INA MASOYA ALJANNAH NA - TopicsExpress



          

INA MASOYA ALJANNAH NA HAQIQA? Bismillahir-Rahmanir-Rahim...... ‘Yan‘uwa Duk mai buqatar shiga Aljannah to, ya yi aiki da wannan Hadithin mai zuwa: An kar‘bo daga: Abiy Umamah Sudayyi Bin Ujlanil-Bahiliy (RA) yace: Naji Manzon Allah (SAW) a lokacin da yake Khuduba a Hajjatul Wada‘i yace: ((Kuji tsoron Allah, kuyi sallolinku biyar (na farilla), kuyi Azumin watanku (Ramadan), ku bayar da zakkar dukiyoyinku, ku yi biyayya ga shuwagabanninku, zaku shiga Aljannar ubangijinku)). [Tirmidhiy ya ruwaito shi, kuma yace: Hadithi ne mai kyau ingantacce]. ‘Yan‘uwa sai mu dage! Mu ga mun yi iyakacin iyawarmu wajen ganin mun aiwatar da wajiban dake kanmu, da ma Qari da nafilfili, domin mu ga mun samu mafi Qolokuwar abunda muke buqata wajen ubanginmu wato: ALJANNAH! Ya ALLAH ka bamu Aljannaul Firdausi mad‘aukakiya. AMEEN. *JUMA‘AT KAREEM*
Posted on: Fri, 28 Jun 2013 09:41:08 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015