HATTARA YAN MATA 2 ...CIGABAN LABARIN Sai naji yana cewa - TopicsExpress



          

HATTARA YAN MATA 2 ...CIGABAN LABARIN Sai naji yana cewa virgin ce, nawa zaka sayeta. Wallahi salinga sai naji kamar raina zai fita sabda tsoro da firgici. Hankalina ya tashi, basira ta ta bace i was totally confused. Sai kawai naji baki na na fadin Innalillahi wa inna Ilaihi rajiun. kawai sai idanuwa na suka kai ga makullin motar, ga makulli a jikin motar ni kuma gashi ban iya mota ba. Take sai Allah Ya bani basiran in cire makullin motar. Sai na zare makullin a hankali na bude kofar motar na wurga makullin cikin gonar masara. Faduwar makullin ya maido da hankalinsa inda yaji karan faduwar makullin. Yana juyowa sai ya ganni tsaye kusa da motar. Kawai sai na fara gudu ba tare da nasan inda zani ba. Har ya biyo ni sai naji kamar ya tsaya. Na waiga don inga me yasa ya tsaya sai kawai naga ya bude motar ya shiga. Ganin haka sai na kara gudu don nasan in yaga ba makulli zai sake biyo ni. Ina ta gudu har nazo inda wani tsoho yake zaune a gaban wani kiosk dake gaban wani gini da akeyi. Nan na fadi a gaban sa ina haki na kasa magana sai kuka nakeyi. Tsohon yanuna min da dan yatsa inyi shiru sannan yayi min ishara da in tashi in koma daga bayan kiosk din. Bayan na koma ne sai naji yana cewa yarinya kiyi shiru kar wani yaji ki. Sai nayi shiru ina duba gwiwa na don ina jin yana min zafi. Ashe na kujene sosai lokacin dana fadi a gaban tsohon. A daidai wannan lokaci ne naji kamar mota na zuwa sai naji tsohon yace yarinya shiga daga cikin shagon kar wani ya ganki. Cikin sauri na shige na boye bayan wani kwali. Wallahi malam salinga ina boyewa sai naji ance sannu baba shi kuma ya amma yauwa. Jira nake inji yace kuzo gata nan amma sai naji motar ta wuce kamar ta nufi inda na fito. Zuwa cen sai tsohon yace haka suke wuce wa da kananan yara kamar ki. sai naji yayi shiru cen kumakamar minti 3. sai naji karar sautin mota na dumfaro inda muke wani sabon tsoro ya sake kamani har saida nayi fitsari. sai naji tsohon yana cewa sun fara zuwa kenan. Kimanin motoci biyar suka wuce. Nidai ina nan na dukunkune a shagon tsoho. Bayan kaman 30 mins sai naji tsohon yana cewa gasu nan fitowa ina ganin sun gama. yau sun gama da wuri. Ina jin motocin na wucewa sai naji mota ta tsaya zuwa cen sai naji muryar wanda ya kawo ni yana tambayar tsoho, baba don Allah ko kaga wata yarinya ta wuce tanan???
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 08:58:48 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015