FALALAR TAFIYA MASALLACIN JUMA‘A DA WURI --------------- - TopicsExpress



          

FALALAR TAFIYA MASALLACIN JUMA‘A DA WURI --------------- --------------- Bismillahir-Rah manir-Rahim --------------- --------------- Lallai tafiya Masallacin Juma‘a da wuri yana da lada hawa-hawa (Step by Step). Kamar yadda Hadithi ya nuna: Daga Abu Hurairah (S.A.) yace: Manzon Allah (S.A.W.) yace: ((Duk wanda yayi wanka ranar Juma‘a, sannan ya tafi zuwa (Sallar Juma‘a) a Sa‘a ta farko, kamar wanda yayi sadaka da Raqumi ne, na Sa‘a ta biyu, kamar wanda yayi sadaka da Bijimin Sa ne, na Sa‘a ta uku, kamar wanda yayi sadaka da Rago ne, na Sa‘a ta hud‘u, kamar wanda yayi sadaka da Zakara ne, yayin da wanda ya tafi a Sa‘a ta biyar, to, kamar wanda yayi sadaka da Qwai ne, da zarar Liman ya fito ya hau Mimbari shike nan sai Mala‘iku su (rufe littafin rubutu) su shiga cikin Masallaci domin sauraron khuduba)). (Bukhari: 881, Muslim: 850). Duk wanda ya zo bayan sa‘o‘innan to, dukkan darajojin sun wuce shi sai dai ya samu ladan Sallar Juma‘a. ALLAH ya bamu ikon tafiya da wuri. (Ameen)
Posted on: Fri, 12 Jul 2013 15:46:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015