HUDUBAR JUMAAR DARUL-HADITHIS SALAFIYYAH (MASSALLACIN ALBANY) - TopicsExpress



          

HUDUBAR JUMAAR DARUL-HADITHIS SALAFIYYAH (MASSALLACIN ALBANY) WANNAN HUDUBAR NA YAU 7/02/2014 TA BADA KARFI NE AKAN MUTUWAR ALBANY DA MAKIRCE MAKIRCEN DA MASARAUTAR ZAZZAU DA MALAMANTA DA YAN DEMOCRADIYYA SUKA DINGA YI MISHI A LOKACIN DA YAKE RAYE. Malam musa minshawy yafara da Godiya ga Allah sannan yayiwa jamaa sallama, yace: Allah yace Acikin mazajema akwai namiji wanda yaci kawa Allah Alkawarinsa ko kuma yake fatan ya cika. Allah yace a suratul baqra karku cema wadanda aka kashe don Allah sun mutu, Allah yace rayayyune kune baku sani ba Allah (SWT) yace Zamu jarabce ku da tsoro da yunwa da nakasa na dukiyoyi da rayuka da yayan itatuwa, Allah yace amma kuyiwa masu hakuri bushara, wanda in musiba ta fado masu suke cewa innalillahi wainna ilaihi rajiun. Manzon Allah (SAW) yace; zaa rinka dauke ilimine ta hanyar dauke malamai. Tabbas ana ta dauke malamai a Nigeria amma meyasa malaman sunnah kawai ake kashewa? Matasa ya kamata ku farga. Ba komai bane kawai sai don suna kan gaskiya. Dama da mara gaskiya da mai gakiya baa shiri. Ina wadanda suka kashe Albany da iyalansa? Donme kuka kashe su? To Indai don ilimi ne toh wallahi baa dainawa. Idan domin fadin gaskiya ne to wallahi yanzu muka fara, idan domin wayarwa Alumma kai ne akan siyasa to wallahi sai mun cigaba, idan don fadin gaskiyar da yake yi ne akan Polio da cutar da Alumma da take yi ne toh zamu dora baza mu fasaba, idan wata aqeeda ne to duk abinda yake akanta dorawa zamuyi. Don haka makisa Albany kunji kunya, domin wanda baisan Albany ba yanzu bincike yake yasan wanene shi? Ku kuma yan siyasa yan democradiyya da malaman fadar gargajiya ta zazzau da sarakunan zazzau kunji kunya. kun gama fada dashi akan a kishi ashe farin jini kuka karamai. Kun kaishi fadar sarkin zazzau kuncimai mutunci badan komai ba kawai don ya rike Sunnah. Wai sai yanzu ne masarautar zazzau ke cewa ashe ma Albany mutumin kirkine! Wallahi karya kuke yi munafukai, dama can kun sani wallahi kin gaskiya ne da son rai kuma zaku gamu da Allah. Ku kuwa yan siyasa da kuke fada da Albany akan Polio wanda ta tabbata cutane acikin ta amma ahaka aka samu yan siyasa da malamai masu sonrai sukace tana da kyau zaku hadu da Allah. Mu bama tashin hankali domin Albani zaman lafiya ya koyar damu. Don haka bama bukatar yan sanda ko sojoji, mu dama namu shine karatu da karantarwa ba kuma zamu fasaba wallahi. A Nigeriya Albani ne ya fara bayyana hatsarin aqeedar boko haram har ake zaginshi amma gashi Allah cikin ikonshi yasa ga gaskiya ta tabbata. Kamar yadda kuka sani, halayyan Albani na kirki ne da kuma tausayi da dogewa akan bin gaskiya. A cikin ayyukan da mallam ya assasa akwai gina makaranta mai suna Darul-hadithis-Salafiyyah don karantar da matasa, da Albany sceince Academy da kuma makarantar karantar da marayu da tarbiyyantar dasu kyauta. ALLAHU AKBAR Albany ya barwa musulunci manya-manyan makarantu da filaye da kudade da littafai masu dunbin yawa yace na musulmine kawai bana yayansa ba. Sheikh Kabir Gombe yace: Wallahi Albany yana da baiwa domin shi kadai ne ya tsaya a garinsa ya karantar da matasa har suka goge, yace mu kuwa bamu da wannan, yace don haka malam Albany mutum ne. Sheikh Yahaya Haifan Kuwa cewa yayi: Wallahi a wajen Albany muka fara jin kalmar salaf da kuma ingantaccen hadisi da wanda bai inganta ba. Daga karshe Mallam Minshawi ya karkare hudubar ne da yiwa Malam Addua da baiwa jamaa hakurin rashi da jawo hankalin Alummah akan aci ribar abinda Albany ya bari don ci gabanmu.
Posted on: Sun, 09 Feb 2014 00:11:15 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015