HAKKIN MUSULMI AKAN DANUWANSA MUSULMI... Hakkin musulmi - TopicsExpress



          

HAKKIN MUSULMI AKAN DANUWANSA MUSULMI... Hakkin musulmi akan danuwansa musulmi guda 6 ne Daga bakin wanda baya karya Annabi Muhammad s.a.w. yace hakkin musulmi akan dan uwansa musulmi guda shida ne 1.Idan ka hadu dashi kayi masa sallama 2.Idan ya kiraka ka amsa masamisali ya gayyace ka walima wanda ba na sabon Allah ba to hakkin ka ne ka amsa masa.. 3.Idan yayi atishawa ya godewa Allah ka gaisheshi maana yace Alhamdulillahkai kuma sai ka ce masa Yarahmakallah 4.Idan bashida lfy ka je ka gaida shi. 5.Idan ya mutu karakashi makabarta. 6.kaso masa abinda kake sowa kanka. (bukhari da muslim) LURA: Wannan fa ya kunshi alummar musulmi duka da mazan da matan kuma ba dole yanuwanka na dangi ba, aa duk musulmi danuwan ka ne kama daga makwabcin ka, abokin aikin ka da dai sauransu. Allah ya bamu ikon sauke wannan hakkoki da suke kanmu... By yusuf abdullahi A jibaga
Posted on: Sat, 02 Nov 2013 18:28:28 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015