JIBWIS NHQ JOS NIG. ANNUAL LAUNCHING OF EDUCATION. Hadaddiya - TopicsExpress



          

JIBWIS NHQ JOS NIG. ANNUAL LAUNCHING OF EDUCATION. Hadaddiya kuma Dunqulalliyar Qungiyar Jamaatu Izalatil Bidiah Wa Iqamatis Sunnah, nhq Jos, founded by Asdheikh Ismaila Idris bn Zakaryya Jos. Karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai na Africa da kewaye, Khalifatul Khairiy, Assheikh MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR. Da mataimakinsa, Garkuwan malaman Africa, Waziri Sidiqin, Assheikh YUSUF MUHAMMAD SAMBO RIGACIKUN. Da Shugaban gudanarwa na kasa, Jikan Shehu Usmanu Dan Fodio, ALH. ABDURRAHMAN MARAFA TAMBUWAL. Da directan agaji na kasa, ALH ISAH WAZIRI MUHAMMAD GOMBE. Suna gayyatan dukkan jamaar wannan duniya tamu, zuwa wurin qaddamar da gidauniyarta na raya ilmi da ilmantarwa a mataki na kasa da kasa, wadda ta saba gabatarwa duk shekara. WURI Federal Capital Territory Abuja, Nigeria, a dandalin nan da aka saba gabatarwa na Eagle Square. RANA Ranakun Asabar da Lahadi na sati mai zuwa, 24 da 25 ga watan January 2015. Kafin gabatar da launching za a saurari waazozi daga bakin malaman qungiyar da hafizanta masu wazi na kasa da kasa a ranar asabar da daddare, kafin sannan launching ya biyo baya daga baya a safiyar lahadi insha Allahu. Kuma kada a manta wannan waazin shine na shida a cikin lissafin waazozin qungiyar na wannan season, an bude kakar waazin bana ne da waazin kasa na garin Deba Jihar Bauchi, 2. sai kuma garin Faggo da ke Jihar Bauchi, 3. sannan na garin Makarfin Jihar Kaduna, 4. bayan nan sai garin Aleiru a Jihar Kebbi, 5. daga nan aka nufi garin Kebbe cikin Jihar Sakkwato, sai cikon na shida 6. Abuja F.C.T. da sunan Allah. Allah ya bada ikon halarta , Allah ya sa a yi lafiya a koma gida lafiya ameeeen.
Posted on: Sat, 17 Jan 2015 20:10:59 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015