FILIN SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAH) TARE DA - TopicsExpress



          

FILIN SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAH) TARE DA LITTAFIN: AL-AKIDATUSSAHIHAT, BI MUWAFAKATUS SHARI’A NA SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI WANDA YA FASSARA: ALHAJI INUWA BABA (MFR) Almajirin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi FCT. Abuja Nigeria. MAI RUBUTU: UMMU ABDILLAH ZARIA HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’AH ///20 **TUNTUBE DA KURAKURAN WASU MALAMAN TAFSIRI (3)** Cigaba: Daga cikin Tafsirin da aka sa Isra’iliyat, fadar Allah Madaukakin tsarki, “Ba mu aiko wani Manzo ko Annabi ba sai idan ya yi burin isar da sakon Allah, sai Shaidan ya sa masa kokwanto a cikin wannan buri nasa, sai Allah ya goge kokwanton da shaidan yasa a cikin zuciyar wannan Manzo ko Annabin, sai Allah ya daidaita ayoyinsa sai ya isar da sakon daidai yadda Allah Yake nufi. Allah masani ne kuma gwani. Abin da shaidan ya sa kokwanto a cikin zuciyar Manzo ko Annabi sai abin ya zame fitina a cikin zukatan wadanda suke da ciwo a cikin zukatansu da kuma wadanda zukatansu suka bushe, lalle azzalumai suna cikin kokwanto mai nisa.” (Hajji 52-53). Mai Jalaini ya fassara wadannan ayoyi guda biyu cikin tafsirinsa. Ya ce ba mu aiko wani Manzo ba kafin kai ya Annabi Muhammad wanda muka umarce shi da wani aiki da sakon da aka ba shi, sai idan ya yi niyar karantar wannan sakon, sai Shaidan ya jefa masa abin da ba wannan sakon ba ne na Allah. Saboda Annabi ya karanta Suratul Najami a cikin majalissar Kuraishawa cewa, “Shin ba ku ga Lata da Uzza ba da Manata na ukunsu?” Sai Shaidan ya jefa wa Annabi a harshensa na wata magana wacce ba Kur’ani ba wato, “Tilka garanikul’ulah inna shafa’atu hunnah laturtaja.” (Ma’ana wadanann mutane ne manya- manya ai ana kaunar ceton su, ai ceton su ana kauna). Da Kuraishawa suka ji ya yabi gumakansu da cewa ana kaunar ceton su, sai Kuraisahwa suka yi farin ciki. Daga nan sai Mala’ika Jibrilu ya ce masa, “Ai ya fadi abin da yake ba a cikin Kur’ani yake ba, Shaidan ya jefa masa a harshensa. Sai Annabi ya yi bakin ciki, sai Allah Ya goge wannan abin da Shaidan ya jefe masa, Annabi ya nutsu don Allah masani ne a kan a bin da Shaidan ya jefa wa Annabi, kuma gwani ne na gyara abin da Shaidan ya jefa na kuskure. Allah gwani ne a kan komai da yake aikatawa. To, wannan abin da Shaidan ya jefa a bakin Annabi, sai ya zama jarrabawa ga wadanda suke da ciwo a cikin zukatanu na shakka da manafunci, da kuma wadanda suke mushiraikai ne ga barin karbar gaskiya. Hakika kafirai suna cikin sabani mai tsawo da Annabi (SAW) da kuma Muminai, ta yadda ya ambaci allolinsu da abin da suke so, suka ji dadi, daga karshe sai Allah Ya lalata wannan abin da ya sa su farin cikin sabani, mai tsawo da Annabi (SAW) da kuma Muminai. Daga karshe sai Allah ya lallata wannan bain da ya sa su farin ciki. Shaykh Gumi ya ce, “Idan an dubi wannan tafsirin (Jalalaini), za a ga akwai karkata mai yawa a kan shari’a, don an tabbatar da abin da Allah Yako re shi tuntuni ba shi ma. Don kuskuren ma shi ne da aka ce Annabi ma ya karanta sai daga baya Mala’ika Jibrilu ya sanar da shi, wannan bai kamata ma a ce ya fito daga bakin Annabi (SAW) ba. Saboda tun farko Allah Ya ce, Ya kare shi daga fadar wani kuskure da har za a jingina shi gare shi. Allah Ya ce, “Idan muka aiko Manzo, to akwai kariya a gare shi, gabansa da bayansa don a tabbatar da cewa wannan Manzo ya isar da sakon Ubangijinsa. Kuma ilimin Allah a kewaye yake da su, kuma ya kididdige komai, ya kuma kidaya komai kidayawa.” Kamar yadda Allah ya ambace shi a karshen Suratul Jinni. In sha Allah zamu ji cigaban wannan bayanin, TUNTUBE DA KURAKURAN WASU MALAMAN TAFSIRI (4) cikin litatafin “AL-AKIDATUSSAHIHAT, BI MUWAKATUS SHARI’AH” na Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya yi masa rahama.
Posted on: Thu, 19 Sep 2013 12:33:29 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015