JIBWIS SCRATCH CARD_ Bismillahir Rahmanir Raheem. Alhamdulillahi - TopicsExpress



          

JIBWIS SCRATCH CARD_ Bismillahir Rahmanir Raheem. Alhamdulillahi rabbil alamin, wasallallahu ala nabiyil karim. Bayan haka. Kungiyar Jamaatul Izalatul Bidah wa Iqamatis Sunnah (Jibwis) ta fito da wani tsari domin tai mako da tallafawa musulunci kuma ya zamana addini ya tsayu da kakafun sa. Yan uwa masu albarka idan baku manta ba kwanakin baya kungiyar tafito da wani tsari na mutum ya bada number shi da kuma adadin kudin da zaa cire masa a kullum, to gaskiya wannan tsarin bai yiwuba, saboda kamfanin wayoyin sadarwa sunce bazasu yarda ba har sai idan kungiya ta yadda zata bada 70%, to kaga wannan zalunci yayi yawa yanzu ace inbaka kwangila ka amsar mani naira 100 sai ka dauki 70 ka bani 30. To wannan shine yasa aka ki yarda saboda kada a rika amsar kudin alumma amma kuma wasu arna su rinka salwantar dasu. To bisa wannan shine aka fito da wani tsari na scratch card. YADDA SCRATCH CARD DIN YAKE. Shi dai wannan scratch card din guda 2 ne, akwa na: -Registration. -Donation. Da farko mutum zai fara sayen na Registaration bayan kayi wanda naira 100 yake, bayan kayi Register zaa turo maka number ka ta Reg din to da itane mutuw zai yi amfani a koda yaushe wajen Donation din kuma zaka iya samun wannan scratch card din a kowane masallacin jumaa, kuma shi scratch card din na Donation akwai na 100, 200, 500, 1000, 5000, 10,000 dadai gwargwadon halin Ka. kuma domin neman karin bayani kana iya tuntubar masallatan jumaar garin ku. MANUFAR YIN HAKA. Bincike ya nuna abokanan zaman mu ta haka suke amfani domin ciyar da addinin su na karya gaba. Kuma kusani mu alummar musulmi muna bukatar abubuwa kamar haka; -asibitin musulunci. -makarantun musulunci. _taimakon gajiyayyu da marayu. _samar ma musulmai aikin yi da sauran su. Kuma insha Allahu ta wannan hanyar muke ganin zaa samu nasarar cimma wannan abu. Daga karshe ya kai dan uwa kasani wannan abu matukar kai musulmi ne zai yi amfani agare ka, kai har da abokan zaman mu sai ya amfana. Dan haka hanzarta kasiyo ko kuma ka ba wani abokin ka ya siyo maka, babu bukar akawo maku ayoyi da hadissai da suke nuna taimakon musulunci saboda ko wanen ku ya sani dai dai gwargwado. Allah ya bada ikon taimakawa.
Posted on: Fri, 25 Oct 2013 14:39:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015