))) JONATHAN ZAI SALLAMI BAMANGA TUKUR ((( Rahotanni dake fitowa - TopicsExpress



          

))) JONATHAN ZAI SALLAMI BAMANGA TUKUR ((( Rahotanni dake fitowa na cewa shugaban PDP na kasa Alh Bamanga Tukur na dab da ya taba kasa Rahotannin na cewa shugaban kasa Jonathan da manyan mukarrabansa sun kwashe dare biyu suna tattauna yadda za a sallami Bamanga Wasu daga cikin mashawartan shugaban kasa sun tabbatar masa da cewa tun da gwamnoni da masu fada a ji sun nuna basa kaunar Bamanga to bai kamata su cigaba da barin shi kan kujerar sa ba don gudun kar jam‘iyyar ta wargaje Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin Delta da Akwa-Ibom suka halarci zaman suma sun amince da shawarar a sallami Bamanga amma kar ayi mai korar kare kamar yadda jam‘iyyar PDP ta saba korar mutanenta Bamanga mai shekaru 77 mahalarta zaman sun bayar da shawarar a umarce shi ya sauka daga shugabancin jam‘iyyar saboda yawan shekaru ba zasu bar shi tafiyar da aikin sa dai-dai ba To ko Bamangan zai mutunta wannan shawara? Lokaci ne zai nuna
Posted on: Sun, 18 Aug 2013 18:18:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015