***KALUBALEN DA KE FUSKANTAR MATASA MUSULMI A YAU *** Matasan - TopicsExpress



          

***KALUBALEN DA KE FUSKANTAR MATASA MUSULMI A YAU *** Matasan farko sun fahimci wannan koyarwar, sun yi imani kuma sun yi aiki tukuru; matasan yanzu sun tsaya a kan addu’a ne kawai ta “Allah Ya dora Musulunci a kan kafirci.” Kafirai kuma suna ta aikin ganin kafirci ya shiga gaban Musulunci ta hanyar raba Musulmi da turbar Musulunci da dora su a kan turbarsu; ga kadan daga cikin nau’o’in irin wannan kalubalen: i. Shiga rabi-da-rabi ko ta kwaikwayon Turawa: Matasa Musulmi a yau sun fi jin dadin saka tufafi ba tare da hula ba, koda kuwa za su shiga sahun gaba a masallaci ko makarantar koyon darasin Musulunci, ko zuwa jana’iza, ko dawafi yayin aikin Hajji da makamantansu; kuma ba sa jin komai game da hakan. Wani lokaci ma su yi shigar da za su sabule wando, su take kafarsa, wai nan “kama kasa” a Ingilishi “earth down.” Matasa mata sun fi kwatanta shigar Musulunci a mafi yawan lokaci, saboda saka hijabi, wanda makarantun Islamiyya suka raya; amma su ma ana samun masu son su yi shiga irin ta Amurkawa, wajen bayyana surar jiki koda kuwa a wurin ibada ne; alhali masu hankali a Turai suna kishin mata Musulmi saboda alfarmar hijabi. ii. Sai burin tara dukiya mai yawa, wani lokacin ko ta halin kaka. iii. Ga gudun daukar nauyin ’yan uwa; matasa sun fi son su zauna nesa da dangi da iyaye; makwabci ya dade bai gaisa da makwabcinsa ba. ib. Babban kalubale da watakila ya fi kowanne shi ne na raba addini da rayuwa, musamman a bangaren siyasa da shugabanci. Illolin raba siyasa ko shugabanci da addini suna da yawa a rayuwar Musulmi. Ga kadan daga ciki: a) Imani shi ne ginshikin farko a rayuwar Musulmi; amma a kasahen Musulmi babu hukumar inganta imani, yayin da ake da hukumar cusa kishin kasa a zukata. b) Sallah tana da muhimmanci a rayuwar Musulmi, amma da za a gayyaci shugabanni bude Masallacin Juma’a, lokacin ya ci karo da bude sabon ofishin jam’iyya, shugabanni za su je wurin bude ofishin ne, idan an ci sa’a su tura wakili wurin bude Masallacin Juma’a; alhali a wurin bude masallaci za a yi wa kasa addua’ar zaman lafiya, a roka wa shugabanni shiriya, amma a wurin bude ofishin jam’iyya za a yi ta yin ihu ne, a yi ta kirarin jam’iyya, watakila ma ’yan Jagaliya su duddura wa shugabanni ashar. c) Azumi da ciyarwa cikin watan azumi suna da muhimmanci a Musulunci, amma kudin da ake warewa don ciyar da bakin gwamnati sun fi wadanda ake warewa don ciyar da mabukata a cikin watan Ramadan, wannan a ma inda ake da tsarin ciyarwar azumin ke nan. d) Zakka ibada ce mai girma kuma hanya sahihiya ta kawar da talauci a cikin al’umma, kamar yadda binciken ilimi ya tabbatar, amma Hukumar Zakka a inda ake da ita, ba ta samun gatan hukumar tara haraji, duk da cewa Bature ya kirkiro ta ce da nufin cin zali da talauta al’umma. e) Aikin Hajji da hukumar da take kula da shi, ba sa samun kudin da ake ware wa kwallon kafa da hukumar wasanni. A dalilin haka, idan ’yan kwallo za su fita waje, gwamnati ce take daukar nauyinsu, ta sama musu masaukin da ya fi wanda ake sama wa alhazai, ta ba su abincin da ya fi wanda ake ba alhazai, a samar musu motocin da suka fi na alhazai, idan sun dawo manyan jami’an gwamnati su tarbe su, su shirya musu walimar girmamawa yayin da ba wanda yake taren alhazai sai jami’an tsaro da wani lokacin suke karbe canjin da alhazan suka zo da shi.
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 20:30:58 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015