IHmm NI KAM YAYA ZANYI? KAWATACE KUMA AMINIYATA!!! Slm, Zuwaga - TopicsExpress



          

IHmm NI KAM YAYA ZANYI? KAWATACE KUMA AMINIYATA!!! Slm, Zuwaga admin (Dandalin Soyayya 1) pls Hide my name and identity(ku boye sunana) Nidai Na kasance ina Jamia ne ta Ahmadu Bello University Zaria(ABU) akwai wata room mate dina wadda Allah ya hada jini na da nata. Tana matukar kulawa dani domin iyayenta masu Haline. Bata son abunda zai bata min rai haka nima bana son abinda zai bata mata rai. Komai namu tare mukeyi Hatta abinci tare mukeci. Bata boye min duk sirrinta haka nima bana boye mata nawa. Ita wannan kawar tawa ta kamu da matsananci Son wani Guy a depatment dinmu Amma ta kasa gaya mai. Kullin tana cikin Tunanin shi. Nayi- Nayi ta barni in sanar dashi amma taki yarda wai tana son sai ya kawo kansa da kansa wai don Kar ajinta ya zube a idonshi. Gashi a Kullin Tunaninshi takeyi duk ta rame. Wani lokacinma idan muna Bacci sai inji tana sumbatu(magan ganu) a cikin bacci har tana kiran sunansa. Da naga cewar ta shiga wani hali sai na yanke shawarar inje in sanar dashi ba tare da ta sani ba. Da naje na same shi Na gaya masa cewar kawata tana matukar kaunarsa. Amsar da yabani tayi matukar girgizani. Abin dayace min shine Ai a lokacin da kika zo gareni Har na fara farinciki don kuwa a tunanina zaki sanar dani cewar kece kike sona, Don Nima na dade ina dakon soyayyarki a zuciyata Nace masa bani bace nake sonshi kawatace amma sai yace shikuma Ni yake So
Posted on: Sat, 16 Nov 2013 16:58:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015