Gaskiyar Abun Dake Faruwa a Syria Kamar yadda mukayi muku - TopicsExpress



          

Gaskiyar Abun Dake Faruwa a Syria Kamar yadda mukayi muku arkawarin kawo muku bayanai game da yadda ake tada bom ko danawa mutane bom a cikin jamaa ko a gidajensu ko a masallatansu ko coci coci,kasuwanni, asibitoci,makarantu,kan tituna da sauransu. Muna son mu fara yin shimfida,domin zamu kawo muku hanyoyin da akabi har aka tada wasu boma bomai din domin mu dauki darasi daga yadda abin ya faru,kuma zamu kawo muku yadda suke yaudarar musulmi da yadda suke ribatar matasa da yan mata domin yin amfani dasu wajen tada bom a cikin mutane. Da farko dai,yanada kyau mu fahimci wannan sabuwar duniyar da muke rayuwa a cikinta sosai.Ya kamata mu fahimci cewar,alamura sun canza sosai ba kanar yadda muka saniba a baya,kuma kullu yaumin canzawa duniyar keyi babu kakkautawa don haka wajibine mu kara fahimtar yanayin da muke zaune,tafiye tafiyenmu,muamalarmu da wasu da sauransu. Muna son mu fahimci cewar,a shekarun baya kayayyakin jin dadi da na alatu duk a kebe suke kowanne na zaman cin gashin kansa ne,to amma yanzu fa? ilimin Thecnology ya iya tattresu a gu daya.Misali a nan: a shekarun baya a cikin gidan masu kudi zamuga akwai akwatun waya (landline) akwai talbijin,akwai radio akwatun lambar waya akwatun sadarwa da sauransu,to amma yanzu fa? ilimin Thecnology ya iya hadesu gu daya,wato duk an iya cakudasu a wayar hannu (tafi da gidanka) babu wanda ya san hanyar da akabi aka samu wannan nasarar ta ilimi sai wanda ya karanci wannan ilimin,kuma mun san cewar turawan yamma ne a kan gaba a wannan fagen. Ba wai iya abinda aka narkar a wayaba kenan aa, waya tana iya kunsar abubuwa sama da dari a cikinta,amma kuma gata nan a hannunka kana yawo da ita,don haka wayar dake hannunka tanda matukar hatsari fiye ga yadda kake zato,amma kuma yanayi ya sabbaba dole sai munyi muamala da ita. Wannan wani dan misali muke baku a kan wayar hannuka,banda rusheshen kwanon tauraron dan adam wanda muke dorawa kan gidajenmu domin kamo wasu taurarin na dan adam a wasu kasashen na daban. In muka kula sosai zamu ga cewar,cigaban ilimi ya sa bamuda iyaka a tsakanin mutanen duniya,amma sai iyaka ta kasaahenmu. Zamu cigaba.
Posted on: Sun, 16 Nov 2014 12:54:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015