30 Halin Da - TopicsExpress



          

Dr. Mansur Sokoto ME YA FARU A KARBALA 30 Halin Da Ake Ciki A Makka. Rundunar Husain bn Numair wacce take tsare da Ibnuz Zubair da jamaarsa suna can suna dako a wajen birnin Makka, ba su samu labarin mutuwar sarki Yazidu ba sai bayan sati 3 cur. Abu kadan ya rage wannan runduna ta hada kai da Ibnuz Zubair bayan da suka samu wannan labari. Amma abinda ya kawo cikas shine, bin Numair ya nemi ya dora hannunsa a kan na Ibnuz Zubair ya yi masa caffa amma da sharadin su yafe duk jinainan da suka gudana a baya; a zauna lafiya. Shi kuma Ibnuz Zubair (R.A) sai ya ki amincewa da wannan sharadi. A nan ne bin Numair ya juya yana nadama, ya ce, Dubi yadda nake kiran sa zuwa sarauta yana neman ci gaba da fitina. Ashe dai Allah bai nufe shi da zama sarki na hakikani ba. A birnin Dimashka an sha takaddama sosai bayan mutuwar Yazid a kan wa zai gaje shi tunda shi bai bar wasici ba. Daga bisani dai aka nada dansa Muawiya karami. Amma ina dadin mulki a lokacin tashin hankali? Ba da jimawa ba shi kuma ya yi murabus ya bar karagar sarauta wayam ba mai bukata. A nan ne Umawiyyawa suka bukaci su je su sasanta da Ibnuz Zubair suyi ma sa mubayaa a Makka. Kuma sai dai madaukakin sarki ya hukunta nadin Marwan bin al-Hakam bayan sun jitu a kan sa. Shine kuma wanda sarautar ta ci gaba daga bisani a cikin zuriyarsa.
Posted on: Thu, 31 Oct 2013 12:57:19 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015