FALALAR WATAN MUHARRAM : An karbo daga Anas R.T.A cewa, wanda - TopicsExpress



          

FALALAR WATAN MUHARRAM : An karbo daga Anas R.T.A cewa, wanda yayi Azumi ranar Jumaa ta farko ga watan Muharram Allah zai gafar ta masa laifin sa baki daya. Manzo Allah ( S.A.W) yace wanda yayi Azumi uku a watan Muharram wato Alhamis, Jumaa da Asabar Allah zai rubuta masa Ibadar shekara dari tara. Haka wanda ya Azumci wuni daya a watan Muharram ya kasan ce ko wane wuni daya ladan kwana 30. Manzon Allah (S.A.W) yace wanda yai Azumi tun daga ranar 1 ga watan zuwa 10 ga watan Muharram shine ranar Ashura, Allah zai gadar masa da AlJannar Fiddausi Madaukakiya. Wanda ya Azumci Ashura Allah zai bashi ladan Hajj dubu da umara dubu za kuma a rubuta masa ladan shahidai dubu za kuma a rubuta masa ladan abinda ya fito daga mahudar rana zuwa mafadar ta zai kasance kamar wanda ya yanta kuyangar Annabi Ismaila (AS) guda dubu zaa gina mai dakuna a gidan AlJanna guda dubu sabain, Allah ya haramta wuta baza taci namansa ba. Manzon Allah (S.A.W) yace wanda yai Azumin Ashura zaa bashi ladan Malaika dubu goma. Wanda ya shayar da mumini ranar Ashura abin sha shima Allah zai shayar dashi da ruwa ranar kishirwa mai girma ba zai sake jin kishirwa ba har abada kuma ya kasance kamar bai taba sabon Allah ba tunda ya shigo duniya. Wanda ya bada sadaka ranar Ashura kamar ya bawa dukkan almajiran duniya sadaka ne. Wanda yai wanka ya tsarkaka ran Ashura ba zai rashin lfy ba a wannan shekarar sai dai in ta mutuwa ce. Wanda ya shafi kan maraya ran Ashura maana yai masa wata kyauta wacce marayan yaji dadi kamar ya kyautatawa marayun yayan Annabi Adamu ne baki dayansu. Haka wanda ya gaida mara lfy a ran Ashura kamar ya gaida yayan Annabi Adamu baki dayansu ne Ranar Ashura rana ce da Allah ya halicci Alarshi, Lauhul Mahfuz da Alkalami, rana ce wacce Allah ya halicci Malaika Jibrilu a cikinta. Ranar Ashura ce aka daga Annabi Isah zuwa sama, ranar Ashura kuma za ai tashin Alkiyama. FA IDA wanda yayi sallah rakaa 4 ran Ashura a kowacce raka a ya karanta fatiha 1 da Qulhuwallahu 50 in yayi sallama Allah zai gafarta masa laifinsa na shekara 50. Manzon Allah yace wanda ya karanta Qulhuwallahu kafa dubu a ran wunin Ashura Allah zai dube shi da idon Rahama kuma za a rubuta sunansa a cikin sunayen Siddikai. Allah yasa mu dace, ina fatan duk wanda ya karanta sakon nan zai tura wa Alummar Annabi Ubangiji ya karbo ibadun mu Amin.
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 19:38:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015