GWAMNA DA MALAMAN MAKARANTA!!! Wannan shine Zangon Karatu na - TopicsExpress



          

GWAMNA DA MALAMAN MAKARANTA!!! Wannan shine Zangon Karatu na Karshe wanda akafi sani da Third Term, wanda yanuna za‘yi sati (12) A cikinsa wato ayiwa yara Darasi na sati (10) Sati na (11) Revision sati na (12) Exam wasu Makarantu suna gamawa Yara karatu tun a sati na (9) na (10) Revision sati na (11-12) Exam dan haka za‘a sami akalla sati (3) cikin wannan wata mai Alfarma na Ramadan kwatsam cikin wannan Satin sai ga bayani yazo daga Mai girma Gwamna cewa A Rufe Makarantu Ranar Juma‘a mai zuwa wasu daga cikin Malamai sunji dadin wannan Umarni ganin cewa muna cikin watan Ibada-dan haka zasu sami damar yin Ibada sosai wasu kuma suna ganin Gwamna yajawo musu babban aiki wajen tun karar Jarabawa A kwana (5) suna ganin Gwamna yashiga Hurumin da banasaba kamata yayi yabar Kwamishinan Ilimi ya tsara abinda yaga dace, bayanai daban-daban sunata yawo tsakanin Malamai wasu sunce Principals na Bording Sch. Ne suka kawo List na abinda suke bukata wanda zaici Miliyoyi dan haka Gwamna yace arufe Makarantun wasu kuma sukace Ziyara yakai daya daga cikin Makarantun Yan‘ Mata ya tarar babu abinci dan haka yace arufe Makarantu, babu wani tabbas na dalilin Gwamna na Rufe Makarantu yanzu Yallabai yatada Malamai tsaye wajen yin Jarabawa ba zaman Opis wasu daga cikinsu-sun zargi mai girma Gwamna da hanasu kudin Geran Azumi wanda Gwamnatin baya tasaba basu, wasu kuma suna yaba masa wajen daukar Sabbabbun Ma‘aikata da Promotion da yaiwa Malaman wanda akace zasu gani cikin wannan wata na July, to Bahaushe yace yau garekane gobe ga waninka kuma kowa yai nagari kansa.
Posted on: Wed, 17 Jul 2013 19:44:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015