INYASS YA SAKE BAYYANA! Wannan karon kuma a kaduna! sama da - TopicsExpress



          

INYASS YA SAKE BAYYANA! Wannan karon kuma a kaduna! sama da watanni biyu da suka gabata ne hoton inyass ya bayyana a bangon wani masallaci a Ikorodu,lagos.kafin nan ya taba bayyana a Abeokuta,Ogun.da kuma wadansu wurare da dama. yanzu kuma sai gashi ya bullo a kaduna. wai abin tambaya ita ce,me yasa a duk fadin duniya da tarihin duniya babu wani Annabi ko wasu salihan bayin da suke bayyana sai waliyyan dariqa? in don daraja da walittaka ne,sun kai annabi da sahabban sa ne? ya ku masu imani da irin wadannan hotuna,ku sani Iblisu laantaacce ya sha alwashin batar da bil adama ta ko wane hanya. ya zo wa Annabi Ibrahim da matar sa a wani siffa domin ya hallaka su,amma Allah bai bashi saa ba. mu sani cewa wannan makirci ne kawai na shaidan domin ya hallakar da alumma,wanda tuni har ya fara samun nasara. musulunci ya karantar da cewa duk wanda ye mutu,ya mutu kenan bazai sake dawowa ba. don haka muna rokon Allah ya raba mu da sharrin shaidan.
Posted on: Sun, 24 Nov 2013 21:30:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015