Gyara fatar ka/ki Gurji Gurji don gyaran fataGurji na dauke da - TopicsExpress



          

Gyara fatar ka/ki Gurji Gurji don gyaran fataGurji na dauke da sinadarai da damada ke taka muhimmiyar rawa wurin gyara fata. Yawan cin gurji na sanya fata sheki. Bayan haka, amfani da gurji yayin gyaran fata na sa laushinfata. Akwai hanyoyi da dama da za ki yi amfani da gurji don gyaran fatarki. Za a iya amfani da gurji don wanke fuska (face wash), ko don sanya karfin fata da kuma haskenta (toner/tightener). · Amfani da gurji don wanke fuska: Idan kika yi amfani da gurji wajen wanke fuska, hakan zai magance miki gautsin fata, zai kumakara miki kyawu. Abin da za ki yi shi ne- Ki bare gurji, sai ki wanke shi, daga nan ki nika, sannan ki tace ruwansa. A hada ruwan gurjin da zuma kadan da kuma sabulun ruwa na wanka (likuid face soap). Sai a zuba hadin a kwalba. Za ki iya amfani da wannan hadin sau biyu a rana- safe da yamma. · karfin fata da kuma kara mata haske: Amfani da gurji na sanya hasken fata ya kuma dada mata haske. Ki nika gurji da na’urar bilenda (blender), daga nan ki tace, sai ki hada ruwan gurjin da kuma naaloe bera. Bayan haka, ki zuba hadi a kwalba, sannan ki ajiye a firij don ya yi sanyi, hakan zai sanya ya dade ba tare da ya baci ba. Za ki iya shafa wannan hadin a fuskarki. · Amfani don fuskar ‘face mask’: Kishafa ruwan gurji a fuska, sai ki jira ya bushe na tsawon minti 15 kafin ki wanke. Yin hakan zai rage gumi da kuma maikon fuska. Za ki iya hada ruwan gurjin da madara da man zaitun da kuma zuma sai a markada su. Idan fatarki mai gautsi ce, sai ki sanya farin ruwan kwai a cikin hadin. · Cin gurji don gyaran fata: Ki rika cin gurji domin na dauke da sinadarai da ke gyara fata, a lokaci guda na taimaka wa magudanar jini.
Posted on: Thu, 05 Sep 2013 04:23:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015