KAMAR ALMARA ; Amrya Ta Kashe Angonta Wata Guda Bayan - TopicsExpress



          

KAMAR ALMARA ; Amrya Ta Kashe Angonta Wata Guda Bayan Aurensu... JOS: Bayan wata daya da daura wa Maryam Yahaya da angonta Muhammad Lawal Alhaji Bala ta amsa a gaban jami’an tsaro cewa ita ta kashe shi mijin nata da ke zaune a Gangare Jos fadar gwamnatin jihar Filato. Binciken da Majiyar Dandali ta yi ya nuna cewa, Lawal Yahaya dan shekara 30 da haihuwa, ya gamu da ajalinsa ne ranar Talata 9 ga Yuli, 2013 a lokacin da ya taso daga wajen aikinsa kuma ya nufi gida da niyyar hutawa. Da ya ke magana da wakilin Majiyar tamu a Jos yayan Marigayi Lawal Alhaji Bala, Mallam Hamza Dikko, ya bayyana cewa bayan sun yi sallar Azahar da Marigayi Lawal sai ya sa a ka dama ma sa fura ya sha kafin su ka yi bankwana a kan zai je gida ya huta, sai kawai bayan ya fito daga massalaci bayan sun yi sallar La’asar ya tarar da dan aike cewa a na neman sa maza-maza a gida, domin wani mutum ya daba wa Lawal wuka a wuya ya tsere. Isowarsa ke da wuya ya iske kanin nasa jina-jina, kuma nan take ya rasu. Binciken da Majiyar tamu ta yi ya kara nuna ma na cewa, bayan ’yan sanda sun zo sun yi awongaba da ita zuwa ofishinsu ne ta je ta amsa a gabansu cewa ita ce ta kashe mijin nata da wukar yanka kayan miya. Babban jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sanda na jihar Filato, DSP Filicia Anslem, ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma ta kara da cewa, da fari Maryan Yahaya ta zargi wani yaro da kashe mijin nata, amma daga baya sai ta amsa ita ce ta kashe shi. *** Allah shi kyauta... SOURCE: LEADERSHIP **** Dandali Promise to Appreciate Ur Comments/ Like / Share
Posted on: Tue, 23 Jul 2013 10:11:44 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015