FILIN AQIDAR AHLUSSUNNAH WAL JAMA’A TARE DA - TopicsExpress



          

FILIN AQIDAR AHLUSSUNNAH WAL JAMA’A TARE DA LITTAFIN: TAUHIDI HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA NA SHAYKH (DR) UMAR MUHAMMAD LABDO Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci Jami’ar Usmanu Dandofiyo, Sakwato MAI RUBUTU: UMMU ABDILLAH ZARIA HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA //15 **ILLOLIN SHIRKA** Shirka tana da illoli masu yawa a rayuwar al’ummai da daidaikun mutane. Ga wasu daga cikinsu: (1) Shirka kaskanci ne da wulakanci ga bil Adama. Allah Madauki Ya halicci mutane, ya girmama su, Ya daukaka su, Ya fifita su, a kan yawancin halittarsa. Ya ce, «Kuma lalle ne Mun girmama ‘yan Adam, kuma Muka dauke su a cikin kasa da taku, kuma Muka azurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda muka halitta, fifitawa» (Suratul Isra’i: 70). Saboda haka, bayan wannan girmamawa da daukakawa da fifitawa, idan dan Adam ya bautawa wata halitta, wacce ba ta kai ya shi ba, kamar dabbobi da duwatsu ko itace, to lalle wannan ba karamar wulakanci ba ce ga kansa. Dan Adam shi ne shugaban halitta a bayan kasa, kuma shi aka horewa kome, don haka bai kamata ya bautawa kowa sai Allah da halicce shi. (2) Shirka mafakar camfe-camfe ce da almarori. Mai shirka yana kudure cewa akwai wani mai iko ban da Allah. Yana girmama, kuma yana tsoron abubuwa kamar gumaka, aljanu da shaidanu, mamata da dodanni da sauransu. Don haka hankalinsa ya zama yana karbar duk wata bankaura a soki-burutsu, camfe-camfe da almarori, tsibbu da surkulle, kuma yana gaskata maganganun bokaye, ‘yan duba, masu bugun kasa da miyagun Malamai. (3) Shirka tana kawo tsoro da damuwa masu hana zuciya nishadi. Domin mutumin da yake karbar camfe-camfe da almarori, kuma yana gaskata karyace-karyecemakaryata, to zuciyarsa za ta cika da tsoro na ba gaira ba dalili, saboda ya dogara ga iyayen gijin karya wadanda ba sa iya amfanar kansu ko su ijewa kansu sharri, balle su yiwa wani. Allah Madaukai Yana cewa, “Za mu jefa tsoro a cikin zukatan wadanda suka kafirta, saboda shirkan da suke yi da Allah game da abinda bai saukar da wani dalili ba game da shi.” (Suratul Ali Imran: 151). (4) Shirka tana hana shagala da aiki na gari. Domin tana koyawa masu yin ta su dogara ga ceton masu ceto, da girman masu girma, da alfarmar masu alfarma. Sai ka ji suna cewa da wani bawa, Annabi ko Waliyi ko Shaihi, ya tuna da su ranar shiga jirginsa! Ko kuma wai suna cikin aljihunsa! Alhali Manzon Allah (SAW) da kansa yana fadawa diyarsa, “Ya ke Fatimah diyar Muhammad, ki tambaye ni a cikin dukiyata abinda kike so, ba ni amfana miki kome ga barin Allah.” (Bukhari). (5) Shirka tana raba kan al’umma. Shirka bautawa iyayen giji dabam daban ne, da son su, da jin tsoron su, da girmama su. Sai ya zama zukatan al’umma sun rarraba, kowa zuciyarsa na tare da abin bautarsa. Wannan kuwa shi ne babban dalilin rarrabuwar kawuna, domin haduwa a kan Akida guda shi ne hadin kai na gaskiya, ba hada baki ba na munafinci. Don haka Allah Mabuwayi yake yi mana wannan gargadi : «Kuma kada ku kasance daga Mushrikai. Watau wadanda suka rarraba addininsu kuma suka kasance kungiya-kungiya, ko wace kungiya tana mai farin ciki da abinda ke a gare ta » (Suratul Rum : 31-32). In sha Allah, zamu ji RABE-RABNE SHIRKA cikin littafin “HAKKIN ALLAH A KAN BAYINSA” na Shaykh (Professor) Umar Muhammad Labdo.
Posted on: Tue, 10 Sep 2013 20:50:22 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015