IN MATA SUKA SAMI YANCI…......Heh­ehehe.. ...Ta tsaya ta kalli - TopicsExpress



          

IN MATA SUKA SAMI YANCI…......Heh­ehehe.. ...Ta tsaya ta kalli gidan da kyau sannan ta share hawaye ta kada kai ta ci gaba da jan akwatinta.Nura ya fito da sauri ya tareta .Nafisa ki daure ki sake bani wata dama zan dena, kada ki bar gidan nan kada ki bar rayuwata, na san kina sona kamar yadda nake sonki me yasa kike son yankewa rayuwarmu hukuncin kisa haka?Nafisa ta tsaya ta kalleshi cikin kwalla me radadi.“ina sonka fiye da komai, rayuwata dukiyata kowana, amma ba zan iya zama da kai da wannan halin ba…zan jira ka ka dena cikin kewa, nayi maka alkawari in ka dena zan dawo amma ba zan iya zama da kai in baka dena ba”Ta jefa akwatin a mota tana rurin kuka ta shige motar yana bin ta yana kuka.Kada ki tafi Nafisa zan dena zan dena don Allah kada ki tafi”Ta ja motar itama da alamar ihun kuka take na rabuwa da shi amma fa zama yakare..nan ya zauna kasa ayashe yana kuka kamar yaro.“zan dena Nafisa ki tausaya wa rayuwarmu ki dawo, ba zan iya rayuwa babu ke ba?”******Nura na zaune a kan dardumar falon ya rike kansa da hannu biyu baya kuka yanzu amma yanayinsa har gara me kuka domin ko kiftawa baya yayi. Hajiya Altine mahaifiyarsa tana tana ta kallonsa cikin mamaki“Amma ni ko Nura me ka yi wa Nafisa da zata iya zubar da soyayyarku haka ta bar gidanka? Yarinyar da ta sha poison don kawai an ce ba zaku yi aure shekarar da take son kasancewa da kai ba…me kayi mata ka gaya min gaskiya”Nura ya yi murmushin takaici ya ciza lebe“Ki bari kawai mama ban kyauta ba na cuceta”“Me kayi mata nace? Mata kake nema”Ya kada kai.“yaya za a yi in ga mace a mace ina tare da Nafisa? Da mata ma nake nema aida ya fi laifina sauki”Ta zaro ido“maza kake nema kenan?”“Da maza ne aida ya fi sauki ma a gareta”Hajiya ta doka salati ta sunkuyo kansa “mutum ka kashemata kenan gaya min”Shima ya dago ya dubeta da mutum na kashe mata da sauki hajiya da na san zata yafe min ba zata bar ni ba”A yanzu bakin hajiya ya li ke tsaye take tana kallonsa da tsoro. Can ta samo abin cewa cikin mika wuya..“
Posted on: Wed, 23 Oct 2013 08:13:57 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015