Hausa Hausa wuraren da ake anfane da yaren Hausa: Nijeriya , - TopicsExpress



          

Hausa Hausa wuraren da ake anfane da yaren Hausa: Nijeriya , Benin , Burkina Faso , Ghana , Nijar (staat) , Nijar , Togo , Sudan , ( Makka da madina a Sudiyya) , kudancin Libya , Gabon ,Afirka ta Tsakiya,Cote dIvoire , Kameru , Aljeriya ,jamhuriyar Kongo , Gambiya , Equatorial Gine , Ethiobia da Eritrea . Mutanen da yarensu na farko ne: 50.000.000 Yawan mutanen da suke magana da hausa: 80.000.000 Matsayin hausa: 41 qungiyar yare Afro-Aziatisch Tsjadisch West-Tsjadisch Hausa Officiële status Wurin da yake na farko: Nigeria (arewacin ) da Nijar lambar yare ISO 639-1: ha ISO 639-2(B): hau Tarihin Yaren Hausa ﺎَﺳُﻮَﻫ Ƙabilar Hausa dai,ƙabila ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Kabilace mai ɗimbin alumma, amma kuma a aladance mai mutuƙar haɗaka, akalla akwai sama da mutane miliyan tamanin da harshen yake asali gare su. A tarihance ƙabilar Hausawa na tattare a salasalar birane.Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300s, saadda suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai,Borno da kuma Fulani. A wasu lokutan Hausawa sun sami gagaruman ikon, mulki da haɗaka ta kau da baki yan neman ruwa da tsaki, da kuma neman angizo a cikinta da kuma harkallar bayi. A farko- farkon shekaru na 1900s, a saadda kabilar Hausa ke yunkurin kawar da mulkin angizo na fulani, sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa ƙarƙashin mulkin birtaniya,yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na ci gaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin kamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne ya yi kane-kane a arewacin Nijeriya. Wannan haɗakar gamin gambiza, an faro ta ne tun asali a matsayin fulani su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a aladance hausawa gwamitse. Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma zuwan addinin Islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam. Ginshikokin aladun Hausawa na da mutukar jarumta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran alummar dake kewayenta. Shaanin noma ita ce babbar sanaar Hausawa inda Hausawa ke ma sanaar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai ya tarar, akwai kuma wasu sanaoin kamar su shaanin jima watau harkar fatu, rini, saka da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sanaoin hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a shaanin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanannen harshe a nahiyar Afirka. Harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa aladar cudeni-na cudeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jamaa da ba Hausawa ba ne a nahiyar Afirka. Bugu da ƙari, akwai cincirindon alummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar alummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce- rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa yan mulkin mallaka na birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu. Ire Iren Yaren Hausa Yaren Hausa yana da ire-ire dayawa. Gabarcin Hausa su ne:- gabarcin Hausa 1 - Kanawa 2 - Katagumawa 3 - Hadejawa yammacin Hausa :- 1- Sakkwatawa 2- Katsinawa 3- Gobirawa 4- Adarawa 5- kebbawa 6- Zanfaeawa Arewacin Hausa :- 1- Arewa 2- Arawa Hausa ajami wanda suka fita daga ƙasashin Hausa suka shiga kasashin larabawa shekaru aru- aru :- 1- Sudan 2- Saudiyya 3- Libya 4- Aljeriya Muhimmancin Yaren Hausa Yaren hausa yare ne me muhimmanci sosai a kimanin kasashe ashirin wurin aikin kasuwanci musamman ma a manyan biranen ƙasashen Afrika ta Yamma (Najeriya, Benin, Burkina Faso, Ghana, Nijer, Togo,Cote dIvoire). Da wasu ƙasashen Afirka ta Tsakiya kawa (Sudan,Gabon,Afirka ta Tsakiya,jamhuriyar Congo,Gambiada Kameroen ). Kabarcin afirka kawa (Ethiobia da Eritrea) Akwai kuma wasu yankunan na ƙasashin larabawa kawa (Makka da Madina da Saudiyya, kudancin Libiya,Algeria. do awanna uwrarun Hausa tanada muhimmamci a harakar kasuwanci da sauransu. Head Admin
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 20:05:59 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015