Hakika duk wanda yake wannan zamani zai iya fahimtar cewar lallai - TopicsExpress



          

Hakika duk wanda yake wannan zamani zai iya fahimtar cewar lallai alamomin tashin alkiyama nata bayyana ta fannoni daban-daban. Idan muka yi la’akari da irin wasu abubuwa dake faruwa a wannan duniya tamu, wanda hakan yayi sanadiyar wanzuwar rashin tsoron Allah a zukatan wasu mutanen. Lallai abin akwai takaici cikin sa. Babu abin da yake kara bani mamaki, yau haka a kasar nan , illa ya wuce, mafi yawan laifuka na fasadi da alkaba’i da ake aikatawa kama , daga fyade, sace-sace, karuwanci, shaye-shaye, kashe-kashe, Zalunci, munafunci, gulma, kifce dama sauran su, duk ba’a cikin wata al’umma a arewacin ake aikata wadannan abubuwa dana zayyano ba, ya zarce musulmi. Musulmi sun bar musulunci kara zube, sun bar dokokin Allah, sun watsar da fadar manzon sa, an kama biyewa sharholiya da hudubar shaidan. An manta dafa za’a mutu kuma na shfa’a dafa cewar duniyar ba fa matabbata bace. An sa duniya gaba, an bar tuna lahira. Haba ‘yan uwa? A dinga sara muna duban bakin gatari mana. A yau ba sai gobe ba, idan muka dubi yadda rayuwar mu take gudana, zamu fahimci cewar tamkar dai ana tufka ne tana warwarewa, dalilina kuwa shine, a zamanin yanzu idan wani burin wani kawo ci gaba da gyara a tsakanin al’umma ne, to fa wani ba wannan ya sanya a gaba ba. Wannan tamkar wani matashiya ne, dana nazarce shi a kwanyata don ya zama shimfida ga daukacin al’umma mata da maza kafin na fantsama kan maudu’in da zanyi tsokaci kansa. Da farko babban abin da ya zaburar dani kan wannan rubutu nawa bazai rasa nasaba da yanda Iskanci da zina ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma ba, babba da yaro. Abin bakin ciki, yau ‘yan mata da samari sun maida Iskancin wani abin burgewa, ko kuma abin yayi. Yanda har mai yinsa bai zamo abin kyama ba. Lamarin da aka san ‘yan bariki dashi, amma yanzu ya dawo hannun ‘yan gida. Wanda ba ‘yan Bariki ba. Rayuwa ta shiga rudu! Babbar manufar wannan fili ne a koda yaushe shine, kokarin ganin kullum an zakulo wasu abubuwa da ke ciwa al’umma tuwo a kwarya, don nufin neman mafita. A wannan karon ina dauke ne da wani tsokaci daya shafi matan dake barin gaban iyayen su, su shiga duniya. Wadanda ake kira da ‘yan bariki ko ‘yan yawon dandi. Dama kuma wadanda ke gaban iyayen su. Da farko a duk lokacin da aka tashi ana Magana akan bariki, babban abin tambaya ko neman sani anan shine, shin me ake nufi da kalmar bariki? Waya dace da bariki? Tsakanin mata da maza, waya kamaci bariki? Sai kuma mu dubi yaya barikin take a halin yanzu? Shin kuma wane bamban ci ke akwai tsakanin ‘yan bariki da wadanda ba ‘yan bariki ba? Farko dai idan ana Magana akan wannan kalma ta bariki, ba wani abune bako ga mafiya yawa cikin al’umma ba. Sai dai kowa da yanayin da yake fassara wannan kalma ga bisa fahimtar sa. Saboda la’akari da yadda wasu lalatattu suka fake a karkashin kalmar , suke tafka munanan ayyukan da ba suyi tsari da rayuwarsu ba. Kuma manufa ko ma’anar kalmar bai yi tsari da su ba. To me ya sasu? Kuma ina mafita? Kafin mu kai ga nan, bari dai mu fara da fayyace ma’anar wannan suna na bariki. Bariki: a fahimtata ba komai bane ake nufi da bariki ba, illa wuri/garin da baka da dangin iya bare na baba, wanda kuma kaje da zimmar wani aiki don neman kudi, ko kasuwanci. A takaice inda ya zamana kazo-nazone bariki. Abin nufi kabar garinku, mahaifarka ka tafi wani gari can, inda baka da kowa naka, a dalilin neman abin rufawa kai asiri. To anan zamu ga cewar, wannan gari ko wuri da kaje shine bariki (kamar yadda wasu daga cikin ‘yan barikin suka tabbatar mini) kai kuma da kaje wannan wuri, sunan ka dan bariki. Don kar muyi tuya mu manta da albasa, akwai bukatar mu fahimci cewar bisa la’akari da ma’anar da kalmar bariki ta bamu, a wannan muhallin tsakanin mace da namiji wa ya kamata yaje bariki? Amsar a bayyanne take, domin shi namiji dama shi aka sani da fita ya nemo ya kawo gida, kuma halin rayuwa ce har ta ke kaishi ga fita bariki. Kuma shi ke kutsawa lungu da sako don neman na kanshi. Amman ga mace fa? In kasuwanci ne, har kasuwancin me zatayi da zai fidda ita, zuwa wasu garuruwan da ba dangin iya, bare na baba? Buga-bugan me mace zatayi ya wuce gari ko inda take? Ina amfanin yawon bariki ga ‘ya mace? Me zata je nema? Ya zarta tayi zaman gidan miji don raya sunnar ma’aiki. Wulakanta kai da rashin sanin daraja da kimar kai, ke sanya mata fita yawon bariki. Im ba haka ba, banda lalacewar zamani, ina kuruciyarki zasu rudeki, ki fadawa rayuwar dabbobi? Ya zamana ke kullum sai kin sai da kanki zaki ci, ki kuma sha. Kin zama rijiyar maza sha….. ya zamana ko wane alhanzir, jaki da aladen ya debo jiki da kazantar sa ke zai tunkaro. Wanda in ba albarkacin ke watsatstsiya bace, kima da darajar da Allah yayi miki ya zarta nan nesa ba kusa ba. Amma saboda kwadayin abin duniya da rashin ilmin tsoron Allah, kin bi, kin gurbata rayuwarki da haramun. Matan bariki, ko ‘Yan dandi, sune suka baro gidajen iyayen su Suka rungumi rayuwar karuwanci, ko sai da kansu a matsayin sana’a, tamkar wani ibada. Wanda kuma mafi yawa daga cikin su, sunyi nisan da basa jin kira. Kuma sun kasa gano illar hakan ga rayuwar su, bare su ran dainawa. To amma wai, hausawa kance in bera da sata to daddawa ma da wari. Kuma ba duka aka taru aka zama daya ba, amma na yarda da cewar lallai mafi yawan ‘yan matan zamanin yanzu tunanin su kadanne. Saboda kyalkyalin banza da wofi suke biyewa a kaisu a baro, su jefa rayuwar su cikin rudu da rashin tabbas. Mata masu duniya kenan! Menene silar bariki ga mata? Har wa yau irin wadannan matan barikin kan fito yawon dandi ne kan wasu dalilan da basu inganta ba. Kamar: Auren dole, cikin shege, wasu kuwa kuncin rayuwane, sai kuma rashin tawakkali, kan yadda suka taso suka ga iyayen su matalauta. Daga anan kuma in anyi gajin hakuri, sai a fadawa koma wane hanyane. Babbar dai bukatar su, su samu irin kayan kyalkyalin da suke gani a gun kawayen su. Daga nan ne kuma kishi zai kama cinsu, saboda ganin wance tana da kaza, ko an saya mata kaza. Ba kuma tare da la’akarin ko wanacan din ‘yar waye ba, nan zasu shafawa idanunsu toka, subi ta kowane hanya don ganin an samu koma menene. Saboda kuma zunzurutun kidahumanci da rashin tawakali, sai su kama sai da jikin su. (ta yaki halal, yaki haram). Don suma aga sunyi irin na wance. Lamarin kuma in baki da gashin wance, to karki ce zakiyi kitson wance. Wannan kenan, amma sai dai wai, banan gizo ke sakar ba, domin bayan tiya akwai wata caca. Kamar dai yadda na dan kawo wasu bayanai dangane da matan bariki, da kuma gurbata rayuwar su da suke a garin hakan. To ya kamata a fahinta da cewar, su fa matan bariki ko ince ‘yan dandi karma yadda sunan su yake a yanzu. Zamu iya cewa mafi yawan su jahilai ne, na karshe marasa wayo da tunani ne domin su, sun ma dauki harkar karuwanci a matsayin sana’a ce, kuma an sansu tambadaddune. To ina su kuma ‘yan matan dake gaban iyayen su, wadanda aka sanya a makaranta, su keda ilmi, watakila ma na boko da arabiya, anan sai muce irin wadannan sune kamilallun kenan? Kuma wannan na nuna cewar, lalata da tambada da kuma zina-zinace; ga karuwai ko ‘yan bariki ta ta’allaka kenan? Amsa, anan itace, a zamanin yanzu duk yanda ka kai ga tunanin ka, abin ya zarce nan. Domin kuwa komai da lokacin sa yake tafiya. Kuma ta wannan bangare an samu ci gaba (irin na mai hakar rijiya) Saboda yanzu an daina fita yawon bariki, ai ta shan dan Karen wahala. Jahilai ne, wadanda basu san dawon garin ba suka rage a bariki. Amma ai ci gaban zamanin da yazo da rudanin dake kawo rudu, shiya sa ‘yan matan zamanin suke sheke ayarsu a gaban iyayen su, son ran su. Yanzu abin ta kai kawo idan har kina ji da kanki, a holewa da iskanci to, ba maganar yawon dandi. Domin kuwa a yau haka iskanci, fasikanci da alkaba’in da ake tafkawa ya wuce sanin ‘yan bariki ko dandi, domin kamar yadda na fada komai da zamanin sa. Kuma lamarin ya zarce gidan magajiya, bare ma ai batun zaman jiran kwastoma kai a kaskance. Sai dai maganar Sakandaren ‘yan mata na kwana, ko jami’o’i da bankuna da wuraren tarurrukan aure (wajen Party) ko Picnic ko kuma tsayuwa a bakin kamar ana jiran dan taxi ko wani abu daban wato, (‘yan good evening) domin karuwancin zamanin yanzun nan ake yinsa. (a fakaice) kamar yadda na ambata a baya. Kuma anan ake tafka ta’asar da ko suma ‘yan barikin sai dai a zage su kan basa gaban iyayen su, amma ba dai batun gogewa ta fuskar tambada ba. Anan dsai zamu fahimta da cewar karuwanci, iskanci da zina baga matan bariki kadai lamarin ya ta’allaka ba, asalima yanzu haka irin yanda ‘yan mata ke totsalewa da holewar su da shigar da suka dama agaban iyayen su da sunan wayewa abin ya wuce kimar tarbiyyar malam bahaushe. Anan, a nawa ganin babu laifin wanda ya kyautu a kama ko gani ya zarta iyaye, domin su ne ummul-a-ba’isin komai na taka muhimmiyar rawa wajen rusa tarbiyar ‘ya ‘yan su, kan rashin kwabar su da ake yi dangane da wani abu da suke wanda ya sabawa addini dama al’ada. Inda maimakon da zarar yaran sunyi abin daya kyautu a tsawatar tare da nuna musu rashin dacewar abin da suka yi, a’a, sai kaji iyayen suna fadin wai, yarinta ne ko kuma kaji ance ai yaran zamani ne. kaji fa, saboda tunanin wai duk hakan wayewa ne. ta yiyu sai ka tadda daga uban har uwar duk ‘yan boko ne. basu damu da duk abin da yaran su zasu yi, daya sabawa addini ba. Ta inda zaka yarda da batuna, sai kayi la’akari da a zamanin yanzu ‘yan mata nawa; ka sani cikin shege suka haifi ‘ya ‘yan gaba da fatiha, kuma ske zaune a gaban iyayen su? Meya jawo haka? Rashin kular iyaye da sanya idanu kan abin da yaran su keyi ne, a bangare guda kuma da sangarta yaran da iyayen keyi ne ya jawo wannan barakar. Sannan suma samarin ‘ya ‘yan masusu akwai rawar da suke takawa wajen lalata ‘yan mata ta hanyar jan hankalin su da kudi. Su kuma ‘yan mata ‘ya ‘yan masu akwai din, karancin ilmin addini yake sasu irin wadannan abubuwa. Duk dai aje a dawo, duk laifin ya ta’allaka ga sakacin iyayene. Mata IYAYEN GIJI! In baku ba gida, in kunyi yawa gida ya…. Wato bana raba daya biyu, anan garin Potiskum kadai za’a samu yaran da aka Haifa ‘yan gaba da fatiha fiye da dari shida. Wadanda kuma akasarin su a gaban iyayen su, suke. Domin ni nan, akwai wani saurayi da na sani, wallahi tallahi yaran da aka Haifa na cikin shege sun haura biyar. Kuma ba’a ko ina yake lalata da wawayen ‘yan matan ba, illa wuce dakin sa dake cikin gidan uban sa. Wani sa’ilin ma akan idon uban yake shiga da budurwa cikin dakinsa, akwai ma ni wanda yace dani, uban ya taba cewa, saurayin duk harkar sa zaiyi ba zai ko kwatanta wanda yayi ba. Har ila yau, akwai wata yarinya wadda itama a gidan iyayenta take, kuma ‘ya ‘yanta biyu, daya ya mutu. Duk kuma cikn shegene. Kuma ko karfe sha biyun dare ne saurayi yazo, fita take ta bishi, kamin kuma ka sake ganin ta, sai ta shafe sama da wata daya ko sati biyu kafin ta dawo. Wani sa’ilin ma cikin abin ta samo daga yawon watsewar, ake wasu sayayyar gidan, ba kuma wai, rasawa suka yi har haka ba. Hakan shima bata sauya zane ba, domin kuwa har wani gargadi ya sanar, kan duk abin zaka yi da ‘yar sa kayi, amma banda duka.. domin yace, inda za’a ji kanku dashi to ka taba ‘yar sad a sunan duka. Kuma shima cewa ‘yar yayi duk iskancin tab a zata ko kamo rabin farcen sa ba. Haka itama wata yarinya dake bayan layin unguwar mu, wadda kowa ke mata ganin wata kamilalliya a zahiri, ashe a badini tana can tana tafka abin da ko kare bazai ciba. Domin kuwa ita nata salon iskancin wajen komawa makaranta take yi, in da inta bar gidan su da sunan ta tafi tasha zata hau mota, sai wani saurayin ta ya zaga ya dauke tada motarsa su wuce can wani gari daban ya kama musu hotel. Sai sun shafe a kalla sama da sati kamin ta koma makarantar. Bisa la’akari da wannan da ire-iren sa zai nuna tare da tabbatar mana cewar, karuwanci da zinace-zinace kusan ma za’a iya cewa ya tashi daga gindin ‘yan bariki, ya dawo ga wadanda ke zaune a gaban iyayen su (wadanda ba ‘yan barikin ba) In gyara, gyara in barna kuwa to! Domin duk laifin na iyaye ne, sakacin su da nuna halin ko inna kula ga tarbiyar ke jawo haka. Kamar yadda na fada, a sama. Idan kuwa haka ne, to ina shawartar duk illahirin matan dake yawon dandi da su daina wahalar da kansu a bariki. Su dawo gidajen iyayen su, domin bai kamata a fake da guzuma a dinga harbin karsana ba. Domin kuwa a mafiya yawan lokuta ire-iren wadannan mutanen da ke neman matan barikin, sune ke zagayawa suyi ta zagin matan ‘yan barikin, kuma sune dai ‘ya ‘yan su ke tafka fasadin daya zarta na matan barikin, amma dake wai, ance laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani. Ba zasu duba nasu da abin da sukeyi ba, suke fadin na wani. Daman manzon Allah (SAW) ya fada, kan duk abun da kayi za’ayi maka. Kuma yana daga alamomin tashin alkiyama, a maida zina da mai yinta, ba abun kyama ba. Musulmi akwai aiki a gaban mu, musamman iyaye mata da alhakin tarbiyantar da ‘ya ‘ya ya rataya a wuyan su Sannan ko shakka babu, ba musulmin da zai so yaga ‘yar sa, kanwar sa, matarsa. Ko yayar sa a harkar dandi wasu na fasikanci da ita ba. In kuwa haka ne, me zai sanya ka nemi matar wani ko kanwar wani? Kaga kuwa abune mawuyaci kayi ba’a maka ba. Iyayena mata, ku sani abin da ke fara lalata tarbiyar yaranku abune karami, kuma yake zama mai girma. Ba kuma komai bane ya zarta shigar banza ba. (wato sanya suturun dake nuna tsiraici). A sau lokuta da dama sai kaga wai, don yarinya tana makarantar boko, sai a barta tayi ta abun da taga dama; dinkunan nuna tsiraici karara za kaga tana yi, wai duk da sunan wayewa. Tana tafiya a kan layi sassan jikinta a waje, ko ina yana dame, yan kuma motsawa. Misali ma shine, akwai wani mutum ninan dana sani, wanda yana da yara mata guda biyu dake makarantar boko, amma tun kafin tafiyar tayi nisa sai daya daga ciki ta watsar da karatun bokon, ta rungumi na addini. Inda ita kuma dayar tayi ta bugawa har matakin karshe a sakandare. Abin mamaki anan shine, a duk lokacin da babbar ta dawo hutu, bata aiki ya zarta sanya matsatstsun kaya da yawace-yawacen bin gidajen kawaye, kuma duk inda taga majalisar samari sai ta tsaya wai da sunan za’a gaisa, sabanin wanda ta watsar da bokon, wadda kullum baka raba tad a hijabi, in kuwa kaga ta fita waje to, kamawa tayi. Kuma uban yana gani, amma ko kala baya cewa. Abin takaicin ma da zaka binciki zukatan ‘yan matan kan dalilin nayin irin wannan shigar banzan, dake motsa sha’awar samari ba komai zaka tarar ba, ya zarce wai, ana yin shigar fitsarancin ne don a burge samari suji dadi. (abin daya kamaci mijin tane kadai ya halatta tayiwa nau’in wannan shiga. Amma saboda sakacin iyaye yasa, tana yin sag a kowa, Allah shirya) Kamar kuma yadda na taba jin wata ‘yar wasan hausa, tana ada kwanakin baya a wani gidan rediyo, da akayi hira da ita. Inda suka tambayeta kome yasa take sanya suturun dake bayyanar da surorin jikinta kuma bata yin lullubi? Amsar daya fito daga bakinta shine, wai tana yine don masoyanta su gani (tsiraicin nata) suji dadi. To kaji fa! Ni kuwa nace, lallai a gaida masoyan wannan jaruma. Shiyasa nake kara jan hankalin iyaye mata, dasu tashi tsaye wajen takawa ‘ya ‘yan su burki, kan irin suturun da suke sanyawa da sunan burge wani. Domin sufa wadanda za’a burge din nan, ba’a san shu’umancin suba. Domin in anyi rashin dace cikin wadanda ake burgewar, wani shifa tunanin sa bai wuce ana tallata masa don ya taya bane. In haka kuwa ta tabbata, ya shiga ya fita shikenan, dama itama mai wannan aikin da biyu takeyi, in kuwa shaidan ya gifta sao dai gyaran Allah amma tabargaza kan amma yi an gama. Yau anyi gobe haka, kaga an baude yarinya ta lalace, kan sakacin iyaye. Suma ‘Yan matan zamanin yanzu suna da nasu laifin, domin majority of them basu da hankali, dabbobine, kuma wawaye. In ya za’a banda tantagaryar jahilci, ya saki wai guguwar soyayya ta kwasheki, tasa ki kyale namiji wai don kuna soyayya ya dinga taba miki jiki, yana mshafa ki, tamkar wata matarsa, in yazo hira. (anya kuwa in kin yi tunani mai miki wannan, sonki yake tsakani da Allah kuwa?) lamarin kuma yanzu haka bawai ga ‘yan mata ya ta’allaka kawai ba, har ma da zawarawa;. Wani sa’in abin har matan auren da mazajen su ba mazauna bane suna wannan kidahumancin. Don ni nan, ganau ne. Haka kuma in ka taba kwalayen ‘yan matan naka, sai kaji wai sunce, ai soyayyar zamanin sai da shan minti. Shan minti ko shan zunubi da zubar da mutunci? Kuma mafi yawa daga cikin shanayen ‘yan matan dake wannan abu, ba kasafai soyayyar zunubin kan kaisu ga aure ba. In ma anyi ba dai a zauna lafiya ko auren yayi nisan rai ba. Sai dai in sun gama sheke ayarsu sun rabuwar baram-baram kowa ya fita kan dan uwan sa, sai iyayen yarinya su, samu wani can gala-gala a cuceshi, ta hanyar kara masa kyauren gangar da aka tsotse moriyarta. Shima in mai hankali ne, ya gano cogen da akayi masa, a waste a dare daya. Wadanda basu san kan abun ba kuwa suyi ta korafi kan yawaitar mutuwar aure, aarewa alhalin ga tushen abin nan. (ba’a dai gano meke haddasa mace-macen auren bane, amma ai kashi tamanin cikin dari na samarin dake aure, badon komai suke sai don maganin sha’awa, da zarar kuma buklatar su ta biya to sai su kama wulakanta matan. Tun da dama matan su suka jawo ta hanyar amfani da suturun nuna tsiraici, har mazan suka gani yaja ra’ayin su, gudun kuma kada suyi fasikanci dasu ace ‘yan iska sai suyi amfani da kudi wajen auren su don neman biyan bukata) KALUBALE GARE KU IYAYE MATA! Har ila yau, bazan karkare wannan rubutu nawa ba tare da nayi waiwaye adon tafiya, don kira da jan hankali ga matan bariki ko dandi ba, (wanda kuma kira garesu kan gyara, shine silar wannan rubutu nawa) duk da cewar, nasan mata ‘yan yawon dandi babu wasu tantagaryun ko ince kusurguman jahilan daya zarta su ba. Amma ga shawarar Ahmad yaro kanin bayanku. Kuma komai nisan jahilcin ku, ya kamata kuyi tunani wajen amsa wadannan tambayoyi? Me kuke nema? ko tunanin samu a wajen yawon dandi? Ya zarta zaman dakin miji? (da dadi, daba dadi) Ina amfani ko ribar karuwanci ga rayuwarki? Wadda kika taba jin labarin sunyi dandi a sararin duniya, wane riba kika taba ji sun samu, daya kaisu gaci? Bayan kin sani ko kuma ki sani yanzu. Kan cewar Allah na fushi dake, kuma ki sani makomarki ba zaiyi kyau ba. (in dai baki tuba ba, kika mutu a haka) ‘Yar uwa duk da nasan karancin ilmi na damunki, kiyi dai tunani mai dan tsafta da kwakwalwarki (duk dai jahilcin ki nasan ba za’a gaza samun gaskiyar da kika sani, kika take a cikiba) ki hangi daraja da rahamar dake tattare da Aure kamar haka: ‘Yar dandi ki jini da kyau. Matar dake ldakin mijinta ta fiki daraja, martaba, da mutunci a gurin Allah da idon duniya; komai na rayuwarta, za tayi shine cikin jin dadi/farin ciki da annashuwa. Sabanin ke da duk wayewar garin duniya; bakin ciki da kuncin rayuwa ke karuwa gareki. Matar da take da miji, takan sanar dashi duk abin da take so, kuma yai mata ko ya saya mata. Ke fa? Sai dai kin jira kwastoma (abokin aikata zunubi/alfasha) sun zo, sannan zaki samu koma menene. In babu kuwa a kwana yunwa. Haka kuma, matar aure miji daya ke gareta, kuma take tarawa dashi. Sannan kuma duk abin da suka yi, lada zasu samu. Ke fa? Kin zama kariya, rijiyar maza sha yasa. Kece wannan kece wanca Haba ‘yar uwa, wannan gurbataccen lamari dame yayi kam? Duk kuma wannan bai ishi ‘yan bariki ishara ba. Ba za kumka su tashi gane martabar ma’aiki ba. Sai sa’ilin da rayuwa ta samu chanji, duniya ta fara juya musu baya, suka gamu da wani chuta irinna zamani, sa’annanne zasu fara dana sani. Wanda kuma lokacin bakin alkalami ya bushe rayuwa ta shiga rudu, da rashin tabbas. Allah Kyauta! A karshe babban abin da nake son kira da tunatarwa gas a ‘yan uwana samari da ‘yan matan wannan zamani, bazai wuce ince su kula da duniya ba. Suyi kokari wajen morar kuruciyar su da abu mai amfanar su. Mata a guji bijirewa iyaye, a fadawa rayuwar halaka; iskanci da rashin kunya ko raina na gaba ba abune mai kyau ba. A daina jan-aji marar fa’ida, gulma da tsugudidi bashi da amfani. Mu dinga zamantowa masu aikata alkairi ga junan mu. Sannan ba fa wayewa bane ‘Yan mata su dinga bi suna gaisawa da maza da cudanya dasu tamkar kawayen su, saboda Allah ya haramta in dai ba mijinki bane. ( ko da kuwa makaranta ne ta gama ku, ya kamata kin da cewar in ba muharramin ki, iyakarki karatu. Kar a wuce gona da iri. Wasu wawayen matan dake yarda da hakan, kan dauki hakan a matsayin wata burgewa ce. Basu san ma hakan zubar musu da mutunci yake a inda suke dashi ba. Alabashi ya kara musu rashin mutunci a inda basu dashi. Kada kuma ayi tunanin gyaruwar duk kan irin wadannan matsaloli dana zayyano, muddin ba tufkar a kayiwa hanci b . Wato indai bana yanzu ne suka gyara nasu ba. Saboda abin da na baya suka tarar dashi zasuyi koyi, su dora daga inda aka tsaya. Allah Kyauta. Allah sa mu Dace Abu Muhd 08037080212
Posted on: Thu, 28 Nov 2013 19:00:20 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015