FILIN SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAH) TARE DA - TopicsExpress



          

FILIN SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAH) TARE DA LITTAFIN: AL-AKIDATUSSAHI HAT, BI MUWAFAKATUS SHARI’A NA SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI WANDA YA FASSARA: ALHAJI INUWA BABA (MFR) Almajirin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi FCT. Abuja Nigeria. MAI RUBUTU: UMMU ABDILLAH ZARIA HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’AH ///06 BAYANI A KAN IMAN (1) Imani shi ne gaskatawa a zuciya da kuma tabbatarwa a aikatace cewa duk abin da ya zo daga Annabi Muhammad mai tsira da aminci, gaskiya ne. Kuma shi Imani abu daya ne, kuma daidai wa daida suke, fifiko kawai yana karuwa ne da tsoron Allah da kuma sabawa son zuciya, da kuma abinda yake mafifici wajen bin Allah. Saboda haka su muminai wajen fifikonsu kamar gani ne, don kuwa wani ganinsa mai karfi ne, kuma wani ganinsa mai rauni ne kamar mai sa tabarau ga mai raunin gani da wanda ba ya sawa wajen ganin, to haka imani yake. Haka kuma daidaituwa wajen imani, wasu daga mutane imaninsu wajen kalmar LAILAHA ILLALLAHU kamar rana yake, kuma wasu kamar wata ne da kuma taurari wajen haske na imani. Ammakuma wasu kamar fitila yake, mai haske da marar haske, wajen imaninsu. Don haka a ranar tashin Kiyama haka za a ga wasu haskensu na imani ya fi wasu. Duk lokacin da wannan haske ya yi rauni sai a ga sha’awe-sha’awe ya sa ya yi rauni, to, amma ga wasu sai ya yi ta karuwa. Saboda haka duk lokacin da imani ya yi haske sai ka ga hasken ya koma wasu sha’awe-sha’awe har imani ya yi ta karuwa kamar wutar daji da ta sami dama. To wannan shi ne wanda gaskiyar Tauhidinsata tabbata. Wanda ya gane wannan zai fahimci fadar Annabi mai tsira da amincin Allah da ya ce: « “La’illah-illal ahu.” Da neman yardar Allah ga fadin haka » (Bukhari da Muslim). Haka kuma duk wanda ya ce, « “La’illah-illal ahu.” To ya haramta daga shiga wuta » (Bukhari da Muslim). Don haka ayyuka ba su fifita da kamaninta ko yawanta, sai dai tana fifita ne da niyar da aka aikata aikin a cikin zuciya. Haka kuma hankali, shi ma yana karbarfifiko a kan aikin Allah, don haka za a ga kowayana da hankali, wani ya fi wani. Haka kuma wajen wajibi da haramci, dukkan su wani ya fi wani wajen aikin. Amma shi karuwar Imani ta fuskar karuwa wanda ya zauna da Annabi lokacin da yake raye, to akwai bambanci da wanda labari ya kai masa daga baya, kamar Najjashi da kamar su, domin shi imani yana karuwa ne wajen zuciya da aiki da gabobi kamar Malamin da yake aiki da saninsa da Malamin da yake da sani amma ba ya aiki da saninsa. Don haka rashin aikin Malami da saninsa, yana nuna raunin imaninsa. Saboda fadar Annabi mai tsira da aminci cewa, “Wanda aka ba shi labari ba zai zama daidai da wanda ya gani ba.” Haka a wata fadar ya ce, “Labari ba ya zama daidai da wanda ya gani.” (Imam Ahmad ya ruwaito). Kuma ga wani labarin da ya karfafa mana cewa labari bai zama daidai da wanda ya gani. Annabi Musa (A.S) da ya sami labarin cewa mutanensa sun koma ga bautar dan maraki, bai zubar da allunan Attaura ba, sai da ya zo ya gan su da idonsa sannan ya zubar da allunan saboda gigicewa. Kuma, Annabi Ibrahim mai tsira da aminci yace, « Allah ka nuna mini yadda kake tayar damatattu » Allah Ya ce masa, « Ya Ibrahim ba kayarda ba ne ? » Sai Annabi Ibrahim ya ce, « Nayarda sai dai ina neman zuciyata ta natsu ne.» [Bakarah :260]. Haka kuma wanda Hajji ta wajaba a gare shi to, wajibi ya san yadda ake yin aikin Hajji don in an sami ikon zuwa a yi aikin daidai, sabodaita Hajji wajibi ce a kan kowane Musulmi sai dai tana wajaba ne a kan wanda yake da halin zuwa, da halin yin Zakka ga wanda ya sami ikon bayarwa, to, amma wajibi ne mu yi Imani da Hajji da Zakkah ko da ba mu da halinyin su. Haka kuma wanda ya zo zai Musulunta to, sai an lakaba masa kalmar, “La’ilaha illalah”to, amma ba za ka ce sai ya yi ayyukan ibada daidi ba, sai daga baya in an koya masa yaddazai yi. Kuma duk lokacin da wata matsala ta taso ta addini sai a sanar da shi har ya zama ya san hukunce-hukunen addini. Saboda hakaba yadda za a yi mutane su daidaita cikin imaninsu. Kuma lallai duk wanda ya tashi cikinayyuka na kwarai to zai kara imaninsa. In sha Allah, zamu ji cigaban BAYANI A KAN IMANI, cikin littafin: “AL- AKIDATUSSAH IHAT, BI MUWAKATUS SHARI’AH” na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya yi masa rahama.
Posted on: Thu, 29 Aug 2013 07:16:35 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015