(Gmc50sb) JUYAYIN ASHURA RANA TA HUDU A BAUCI. Duk jamaan da - TopicsExpress



          

(Gmc50sb) JUYAYIN ASHURA RANA TA HUDU A BAUCI. Duk jamaan da aka tura su yaki Imam Hussain sun yi ne domin neman duniya, in da ya ce duk mayakan da suka je filin karbala domin kashe Imam Hussain bawai sun yi a rashin sani bane. Sun san waye Imam Hussain (AS) dalili guda dukkaninsu kudi da kayan duniya sasu aikata wannan mummunar aikin. Daga wanda aka masa alkawarin za a ba shi kaza, sai wanda ya aka masa alkawarin kaza. Kuma wasu ma baa basu ba, ka ji asara biyu. Wadannan kalaman sun fito ne daga bakin Malam Umar Saidu Gani a cikin jawabinsa na ranar jumaa 5 ga muharram a wajen zaman juyayin kisan killar Imam Hussain (AS) a rana ta hudu a Bauci. Malam Umar ya yi maudui mai taken ASHURA MANHAJAN NASARAR YAN GWAGWARMAYA da Malamin ya shiga jero abubuwan da ya kamata dan gwagwarmaya da dauka a cikin Ashura ya jajirce ya nanata DAKEWA A FAGEN DAGA ya ce Imam Hussain (AS) ya koya mana dakewa da dogewa akan gaskiya, ko da zai kai mu ga ras ranmu. Dan uwa mai gwagwarmaya dauki wannan ka nemi dakewa akan harkokin harka ko da zai kai ka rasa ranka, Imam Hussain ya koya mana sadaukarwa a tafarkin Allah in ji Malam Umar Gani tun kafin jawabin nasa kamar kullum mawaka karkashn Dan lushi sukai ta rera waken juyayi mai raza zukata, daga nan yan tamsiliyya suka daura daga Inda suka tsaya a rana ta 3. Sun nuna shadan da mata ta fara yi a filin karbala bayan danta ya yi shahada ita ma ta dau takwabi ta doshi makiya suka mata sha sai da ta yi shahada. Daga bisani mai gabatarwa Adamu Baba Muhammad ya gabatar da mai jawabi kafin ya gabatar da shi ya yi kira ga yan uwa masu tattaki daga unguwanni da su kara sauti akan yanda suke domin baiyana me ye suke tafiya akai, ya ce hakan na matukar isar da sauko. Da mai jawabi ya kammala wakilin yan uwa na Bauci ya yi taaliki inda ya numa gwagwarmaya a matsayin wajibi ga duk dan shia ya ce shia ba gwagwarmaya tamkar biya ne ba gishiri. Haka gwagwarmaya domin kawo canji shi ma wajibi ne. Daga Malam Yashin ya rufe da addua
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:27:19 +0000

Trending Topics



lack Friday and Cyber Monday Sale HQRP 3300mAh Yellow APS Battery
The Road FRom BhuTan The planned aRRival in TRi-CiTies oF seveRal
I should have just sung this song on video but I wont l 1st
Pomegranate Lovers Click Like Health Benefits of Pomegranate/
{IICJ;2649} JOB FAIR ON 27TH JUNE, 2013 Consulate General of

Recently Viewed Topics




© 2015