IMAM IBN QAYYIMUL JAUZIYA (R.A) Yace:- ABUBUWA 4 SUNA CUTAR DA - TopicsExpress



          

IMAM IBN QAYYIMUL JAUZIYA (R.A) Yace:- ABUBUWA 4 SUNA CUTAR DA JIKIN DAN ADAM: * 1- Yawaita Magana, * 2- Yawaita Bacci, * 3- Yawaita Cin abinci, * 4- Yawaita Jimai. ABUBUWA 4 SUNA RUGUZA JIKIN DAN ADAM: * 1- Bakin Ciki, * 2- Bacin Rai, * 3 - Rashin Bacci, * 4- Yunwa. ABUBUWA 4 SUNA BUSAR DA FUSKAR DAN ADAM. Sannan su tafiyar da ruwanta da farin ganinta):- * 1- Karya, * 2- Bushewar Zuciya, * 3- Yawan Tambaya Ba Akan Ilimi Ba, * 4- Yawaita Fajirci. ABUBUWA 4 SUNA KARA RUWAN FUSKA DA HASKENTA:- * 1- Tsoran ALLAH, * 2- Cika Alkawari, * 3- Yawan Kyauta * 4- Kame Kai. ABUBUWA 4 SUNA JANYO ARZIKI:- * 1- Yawan Istighfari Safe Da Yamma, * 2- Tsayuwar Dare, * 3- Bada Sadaka * 4- Zikiri Safe Da Yammaci. ABUBUWA 4 SUNA HANA ARZIKI:- * 1- Baccin Asuba, * 2- Karancin Sallah, * 3- Kasala * 4- Hainci. YA ALLAH KASA MUDACE, KA BAMU IKON AIKATA AIKI NAGARI. ALLAH KASA MUCIKA DA IMANI KA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA. Dan Allah kudinga yin like da comment ko kuma kuyi share dinsa domin yan uwanmu su amfana. Admin Prince Abubakar Sadeeq
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 11:03:35 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015