Jonathan Ya Mika Wa Majalisu Kudirin Kara Lokacin Dokar Ta Baci - TopicsExpress



          

Jonathan Ya Mika Wa Majalisu Kudirin Kara Lokacin Dokar Ta Baci A Jihohin Yobe, Borno Da Adamawa Shugaban Goodluck Jonathan cikin wasu wasiku da ya aika ga shugabannin majalisun dokokin kasar nan, ya nemi su aminci da kudirinsa na kara tsawon lokacin dokar ta bacin da aka sanya a jihohin Yobe, Borno da Adamawa, dake Arewa maso gabashin kasar nan, sakamakon yawan tashe – tashen hankulan da ake yawan samu a yankin. A watan Mayu ne dai aka sanya dokar ta bacin a jihohin na tsawon watanni uku, wadda za ta kare a wannan wata na Nuwamba. Sai dai shugaban ya nemi majalisun su amince ya sake kara lokacin dokar har tsawon watanni shida nan gaba, a cewarsa har yanzu akwai barazanar tsaro a wasu sassa na jihohin. Idan majalisun sun amince da kudirin na Jonathan sabon lokacin da aka kara zai fara aiki ne daga ranar 12 ga watan nan.
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 19:54:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015