IDAN MUTUM YANA CIKIN SHAN ABIN SHANSA LOKACIN SAHUR SAI YAJI - TopicsExpress



          

IDAN MUTUM YANA CIKIN SHAN ABIN SHANSA LOKACIN SAHUR SAI YAJI KIRAN SALLAH YAYA ZAI YI? Anan mutum zai karasa abin shansa ne. Domin hadisi ya tabbata daga Abi Hurairata (R.A.) yace:- Manzon Allah (S.A.W.)yace: "Idan dayan ku yaji kiran Sallah alhali kwarya tana hannunsa kada ya ajiye ta har sai ya biya bukatar sa (sai ya gama sha)". (Abu Dauda ya rawaito shi, Babi na 18, hadisi na 2060) Hadisin Sahihine, kuma Sheikh Albani ya ingantashi a cikin Sharhin Abi Dauda hadisi na 1350. Amma mutane suyi hattara kar su mai dawannan ya zama Aladar su kullum.
Posted on: Thu, 11 Jul 2013 05:40:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015