***ILLOLIN DA MADIGO KE HAIFARWA GA MASU - TopicsExpress



          

***ILLOLIN DA MADIGO KE HAIFARWA GA MASU YI! **Lesbianism*** Madigo shi ne mace ta biya bukatarta da mace, ta hanyar rungumar juna da hada gaba. Madigo haramun ne a addinin Musulunci. Malamai sun sanya shi daga cikin manya-manyan zunubai. 1- Sai dai shari’a ba ta bayyana wani hukunci zaunanne da za a yi wa masu madigo ba, alkali ne zai duba me ya dace ya yi musu na hukunci, bulala ko dauri ko kora ko tozartawa, ko kuma a hada musu duka. 2-Wasu malaman suna ganin za ayi musu hukuncine dai-dai da na yan Luwadu. Duk dai hukuncin da alkali ya yanke na razanarwa da tsoratarwa yayi.(Duba Al- mausu’atul Fikihiyyatul Kuwaitiyya da Almugni na Ibnu kudama). **Illolin Madigo** kamar sauran abubuwan da suka gabata ne wajen haifar da cututtuka da bala’i da musiba ga mai yinsa da kuma kasa baki daya. Ga kadan daga cikinsu: 1* Madigo tana canzawa mace halittarta daga dabi’ar da Allah Ya halicceta da ita, ta koma tana shaawar mace ’yar uwarta. 2* Cikin Madigo akwai rashin kunya da fitsara, alhali Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Kunya alheri ce gaba dayanta”. A wata ruwaya : “Kunya ba ta kawo komai sai alheri”. (Bukhari ne ya rawaito). 3* Madigo yakan haifar da cutakan zamani. A wani bincike da aka gabatar ya tabbatar da za a iya daukar cutar KANZAMAU ta hanyar madigo, idan aka yi da wadda take dauke da ita, kamar yadda za a iya samun ciki ta hanyar madigo, idan mace ta yi da wadda ba ta dade da saduwa da da namiji ba. 4* Haka nan likitoci sun tabbatar da madigo yana iya jawo rashin haihuwa. 5* Ana iya rasa budurci ta hanyar madigo, wanda hakan ba karamin tozarta ba ne ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure. 6* Mai madigo takan rayu cikin kuncin zuciya da kunarta, saboda Allah zai debe mata natsuwa a tare da ita, Ya maye gurbinta da kunci da damuwa. 7* Madigo yakan hana ’ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, to zai yi wahala kafin ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta rika fita tana yi, har idan Allah Ya tona asirinta, mijinta ya sake ta, saki na wulakanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da madigonta. 8* Duk Mai madigo idan bata tuba ba, bata Gamawa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haduwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai kabari! 9* Madigo dabbanci ne, saboda ko Dabbobi mata ba sa yin madigo. 10* Cikin madigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da Ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji. 11* Haduwa da azabar Allah a lahira, idan ba a tuba ba 12* Madigo gaba dayansa kazantane!!! YA ALLAH KA KARE YAN UWANMU MUSULMAI DAGA WANNAN BALAI, YA ALLAH KA KARE MUSULUNCI DA MUSULMAI.........AMEEN
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 14:07:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015