KECE GUDALIYA •••••••••••PART - TopicsExpress



          

KECE GUDALIYA •••••••••••PART 1••••••••••• Tana kwance a kasan rumfa. Duk da zafin rana da akeyi hakan bai hanata kwanciyartaba takwanta har da minsharinta tana barci. Duk da daidaigun mutane dasuke wucewa acikin kasuwane. Kasancewar yau asabar kuma yau akecin kasuwa acikin billirin. Yawanci tangalawa ne dakuma bafulatanai saikuma waja gawanda yake ganewa yakuma banbanta. Kayan jikinta zai bayyana muku wacece ita. Yarinya yar shekara 10. Tana kwance. Irin almajiran tashan nan. Hayaniyar datayi yawa tasa ta tashi tadauki yakunnanen hijabinta ta saka. Tana tafiya tana susa kanta. Wata rumfa tanufa inda ake siyar da abinci ga yan kasuwar. Ta tsuguna tacewa wata mata babbar mace wacce zatakai shekaru 40 a duniya. Inna ladi naxo wanke wanken. Matar ta cakumo kanta shegiyar yarinya! Inakika shiga naketa nemanki. Kema kinsan yawoko. Yau bake ba abinci kishiga kasuwa kinemo. Haka kuwa akayi tasha wanke wanke ta tsaftace gun. Dolenta tabar gun a yayinda wani customer yafara complain baya iya cin abinci saboda kyankyami. Wanda ta haddasa. Afrah kenan! Baiwar Allah. Wacce ta tashi batasan waye iyayentaba. Gidanta shine kasuwa. Batada matsuguni ko gun zama. Inna ladi ce take taimaka mata da abinci idan tamata wanke wanke shima saita sha gori da duka da wulakanci.…… Kukasance tare dani a part 2 KECE GUDALIYA ××××××××PART 2××××××××× Baxatace ga yadda rayuwarta takasanceba. Yauma tatashi daga rumfarta tadauki zaninta taje famfon masallaci tawanke shi. Tadan tsaftace jikinta. Wani mai sayar da dabino yazo wucewa tace don Allah malam kataimaka min da dabino. Ko biyune inci. Yakalleta tausayin yarinyar yakamashi ko su waye iyayenta dasuka barta haka . Yaciro yakulla a leda yabata. Takarba hannu na rawa ta durkusa agaban famfon tanaci tanashan ruwa cikin mintuna kadan tashanye tas! Shima yana zaune yana kallonta. Yace a ina kike dazama. Tanuna masa kasan rumfar. Yace ina nufin gidanku tace nanne gidan. Mamaki ya kama shi bata kare mishiba saida yace ina mamanki da babanki. Takalleshi tace bani dasu. Susar kai takeyi sosai. Yace anan kike sallah kici abinci kiyi abinci? Takalleshi tace meye sallah. Salati yayi yazaro ido. Duk da kankantan ta yaci ace tasan meye sallah. Yace me akeyi anan. Yanuna mata masallaci. Tace kullum anacewa Allahu akbar . Ayita wani yare. Sai maza sushiga. Yace bakida kawane? Tace banda kowa. Abun yadaure masa kai sosai. Yace zakije gidanmu. ?. Cikin murna tace laa ae zanje. Yace mujeto. Sukayi tafiya har suka isa gidansu. Daga zauren yayi sallama sukashiga. Tana labe a bayansa kamar barauniya. Gidan dan madaidaicine. Saidai da alamu akwai saointa . Yashiga yayi sallama matar dake xaune tana kasa goro ta amsa. Tana wage baki. Yazauna inna ina wuni. Lafiya dan nan yakake yace lau inna. Idonta yakai kan afrah tace wannanfa a ina kasamota. Yace inna wallahi yarinyar taban tausayine. Atasha take kwana batada kowa ko sallah bata iyaba. Innan taja tsaki sannan tace. Mtsw. Kai gaka sarkin tausayi daga ganin mage ka tsinto ina rabaka da shige shige. Haba inna wlh bahaka bane . Dan Allah yimin shiru. Muma yamuke ciyar dakanmu ka jajibo wata. Yace Allah zai kawo. Da alama dai innansa batayi naam ba. Amma dole yazauna yayita bata baki harta hakura. Dasharadin afrah zatadinga wanke wanke da shara dakomai kafin abata abinci. Baiso hakaba amman dole yasa yace eh. Nan bilki kanwansa wacce kansu zaixo daya da afrahn tashigo. Da tallanta akai. Nan innan tace zo autana daga yau bake ba talla munsamu yar talla. Zaiyi magana ba fuska. Nan bilki tazauna tana wage yellown hakoranta. Ganin afrah ta toshe hanci (uhmn kuji har kura zaice wa kare maye injin benaxir). Tana cewa mama wannan kayanfa wai afrah. Inna tace wai kwasota yayi a kasuwa……… Kukasance tare dani a part 3 KECE GUDALIYA °°°°°°°°°PART 3°°°°°°°°° Bilki tayiwa afrah kallon sama da kasa kamar wacce taga kashi. Kashinma irin mara gata. Tace inna nasamu yar wanki. Aminu ya hanbareta dan tsabar rashin kunya agaban nawa kike cewa kinsanmu mai wanki. To wlh zanjimiki ciwo. Innace ta katseshi kai yadai yarinya da gidan ubanta zaka takura mata. Maza ka bacemin a gurinnan. Bilki taturo baki. Wlh mama yaya yacika takura. Shikuwa aminu. Zuwa yayi yadiba ruwa yabawa afrah yace tayi wanka. Tacude jikinta har kanta. Haka kuwa tayi. Itakanta taji dadin jikinta fitowarta keda wuya tatarar ya aje mata tuwo taci tayi nak abunta batare da wani damuwa ba. Kasancewarta karamar yarinya. Lokacin sallah yayi yadauko buta yace kiyi alwala takalleshi tace ban iyaba. Yazauna yakoyamata. Sallahnma haka yayi. Yace kullum zandinga koyamiki adduar sallahn. Duk wanda baya sallah to tabbas zaishiga wuta. Kuma musulmai ne basa sallah. Da alama dai kwanyarta na aiki donkuwa duk kalmar daya fada mata bata mantawa. Dare yayi yataso bilki yahada dasauran yaran gidan da afrah yashiga koya masu karatu. Bayan kammalawa sunci abinci yace kowa yaje yakwanta. Afrah tamike tadauki. Zaninta tanufi daki. Nanfa akafara hayaniya. Bilki takira inna sukahau gori. Ke inbanda abunki inbanda naci irin wannan yazaayi. Ace kinzauna mana agida har kina tunanin kwana akan gado. Afrah ta matso kwallar idonta tace bakwana zanyiba. Da zan gyara matane ni akasa zan kwanta. Nan inna tatusata tagyarawa bilki gado itakuma ta kwanta akasa. Bai dametaba kasancewar tasaba Nakasuwa harda duwatsu nankuwa harda sumunti ta gyara tayi baccinta. Da asubar fari ruwa taji ankwara mata. Shegiya tsintacciyar mage. Kinsamu gu harda wage jiki ki kwanta to kitashi kije dibo ruwa kiyi wanke wanke. Afrah ta murtsike ido . Tace to. Tadauko buta donta gabatar da sallah kamar yadda yaya aminu yace tayi duk dabata iya karatunba haka ta dungura tadauki langa taje layin borehole tadebo ruwa tacika randar nan tam sannan tadauko wanke wanke tayi . Tashare gun. Tahura wuta wanda duk tasaba agun inna ladi mai abinci. Sannan innansu aminu tadaura mata tallar alale tace saura kobo na yabata sainaci ubanki. Matsiyaciya. Tagoge kwallarta. Duk da karancin shekarunta kalmar zagin yana mata ciwo.…… Kukasance tare dani a part 4 KECE GUDALIYA •••••••••PART 4•••••••••• Tafita tasha tanufa duk inda tasan zata samu ciniki to nan take xuwa. Kasancewarta fara yar bulbul da ita duk kuwa da talauci datakeyi. Bashi zai hana mutum gane cewa kyakkwawar gaske vace ba. Fatarta mai kyau saidai duhu tayi saboda wahala. Duk tsayin gashin kanta cunkusheshi takeyi cikin dankwali. Idonta manya manya wanda zan iya cewa su sukafi jawo hankalin kowa a kanta ga dogon hanci saikuma tsukakken bakinta . Tafiyarta ahankali takeyinsa. Duk da nauyin tallarma tasa mata wata gajiya. Don haka tanufi rumfarta tazauna agun. Nan masu wucewa suke dan tsayawa siya. Tayi ciniki kam. Amman baa siye dukaba. Wanda ita bata kawo komai aranta ba tamike tanufo gida. Tayi sallama innan tana zaune tana taunan goro. Tana ganinta tahau yake hakwaranta. Bayan afrah tasauke tafitar da guda hudun da baa sai daba. Inna tamike tace wannanfa. Afrahn tace Inna baa siye bane. Inna ta cafkota tahadata da garu. Don ubanki wannan din wazaici. ? Asaran kudi zakimin?. To yau bakida abincin rana. Afrah irin macece wacce takeda zafin zuciya fiyeda tunanin mutum. Don ita kama kunnen baimata ciwoba kamar irin bakar maganar da ake gayamataba. Don haka tamike tayi waje tazauna agun. Akwai wani lungu agefen zauren nan ta zauna taci kukanta. Ahankali ya dafata tadago a razane……… Kukasance tare dani a part 5 KECE GUDALIYA ********PART 5********* Yaya aminu yaushe kadawo. Ya kalleta batare da ya amsa tambayartaba shi sai ya tambayeta . Mekikeyi anan? .Tace dukana inna tayi akan bansiyar da alala ba. Tace yau banda abincinbrana ma tace. Yaji zafin hakan sosai. Sai yace yihakuri kixo muje. Ta zuba masa mayun idonta tace nibazanjeba. Yace kintaba ganin anyi zuciya da mama ?. Tace waye maman . Yace inna mana. Saita nutsa tace gwara rashin maman ashe. Dasauri yabata rai. Inkinaso mushirya to wlh kitashi kishige gida. Bayanda ta iya dole tamike.. Bayan sunshiganma innan tahada dashi tamusu tatas. Rayuwa tacigaba da wahalar afrah. Komai sai gaba yakeyi. Wani lokacin sai ta gwammace kasuwarta kasan rumfa. Duk kankanta tana ganewa don tanada basira. Wani abu dayake daurewa aminu kai shine zafin zuciyarta. Tanada balain zuciya sau dubu inzaa mata gori akan abinci to zata hakura da abincin duk yunwarvda takeji . Ga miskilanci dayake ganin shima ajikinta. Yakanyi mamaki ina iyayenta suke kullum adduarsa Allah ya bayyana masu dasu. Tuni yakoya masu sallah da duk abubuwan da yara mai shekarunsu zasu sani. Duk acikinsu afrahn ma tafi kaifin basira.Bilki kuwa tasamu yadda takeso inna tagoya mata baya tana wulakanta afrah amman sai yayanta bayanan. Inbahaka ba zataci kaniyarta itama. Wata rana afrah nagyarawa inna gado. Inna takare mata kallo tace bilki kiduba acikin kayanki kiciro marasa kyau kwara daya kibata . Bazan iyacin abinci hakaba . Bilki taturi baki haba inna. Ai zaa rainani insa kaya tasa . Tahakura dai tukin. Inna tace yihakuri autana kikawo mata. Tamike tadauko wata rigar kanti tajefawa afrahn ke! Amsa. Afrah ko juyowa batayiba balle takalleta. Inna tace ke afrah. Tajuyo sannan innan tace ga kayan dauka. Tace aa inna kubarshi nagode. Tanafadan haka tafice. Mai inna zatayi kuwa tamike tajawota itada bilki suka shiga nada mata duka. Aminu ne yashigo jin ihu yasa yashiga dakin dawuri wani irin fuzga yayiwa bilki ya wurgata gefe guda sannan yafara riko inna. Haba inna yakuke hakane dan Allah kasheta zakuyine?. Kai dan nan ashe bakada kunya? Akan wannan matsiyaciyar zaka karyani. To nabaka nanda minti goma ka tattarata kabarmin gida banson ganinta. Yabatarai sannan yace haba inna!. Kafin yacigaba harta fara kuka tana fadin. Tunda mahaifinka ya rasu nake rukonka baka ganin mutunci na. Yanxun akan wata tsintacciyar mage zaka karyani. Nan yakarya murya yafara bata hakuri. Kamar bazata hakura ba amman tashare tace yarinyar ce inaga tafiyarmu bazataxo dayaba tanada taurin kan tsiya. Anan bilki tabata kaya amma kememe yarinyar nan taki karba……… Kukasance tare dani a part 6 KECE GUDALIYA ••••••••••PART 7••••••••••••• Washegari dahiru yayiwa aminu magana. Yaja afrah bayan tagama wanke wankenta da aikacen gida. Saanta daya baa daura mata alala ba. Suka nufi gidan galadiman garin. Gida ne babba sassa sassa. Kowa da bangarensa. Maana da yayan da iyayen kowa nagun tare da matansu. Bayan sun nemi iso agunda dahirun yanema ma afrah. Matar tafito . Babbar mace mai cikar kamala. Bazata gaza shekara hamsinba. Ta fito tana faraa. Bayan sun gaisheta sai dahiru yace gatanan hajiya. Haj. Takalli afrah takara kallonta kafin tace wannan dahiru ai tayi karama. Alhakinta zandauka. Yace ai haj. Amman ta iya komai wallahi. Ta numfasa tace to shikenan. Yarinya meye sunanki. Tace afrah. Nan tace zakimin shara kawai. Sai goge goge zaki iya?. Afrah dasauri da murmushi afuskarta tace eh. Sai hajiyar tace. Wuni zakiyi ko kwana dasauri aminu yace kwana haj. Tace ahto badamuwa. Inkika zauna dani da zuciya daya xaki moreni sosai afrah murna kamar ta tashi ta rungume matar. Haka suka gama bayani akan awata zaabata dubu biyar. Aminu godiya yayi tayi. Nanfa yaje gida gabansa nafadi. Kar innansa tace dagangan yace kwana. Saidai badamuwa yariga yashirya mezaice, Isarsa keda wuya. Yazauna yaci dumamen tuwonsa yakora dakunun kanwa. Yayi gyatsa yadade baici abinci cikin kwanciyar hankali irin nayauba. Innar tafito tace ina matsiyaciyar?. Yace wallahi inna matar galadima ce tariketa wai saidai tayina kwana zata bata dubu biyar awata. Nanda nan inna tahau murna jin ance dubu biyar. Tsohuwa mai idon naira. Nanfa tuni tamanta da maganar wata afrah. Cangun afrah kuwa. Haj.fatima wacce take uwargida agun galadima tabata wani daki. Harda gado da tabarma anshinfida tace ki saka kayanki anan. Anan zaki dinga xama. Nan takira wata kuyanga tanuna wa afrah yadda zatayi. Amman haj Ta aika aka siyo sabulai tabawa afrah tasa kuyangannan tamata wanka tadirjeta. Tabata kaya duk daba sabbine ba masu kyan gani. Afrah taji dadi sosai.Hakan yasa tasaki jikinta Zamanta agidan yasa tacanja sosai. Dasafe inta tashi tagaishe da haj. Tayi shara da goge tawanke bandaki. Sai takarya shikenan tayita zama wani lokacin takan shiga cikin gidan tadan taya kuyangun aiki. Duk da akwai saointa acikin yaran amman bata shiga cikinsu. Tana tsayawa a inda Allah ya ajeta don afrah nada zuciya sosai bata daukar shiririta duk da kankancinta. Hajiyar tasha zama tayi nazarinta . Wannan da ace baasantaba xaace daga gidan sarauta tafito halayenta sak irin na yayan gidan sarauta ne gatada shiga rai. Kowa nasonta. Inta zauna dakai dole kasota afrah kenan! Dare dare akanyi karatu ga yaran galadiman acikin gida . Hakan yasa haj tace afrah tadinga xuwa. Sannan dayamma akwai islamiya agefen gidan galadiman. Nan afrah zataje bayan windown ajin tazauna. Ana koyamasu itama tanayi.Takanyi mamakin yadda ake koran yaran galadiman suje makaranta suna guduwa gata ita tana nema ido arufe.…… Kukasance tare dani a part 8 KECE GUDALIYA ×××××××××PART 8×××××××× Aduk sati aminu yakanje yaganta. Ya balain jin dadin yadda yaga tacanja. Kamar ba itaba. Ahaka tacika wata haj tabata kudinta. Ta ajiye lokacin da aminu yaxo tadauka tabashi. Lokacin daya ce ta ajiye tace aa bata bukata domin cida sha da sutura duk tasamu. Tace yakai wa inna . Dolensa yakarba yakaima inna. Inna dadi taji sosai. Nanfa suka dantse kudi. Acikin wani sati dan hajiyar wanda yake zama a abuja da matarsa zaixo. Nanfa akashirya tsaf komai bayan yaxo. Afrah tana daki haj. Takirata takaimasa kayan dazaici. Ananfa haj. Akan yanaso karamar yarinya afrah saboda tana taimaka masu dawani abun. Hajiyar tace badai wannanba matarka dasonjiki ni bansan wani irin aure kukayiba. Ya sosa keya yace sai hakuri ai . Nanfa dakyar yace abar masa afrah yatafi da ita. Haj. Takira afrah tace zaki birni?. Nan afrah tadaga kai tare da cewa in yaya aminu ya amince zani. Nan tace indai aminu ne badamuwa Allah yakawoshi lafiya. Dahaka suka kwana washegari hajiyar ta aika akira mata aminu yaxo tagayamishi bukatarta bakaramin girgiza yayiba.Sai dai bazai iya musa mataba . Don hallarcin daya mata. Haj takara dacewa karka damu zata dinga xuwa hutu. Sannan har makaranta zai sata ka kwantar da hankalinka. Nanfa ta lallasheshi sannan yace to. Sukayi magana akan zataje tayi sallama dasu inna. Sunfito tana biye dashi. Yace wato so kike kitafi kibarni?. Tace aa yaya wlh naji ance makaranta. Har suka isa gidan suna tattaunawa. Bayan shigarta inna tace kardai kinyi laifi sun koreki kinmana bukulun arxiki. Nan aminu yace haba inna . Nan suka zauna yagayamata komai. Tace to nidai a dinga turo mana da albashin. Shikam al-amin mamaki yakeyi sosai. Yadda inna take son kudi. Bayan tayi sallama yakara janta suka tafi gidan galadiman . Anan ya tsaya yana kallonta yace afrah tace naam yaya. Yace duk da karancin shekarunki nasan kinada basira don Allah kitaimaka inkinje kikama kanki kiyi biyayya. Sannan kar yan birni su hure maki kunne. Yana maganan muryarshi na rawa alamun kuka zaiyi. Itakam tuni tafara kukan. Yace kituna aduk inda kike ! KECE GUDALYA acikin ruhina . Ina rainonki araina. Allah yasadamu da alheri. Yajuya zaitafi dagudu tabishi tana yaya . Juyowar dazaiyi kawai yarungumota kuka yake sosai. Itama kukantake. Ahaka dakyar suka rabu babu mai lallashi harta koma yatafi. Ranan batayi baccin kirkiba. Tana jimamin barin al-amin gakuma dokin xuwa birni. Washegari karfe bakwai haj. Tashiryata tsaf tace mata inkinje . Matarsa ce kawai basu haihu ba. Sai kaninsa duk yayanane kiyi biyayya yadda nasanki. Ahaka sukayi sallama,Haj harda kwallarta.Nan tashiga gidan baya acikin mota prado. Sanyin Ac. Ne ya ratsa jikinta itadai tasaba jin wannan kamshin ne kawai idan tana falon haj. Suna tafiya yakunna karatun qurani. Inda taga ma ta iya donhaka tafarabi. Ahaka bacci ya kwasheta . Tohfa afrah tabar garin gombawa dibar fari. Zata nufi garin abuja.… Kukasance tare dani a part 9 KECE GUDALIYA =======PART 9 ======= Gab da laasar suka shiga garin abuja har anguwarsu maitama. A lokacin afrah ta tashi. Bayan horn dayayi ma maigadi yabude tsararren gidan. Tsabar kallo afrah bude baki tayi. Ashe titi da wuta datagani har motoci nafila ne akan kaftareren gidan dasuka xo. Parking dayayi daidai dafitowar wata mata fara ce tas kyakkywa zakace irin shuwaaraf dinnanne. Doguwar rigace ajikinta dagudu ta rungume shi oyoyo darlin. Nan suka shiga wata duniyar afrah kam kunya tarufeta ga jaka tarike a hannu. Kiciniyar bude booth ne yasasu dawowa hankalinsu haryace dear ga mai taimaka miki nakawo maki ita. Tadan yamutsa fuska oh to badamuwa. Nan afrah ta rusuna tagaisheta. Ta amsa ba yabo ba fallasa. Sunshiga inda aka nuna mata fannin dazata zauna. Nanma kallo tayitayi harda ac. Da gadonta babba . Ga bandaki dakuma wardrobe. Tazube tashiga bayangida tayo alwala sannan tayi sallah a kankanta shekarunta tasan illar barin sallah.Idarwarta keda wuya yaya babba yashigo tare dacewa fito kici abinci tabishi sukafita. Kitchen yanufa da ita taga yabude leda takeaway yafitar yabata shima yadau daya tare dazubawa a plate yadau cokali yanufo falo. Itama hakan tayi saidai tanufi daki. Tanacin abincin tana mamaki itadai a saninta abincin siyarwane akesawa acikin abun takeaway. Toh meyasa matarsa bata masa girkiba?. Kamar yadda hajiya takewa galadima idan yayi tafiya kafin yadawo ayi abinci kala kala azuba masa. Sai inda yakoshi. Amman shikam gakudin saidai wayam. Wata zuciyar tace meye ruwanki a ciki. Kikasani ko matar batada lafiyane?. Nanta basar tagama cin abincinta anan bacci ya kwasheta. Sai magriba tafarka tafita kitchen anan taga yaya babba yana fera dankali tace yaya kawo intayaka. Nan yace tazauna su fere tare. Duk da Allah yayisa da kyankyami bayacin abincin maaikata hakan yasashi tunda amina matarshi bata girki shiyake shiga yayi abunsa. Suna ferawa yana tambayarta abubuwan daya shafi addini. Yaga ashe yarinyar tanada dan sani. Ga wayau da basira dayayi mata yawa. Sukagama. Yakoya mata yadda ake kunna gas tare dacewa kinga inbani gida saikixo kigirka. A banki nake aiki. Sai dare nake dawowa. Amina bata girki. Nan takalleshi kamar zatayi magana saita basar. Suka soya dankalin da kwai yahada tea kakkaura yadibi nasa yatafi falo itama tadiba nata tayi daki. Anan taci tayi kyam kafin ta tashi taxo tawanke kwanukan tayi sallahr ishai. Sannan tayi wanka tabi lafiyar gado! Aminu kuwa tun tafiyarta yabi yasusuce yawani dawo takar wani mara lafiyar doke kwance. Har yasa mutane sukagane kowa lafiya yau haka?. Baitaba sanin yashaku da afrah ba sai ranan. Wani irin kaunarta yakeji. Lalle SO GUDALIYA ce. Sannan so haukane. Inbahakaba yarinyar dabata dara shekara 12 ba meye abunso?. Wata zuciyar kuma tace gamo najini ne.…… Kukasance tare dani a part 10 KECE GUDALIYA °°°°°°°°°PART 10°°°°°°°°° Washegari dasafe afrah tayi sallarta. Don babban yaya yatasheta da asuba yana tashinta yaga tamike. Sabanin matarsa dasai safiya garau take sallah. Sunfito kenan . Rigar baccice ajikinta. Tana mika shikuwa kofin teans ne a hannunsa yana nazarinta. Takaraso tana cewa hello darling! Ya murmusa tare dacewa yakike. Ta sunkuya ta sumbaceshi. Nan yaji jikinsa yayi laasar. Yanadaga cikin dalilin dayasa yagagara kara aure ko rabuwa da amina. Tasan kissa da kisisina. Magananta ma kadai abun kalloce.Kan mu gangaro gun kyau . Amina yar maidugurice shuwa arab. Bakaramin kashe kudi yayi gun aurotaba. Kasancewarta boti wato ajebo. Yazama ko indomie bata iya dafawaba. Bakaramin matsala suke fuskantaba tagun zamantakewa. A inda yadauko wata takoyamata amman amina tayi kif da ido tace aa. Bazata wahalaba. Kalar ta tsufa yakara aure!.Akwai tsaftan jiki kam amman banda muhalli. Jikinta kullum acikin kamshi yake tarike maganin mata. Amman ba abinci bana muhalli. Yadauko mai aiki amman kememe tahana ita adole mai kishin mijinta. Dole yasa namijine yake share share da wanke wanke da sharadin tana daki zaiyi komai yafice. Gata da rashin son zumunci. Donma anyi saa zuriyar galadiman bamasu daukan raini bane. Hakan yasa bata masu .afrahnma tun yana billiri yace mata hajiya tabada yar kanwata yataho da ita don taimaka mata. Hakan yasa tayi shiru donba yadda ta iya. Sannan aduk lokacin data bukaci abu yahanata to shima dole tadana masa . Donta karance shi tsaf tasan halinsa. Bamai neme nemen mata bane.Sannan gashi dayawan bukata aduk randa yamata taurin kai. Rannan baccin kunci zaiyi donkuwa tasan hanyar maganinshi. Hakan yasa yake tsoronta ko maganar wata bayayi balle ace neman aure. Gashi taki su haihu duk da haryau baisaniba. Kwayuka takesha abunta. Suna neman shekara biyar kenan. Hajiyarsa tayi tayi yakara aure yaki. Batasan badagashi bane. Uwarsa ta abuja ne tahanashi wato amina.…… Kukasance tare dani a part 11 KECE GUDALIYA ********PART 11******* Alhaji muhammed galadima haifafen dan billiri sannan dan billiri wanda ya ajiye iyalansa acikin garin. Yanada mata fatima wanda akafi sani da hajiya babba. Ita yar garin dukku ce. Wadda sukahadu tun kuruciya sukayi aure . Mata mai cikar kamala wato wacce afrah tazauna agunta. Haihuwarta bakwai amman basu rayuwa duka ba Biyune suka rayu. Wato usman Yaya babba kenan. Saidan autanta Ahmed. Hakan yasa dakyar galadiman yakara aure da Aisha inda ta zube masa yaya uku duka mata itakuma. .Anacemata anty amarya. Farkon yarta sunanta salamatu wacce akaimata aure da dan sarkin dukku tahaihu amman Allah yayi wa yar rasuwa don ko ganin yar batayiba. Saikuma Hafsat itama tayi aure da yayanta biyu acikin garin gombe. Yar autarta Hussiena itace batayi aureba tana zama agun salamatu tana karatunta. Gidane na mutunci da kamala. Kowa yasan mutuncin juna. Ga su da farin jini duk inda suka shiga. Abun hannunsu bai tsole masu idoba. . Zuriar galadima kenan!. Afrah bayan karyawa tafito inda tagaishe da babban yaya da anty amina. Inda babban yayan yace afrah tunda kin iya girki zakidingayi . Akwai masu hidima afrahn tace to. Tamike tanufi kitchen inda tahadu da abu mai aiki yanata wanke wanke suka gaisa tafara hada abun girki shima yaci gaba da hidimarsa. Fitar yaya babba yasa amina ta kwala mata kira tana zuwa takalleta sama da kasa. Tace ke kin tabbata ke kanwar sa ce?. Afrah tayi xuru xuru da ido kafin ta amsa sai aminan tace bar kallona da manyan idonki irin na galadima. Ku zuriarku kowa da manyan ido. Afrah dai tana shiru can tace kitashi kije kigyara min kan gado kigyaramin wardrobe. Sannan kije dakin yaya babban shima ki gyara ki wanke bayan gidan ki kimtsa. Sannan ahmed bayanan inyadawo shima zakidinga mishi inya amince don miskilin gaskene. Tamike tafice. Afrah taja dogon numfashi. Angudu baa tsiraba………… Kukasance tare dani a part 12 ♥♥ KECE GUDALIYA♥♥ ••••••••••PART 12•••••••••• Tamike tashiga dakin aminan nanfa ta tsaya. Dakin yasha kayan duniya kam. Gawanin sanyi da kamshi dake ratsata . Ta isa bakin gadon. Tafara gyarawa shikanshi gadon abin dubawa ne. Ta gyara shi tsaf kasancewar ta saba gyara na hajiya babba hakan bai bata wahala ba. Tagama tashare dakin ta goge duk daba wani datti bane. Ta wanke bandakin. Sannan tanufi fannin yaya babba shikuma tayi mamakin ganin dakin a birkice ba kintsi. Nan ta tattara komai ta gyara gadon ta wanke bandakin. Sannan tafeshe ko ina da room freshener bayan tagama tafice. Takarasa girkinta lokacin Abu yakammala nashi aikin har yafita. Gajiyar datayi yasa ta nemi gu tazauna. Zuciyarta namata sake sake. To itahaka zata kare a bauta? Duk inda taje bauta takeyi . Wata zuciyar kuma tace eh to dasauki ai. Yafi talla. Tunda kinacin mai kyau nanta ce alhamdulilah ala qulli halin tamike taje tayi wanka . Ta kimtsa sannan tafito falon takunna tv kasancewar duk takoya agidan hajiya babba. Tana kallon mbc 3 inda suke cartoon. Hankalinta duk nakan tv. Rankwashi taji anzuba mata. Wani kara tasaka gami da juyowa. Amina tagani a tsaye akanta tana fushi. Tace anty menayi?. Ubanki kikayi shegiya yar iska banacemiki ki gyarawa darlin wardrobe ba?. Tayi kasafai sannan tace waye darlin.?. Takaici yakulo amina kawai tazaro wayar cable dan ubanki ni kike cemawa waye darlin?. Ihu takeyi sosai. Ahaka tagama dukanta duk jikinta yayi radai radai takamo kunnenta tamata kashedi. Bari in gayamiki inma munafakar xuriarku sun turokine kisamun ido wallahy saina karkaryaki. Matsiyaciya. Tadaga hannu zata kwala mata rankwashi taji anrike hannun! Juyowarta keda wuya suka hada ido da babban yaya. Idonshi yayi jaa sosai. Har kamaninsa yarikida. Yace amina ni kike ciwa mutunci?.Tace menayi? Yace bansaniba najifa duk abinda kikace. Kinsan dayaya nadaukota ne?. Daga xuwa zaki fara takura mata. To wlh zaki sha mamaki. Yafizgo hannun afrah sukayo waje. Yacusata a mota nanfa yafara tuki afrah tagama tsorata. Sunyi tafiya har yakai wani gida yana xuwa yayi horn akabude. Yajuyo yacewa afrah. Nan gidan yayata ne salamatu. Itada hussiena yar autarmu. Zansaki a makarantar su husna. Kiyi zamanki anan kinji?. Ta gyada kai tace to nagode yaya babba. Amman karkayiwa anty komai ninayi laifi. Yace laifin mekikayi. Tace in gyara dakinta da naka dakuma na darlyn. Nikuma sainagyara naka da nata kawai. Ban gyara na darlyn ba. Dariya taso ta kufce masa amman yadanne. Lallai dole yasa afrah a makaranta. Suna shiga yayi sallama . Matar gidan tafito tanaganinsa tawage baki. Oh yau antuna damune ? Yace eh .Suka zauna bayan sungaisa afrah ma ta gaisheta. Nan babban yaya yace ina hussiena?. Tace tana xuwa. Takirata sukafito duk suka zauna sannan yalabarta masu komai. Tare dacewa wallah gudaliyan hajiya ce. Amana ce. Bazan iyaciba. Donhaka hussy awani skul kike? Ta ce turkish. Yace badamuwa. Zamuje acan tayi tafara. Adda salman tace to kana ganin zata iya coping? Tunda bata taba xuwaba. Nan yace tanada basira d gurl is smart. Yace yanxu hussy gashi yabata check din dubu dari.Anjima kudauki driver yakaiku shoprite ko grandsquare kitabbatar tasiya duk nessasary things sannan inkudin yakasa kumin magana.Adda salma tace aa tamin magana dai. Nan yafice tare dacewa zai dawo next week bayan yagama sheduling skul dinta. ……… Kukasance tare dani a part 13 ♥♥ KECE GUDALIYA♥♥ °°°°°°°°°PART 13 °°°°°°°°°°°° Bayan tafiyarsa husna tace zomuje daki nan sukaje dakinta. Tace kisake jiki kinji.? Nan afrah tadan ji dadi. Nan bayan sunci abinci sunshirya husyn tajata suka fita grandsquare suka nufa. Nantabata keken tace tarike ahannunta. Duk abinda kikeso kidauka. Nanfa afrah tarasa yazatayi ta tsaya kallo kawai. Hussy tashiga jidan kaya.kamar wanda kyauta zaabasu. Aikuwa sukaxo biyan kudin sai da suka ci kusan dubu dari uku.Donma adda salma takara musu kudinne. Maaikatan suka samusu kayan a mota. Suka dawo gida anan husy ta taya afrah tashirya wardrobe dinta tsaf. Sannan takira tela yaxo yakarbi dinkunan dazaiyi na afrahn. Haka tazauna agidan adda salman mutane masu karanci. Duk da husy tagirmeta akalla ita tanada shekara 17. Afrah kuma zamu iyacewa 11 xuwa shabiyu. Amman bata dauki girman kai tadaura ma kanta ba. Tunda taji ance gudaliyan hajiya babba hakan yasa take darajata. Tariketa tamkar kanwarta. Dasafe insun tashi zasu hadu su yi girki. Adda salma kam tarasa maiyasa take jin afrah aranta. Tanason yarinyar itakam.Afrah tanada shiga rai. Insungama suje garden din gidan suyi ta hira. Ahaka babban yaya yaxo yasamesu yaji dadi sosai . Yace kutaso muje skul din amman abuja international zannema mata Nan suka garzaya sukaje. Anan yayi bayani akace badamuwa akasata a primary 5 dakuma extra lessons datake. Ahaka yace tadage da karatunta. Kullum dasafe sukan shirya suje insungama azo adaukesu. Wasa wasa afrah hartayi comon entrance. Tashiga turkish js1. Duk wanda yasan afrah ada bazai tantancetaba. Gashi tafara girma tayi kyau. Gashinta mai santsi yakara bayyana. Haskenta mai kyau. Ga dara daren idanu. Masu fizgar hankalin mai kallo…………… Kukasance tare dani a part 14 ♥♥ KECE GUDALIYA ♥♥ ••••••••••PART 14•••••••••••••• Dahutu yayi suka tattara suka nufi gombe. Suna isa tayi gidansu aminu. Amman bataga kowaba. Ta tambayi makwabtansu sukace ai bayan tafiyarta inna ta kwanta ciwo . Wani dan uwansu ne yaxo yakwashesu duka harda aminu. Sunyi mamakin ganin yadda afrah tadawo. Hatta hajiya bakaramin dadi tajiba. Da daddare sun hadu ana tadi. Husy take cewa nikam hajiya wai yaushe yaya ahmed zaidawone?. Hajiyar tace sai nanda shekara biyu . Shima inyadawo wata daya zaiyi sannan yakara komawa . Inya koma baxai dawoba sai bayan yakammala. Tunda baidade da tafiyaba. Babban yaya yace amman medicine dinnan saida yadage saiyayi. Allah shi taimaka. Ahaka kowa yayi sashinsa. Adaren hajiya da afrah kwana sukayi suna tadi. Tana bata labarin komai. Hajiya tace amina wato zuriarmu ce bataso. Shiyasa take zaginki. Randa na tursasashi saiyakara aure. Afrah tana dariya tace haba hajiya. Yaya babba nefa. Tace babba? Aure naneman shekara shida ba haihuwa. Allah shi kyauta. Satinsu biyu suka tattara suka koma abuja. Inda afrah da husy suka koma makarantar a lokacin afrah tana shirin rubuta waec. Afrah na shirin shiga aji biyu. Duk makarantan ansan afrah gatada farinjini. Malamai da dalibai kowa nayinta. Gata batada girman kai. Baruwanta da shigeshige ko kwashe kwashen kawaye ba. Haka zalika tanajan mutuncinta gatadai karama amman akwai zuciya. Harta malaman suna mamaki don akwai wata rana. Afrah na assighment malamin yashigo ya karba. Taxo mika nata yace aa aitayi latti. Takoma taxauna. Kuma agabanta wasu suka mika tare dabada hakuri yakarba.Amman afrah ko ajikinta. Bayan antashi dayar yar ajinsu salamatu musa abubakar yar bauchi ce. Mutumiyar arziki. Ga faraa sosai. Tanason afrahn kuma duk makarantar sunfi shiri da ita. Salma dambam kamar yadda suke cemata tace afrah galadima. Bakiyi submitting assighnment dinkiba. Afrah ta tabe baki. Bar mutumin nan nabashi yaki karba sannan yaxo yakarbi nawasu agabana. Inace 10marks ne badamuwa.zanfito dasu a exams. Salma tarike baki haba afrah yakike haka.Baa zuciya da karatu fa.Afrah tace to ni nayi. Haka tahakura tabarta. Aikuwa yabawa afrah 0 a assighnment. Afrah duk da hankalinta yatashi amman tadaure tashare. Suna aji aka aika taxo taje tagaisheshi. Mrn sir! . Yakalleta sannan yabasar. Shiyarasa wacce irin yarinyace wannan gatadai karama sai fadin ran tsiya. Yace whats ur name! Tayi shiru tana kallonsa. Yadago ido yaga itama shitake kallo. Baisan lokacin dayace afrah galadima !!! Why are you staring at me?. Tayi murmushi tace sir. Dax my name.yace which ?. Tace d name u jex called naw! Goshinshi yadafa itakuwa murmushi takeyi kamar yadda tasaba. Yace get out!. Ko oho itakam tafice. Koda jarabawa yaxo yasa mata ido sosai. Itakuwa kullum addua take Allah yadaurata akanshi. Haka sukayi jarabawa suka kammala. Da result yafito afrah ce first. Kuma duk aciki subject din mutumin yafi scores. Taja gauron numfashi tare dacewa God save dix nigga!! Wasa wasa afrah har tafara shirin jsce alokacin dazata fara . Ahmed yadawo gida hutu yagama hutunsa yakoma. Kuma alokacin husy ma tazana ssce dinta. Duka suka kammala alokacin suka dawo hutu.kafin ita afrah takoma. Yayinda husy zata jira result dinta………… Kukasance tare dani a part 15 ♥♥ KECE GUDALIYA♥♥ •••••••••••• 15 •••••••••••••• A hutunne yaya babba yadamesu suxo gidanshi hutu bada son ransu ba.Sukaje saboda sunsan halin matarsa sarai. Sunje hutunnema hajiya babba takirasu suka dawo gida. Ashe biki akeyi hajiya kam tabawa yaya babba mata. Yar wazirin dukku yarinya kyakywa kamar ita tayi kanta. Husy da afrah na daki suna tattaunawa. Husy tace nifa wlh haj. Ta burgeni zamuga wannan shegiyar matarsan ina zatayi don kishi. Afrah tace ni har banson haduwa da ita tana ganina zata fara cewa. Idona kamar na galadima. Hussiena ta kwashe da dariya tare dacewa. Kumafa saidakika fada nalura. Wallahy idonki irin na baba galadima ne. Afrah tace ke bakiga naki idonba sai nawa . Anan wayar husy tayi ringing tana dauka tafara hello yaya ahmadu. Ow to sorry yaya ahmed. Yakake . Yace lau. Nanfa sukashiga hira tana bashi dariya. Har tace ga amanar hajiya ku gaisa. Afrah takarba taredacewa hello yaya. Yace yar amana? Tace naam. Ina wuni. Lafiya yakike. Lau yaya. Ya skul? Skul alhmdlh. Nan dai sukadan taba hira takashe wayar. Hajiya tashigo tare dacewa kai kuxo amuku kunshi. Nan suka fita aka musu lalle. Wasa wasa biki ya kankama.alokacin adda salma tabugawa amina waya kixo ayi biki dake . Duk da bata fahimci aurenwa ake ba. Haka dai tabiyo jirgi taxo. Nida hussiena ido mukasa muga ikon Allah don da alama batasaniba. Dare yayi muna daki mukaji hayaniyakam. Fitowar dazamuyi muka tarar amina kam sai zage zage.wallahy anci amana . Munafukan banza munafukan wofi.shine har zaku kirani nazo?. Kishiyar banza kishiyar wofi. To wlh ta shigo muzuba da ita. Kasancewar dagani sai hajiya saikuma husy. Hajiya babba tace meye haka kamar ba musulmaba. Nan tafara cewa ai kece babbar munafukar ai . Mara mutunci. Tsabar zafin zuciya afrah tace ke ki iya bakinki hajiyar zaki zaga?. Anzagan! Ayi hukunci mugani. Hussiena dasauri taje zata wankamata mari hajiya tarikota dole tahakura. Tana banbamin masifa hajiya kibarni inkoya mata hankali. Banza wacce batasan darajanmr mutaneba. Hajiya ta tuso kanmu. Mukashigo mukabarta agun. Yaya yana zuwa nida husy har rige rige mukeyi wajen fadamasa. Ransa yabaci yafara fada. Hajiya tace don Allah yimin shiru da bakinka. Agabana kaita cika baki. Agabanta mezaka mata?. Akwai abunda zakayine?. Yayi shiru can kuma sai yamike.nida husy haka muka kwana muna tadin abun. Washegari mukaci mothers eve. Sannan akaxo akayi dinner duk wannan hidimar basuga amina ba ashe tayi gaba abunta.………… Kukasance tare dani a part 16 ♥♥KECE GUDALIYA♥♥ °°°°°°°°°°PART 16 °°°°°°°°° Tana isa takira mamarta nan suka shirya kursullinsu. Afrah kuwa bayan gama biki suka tattara suka koma abuja da yan rakiyar amarya. Aka kai amarya gidanta. Afrah da husy Allah Allah muke muje muyi kallo. Donma abun dasauki tunda amarya ma ba tayar baya bace haka uwar gida adda salma ne tahanasu Hakadai suka hakura. Asatin afrah takoma makaranta. Koyaushe hussy nahanyar xuwa gaisheta har admsn dinsu yafito. Inda zata cigaba agun nile turkish sun bata biological science. Lokacin afrah na ss1. Suna shirin shiga ss2 ta kwanta ciwo . Zazzabi mai tsanani yarufeta dole aka dawo da ita gida. Hankalin babban yaya da adda salma yatashi musamman adda salma datakejin son afrah aranta wani kauna ta daban. Hajiya babba ma taxo nan suka hadu suna jinya. Ulcer ce mai tsanani tariketa. Anyi magani kamar baayiba.Akarshe adda salma tace tasan wani malami yana bada maganin gargajiya anan aka kira malamin yaganta yatausaya mata sosai saboda tafita hayyacintaYace tunda tana FAMA DA WANNAN MATSALA ZATA IYA SAMUN GARIN HABBAT SAUDA, DA GARIN KUMSARI,DA GANYEN ZAITUN MAILAUSHI, TAJI KASU TARIKA SHA INSHA ALLAHU ZAA DACE.Sannan kuma yace ta daura niyyar yin AZUMIN LITININ DA ALHAMIS kullum idan taci abincin sahur sai taci danyen kabeji mai dan yawa aqarshe, sannan kuma idan tayi bude baki da dabino sai tadora da kabeji, daganan har sai tayisallar IshaI kafin taci wani abu lokacin wannan kabejin yafaranarkewa, Yafara aikinsa.Sai ta aikata haka kamar na wata daya bafashi, In Allah yayarda zataga canji sosai.Kuma ta riqa shan (madarar akuya duk zata kwanta……………… Kukasance tare dani a part 17 ♥♥KECE GUDALIYA♥♥ •••••••••••PART 17•••••••••••••• Aikuwa wasa wasa saigata tawarke sumul. Saidai jarabawar wannan term din tawuceta .Maryam kuwa wato amaryar babban yaya har tana dauke da juna biyu murna kam bakanta. Anan husy take bawa afrah labari ashe tym danake skul. Lokacin da maryam tasamu ciki. Alokacin yaya yatusa aminar sukaje asibiti don complain. Nan likita yace magunguna hana haihuwar datasha su suka mata illa. Ananne babban yaya yayita sumbatu kin cuceni amina. Ban yafemikiba. Mena miki dabakison haihuwa dani. Amman alhamdulilah da Allah yakawo mai kaunata kije gidanku na sakeki. Nan tayita kuka. Husy tace hargun adda salma taxo ban hakuri. Adda salma tace bayanda ta iya. Karashe ta tattara tatafi. Sanadin dayasa yanxun dangi kowa nason xuwa gidan yaya. Afrah ma kasancewar tasamu sauki anan babban yaya yace tazauna. Suna zaune da maryam cikin mutunci da girmama juna. Wata rana afrah naxaune a falo tamike kafafu sanye da gajeren wando da wani spageti top. Ta tufke gashin kanta. Tayi balain kyau. tana sauraron wakar ashqui tum hi ho dake tashi awayarta. Kasancewar maryam da babban yaya sunfita. Turo kofar akayi . Juyowa tayi taga mutum atsaye. Gabanta ne yafadi. Tatashi tagudune ko ta tsaya? . Batare da sallama ba yawuce. Ko kallontabaiyiba. Dakin da tasan anacewa na yaya ahmed ne bata taba ganinsa ba . Nantaga yanufa. Jikinta yayi sanyi. Tohfa lalle. Amman ta basar tacigaba dajin wakarta hartana danbi.Budar kofar akayi sannan yace ke kina damuna ki kashe wayar. Zuciyarta tahau tafasa. Lallaima duk da yafita iko da gidan tunda gidan yayansa ne amman daraja dan adam da dadi ai. Bata kulashiba ta shareshi . Saima kara volume datayi tajuya masa baya. Tanakai gashinta taji an fuzgo wani kara tasaka tare da mikewa . Bai sake kanba tarike kugu. Wats dix! Meye haka baniso! Ya harareta nd hu r u?. Da confidence dinta tace AFRAH wacce tafi karfin wulakanci duk mulki da arxikin mutum. Tsaki yaja. Tare dacewa wallahy zanfasa miki baki. Tace mafashi!. Shifa ya harxuka harya daga hannu zai mareta tarike hannun tare dacewa HOLD ON!!!! Banson raini! Meye haka daga shigowa ba sallama kawuce nd kaxo kana neman fada! Wannan aladar turawace ai. Gwara kasani kai musulmine. Meyema sunanka?. Ahmadu ko?. Arayuwarsa tunda yake mace bata taba mai gautsin bakiba. Gawata kucila taxo tana dasa masa magana yagagara yin komai. Ba abunda ya tsana irin ace mishi ahmadu. Gashi yautafada baiyi komaiba. Cillata yayi. Tafada kan kujera. Taharareshi tace ka tsokona jaraba wallahy. Baikulataba yafice daki. Nan tazauna tunanin mezata masa.karar motarsu yaya babba taji nan tafashe da kuka sosai. Yaya nashigowa hankalinsa yatashi nan suka fara tambayar lafiy?. Saida tagama kukan adaidai lokacin ahmed yafito sannan cikin shesheka wancan ne daga shigowa yacire belt yayita bugamin shi. Ya finciko min gashi. Yana zagina don kawai yaji inajin waka. Habawa nanfa yaya yatunxura kai lafiyarka daga dawowa zaka takurawa yarinya?. Yace yaya yarinyar nan makirace wlh karya take. Afrah tace yaya shinshina hannunsa kaxo ka shinshina gashina. Ai zaaji kamshin gashin………… Kukasance tare dani a part 18 ♥♥KECE GUDALIYA♥♥ ××××××××PART 18×××××××× Aikuwa yaya yashinshina kanta yafizgo hannun ahmed yashinshina. Kamshi iri daya. Baisan lokacin daya kaimishi naushiba amman dagudu ya gauce. Haba yaya sharrifa takemin. Kamin shiru da bakinka. Ga shaidanan nagani. To wlh bata hakuri. Ya turo baki tare dacewa sorry. Afrah dasauri tace banjiba ka kara fada! Aikuwa yaya yatusa kanshi dole yaje gabanta tareda cewa kara maimaitawa. Dole yafada. Maryam kuwa sai kallo take. Abun yabata mamaki. Mutane kamar masu ganin hanjin juna. . Koda suke daki daya. Tana maimaitawa babban yaya. Yace kinsan wani abu?. Tace aa. Yace to yau suka fara haduwa. Nanta zaro ido. Tare da dafa kirji. Yace wallahy. Nanfa tace lallai. Ai wannan zaace tare suka girma. Yaya yayita dariya.Afrah kuwa suna shiga tadan rausaya kai tare dacewa sorry. Irin wato kwaikwaya yadda yayi bakinciki kamar yamutu. Ficewa yayi yabar gidan. Yana tuka mota hankalinsa duk ya gushe. Gidan giya yanufa yayi order. Nanyafara kurba. Duk atunaninsa yabar tuna afrah. Amman ina ita zuciyarsa kemawa gixo.Afrah kuwa saida tashiga daki taji kwata kwata bata kyautaba.wata zuciyar tace daidai kenan. Inbahakanai masa na zaimayar dake boyo boyi…………… Kukasance tare dani a part 19 ♥♥ KECE GUDALIYA♥♥ °°°°°°°°PART 19°°°°°°°°°°°° Suna zaune har babban yaya suka shige daki don yin bacci. Amman ta tsinci kanta dason jira taga yaushe zai dawo. Ahmed bai tashi dawowa ba sai daya nadare. Afrah kuwa takulu. Ta tabbata ba abun alkairi yake shukawaba. Yana shigowa tagal tagal yana sumbatu. Yarinya sai ikon tsiya. Duk inda naganta saina faffasa mata goshi. Tana kallonsa kukan takaici ne ya zubo mata. Meyake nufi?. Aikuwa bata ida tunaninta ba taji an makurota. Wani irin ihu tasaka. Wanda baya gidanma dole yaji. Aikuwa saigasu maryam sunfito. Innalilahy . Ahmed kasheta zakayi?. Babban yaya yahankadashi tare da mishi kallon kurilla. Innalilah. Ahmed yaushe kafara shaye shaye?. Maryam tace bayayine?. Inhakaneto abokan banzane! Babban yaya yazauna takaici da bakin ciki yarasa mezaiyi.Akarshe yamike yatusa shi adakinsa yakullo dakin. Yace kekuma duk lokacin dakikaganshi kigudu daki. Wataran inbamunan ai kasheki zaiyi. Nan suka shige suna jimamin abun. Itakam afrah komai ya kuncemata. Yamazaayi ace yana shaye shaye . Gaskiya da sake!!. Ahaka tashige daki. Tayo alwala tayi sallarta tayi adduoi . Tamike tabi lafiyar gado.Washegari taci kwaliya tsaf tafito donsuyi abincin rana tunda ita ba gwanar breakfast bace tashige kitchen tasamu Maryam tace yauke zaki mana girki. Afrah tace to anty zauna anan sai inna miki bayani kina ganiPotato soup sunan miyar,Zamu nemi albasa,tumatir,attaruhu,peas,g reen beans,curry,gishiri,maggi,mai,Alayyahu. A tafasa green beans da peas ki feredankali ki yayyanka shi cube shape ki markadakayan miya a blender ki soya sama-sama,Sai kizuba dankalin ki jiya ki rufe kamar minti 2 sai kizuba peas dinki da green beans aciki ki sakamaggi da gishiri da tafarnuwa idan kina bukata saiki barshi ya dahu kamar minti 10 time din da kikatabbatar dankalin ya dahu,sai ki zuba curry daalayyahu ki rage wutan yay kamar minti 3 zuwa 5 sai ki sauke. Anaci da shinkafa ko masa ko taliya. Sai maryam tace yimana shinkafan Kukasance tare dani a part 20 ♥♥ KECE GUDALIYA ♥♥ ×××××××PART 20 ×××××××× Anan suka shirya komai tsaf. Gida kam yakaure da kamshi. Sukayi serving akan dinning table. Maryam tace bari inje nakira yaya. Kekuma jeki kira ahmad. Tace bajiya anrufeshiba?. Maryam tace ai yabudeshi sukaje sallar asuba. Yadai koma baccine. Tace ni anty tsoro nakeji kada nashiga ya makuremin wiya. Maryam tayi dariya sosai tare dacewa habadai. Kedai jeki. Ainasanki kema ba tayar baya bace. Nanfa taja numfashi tahade rai ita adole kartaje yarainata. Tana zuwa tabuga kofar shiru ba amsa. Tayi sallama ba amsa. Hakan yasa ta murda kofar tare da cusa kai. Aikuwa taji an fizgota. Ihu zata saka yatoshe bakinta yarufo dakin tare dacewa nikikeyiwa rashin kunya ta daga kai tunda ba damar magana . Yabude bakin tare dacewa inkika min tsiwa sainacire bakin. Ta murkuda bakin kuwa tare dacewa kaciren mana saime. Duk abinda yaken nan idonta nakasa. Yace mara kunyar banza mara gaskiya to wai akan me zakixo kitarewa mutane agida?. Dago idonta tayi tana kallonsa. Azahirin gaskiya ita bashi take kalloba. Maana idonta nakanshi amman ta zurfafa wajen tunanin kalmar amsar dazata bashi abun yabashi haushi. Yayinda shikuma kallon datake masa yasa ya tsargu sosai. Manya manyan dara daran idanuwanta tsoron idon yake. Tunda yafara ganinta idon suke mika masa wasu irin sakonni. Bayason kallon su. Musamman intakalleshi kafin ta yi magana saitayi murmushi. Maana ta samo amsar bashi nan zata caka masa magana. Haka yanxun ma yafaru data tunano amsar bashi sai tayi murmushi tare dacewa natarewa mutane ne agida saboda wanda yakamata yazaunan baida daa. Baida ladabi. Baisan darajar dan adam ba Mashayin giyane, Mara kunya ne. Hannu yasako zai mareta adaidai lokacin yaya yashigo kai ahmad lafiyarka? Kadanne yar mutane kana mata mugunta?. Kai abunkafa yafara isata. Daga dawowarka jiya kabi ka addabemu. Yace yaya wlh batada kunya. Dallah yimin shiru shekara nawa muna tare da ita?. Bata ta6amin ba saikai jiya?. Toh kaida haj. Nan yafara ai hajiyar zata sauraren inku kunki sairarona. Sukaja afrah harsun fita tace yaya namanta wayata bari in dauko. Yace inzaimiki wani abu kiyi ihu zanxo yanxunnan. A zahirin gaskiya dagangan tabar wayar donta koma ta tsokaneshi. Tana komawa tashiga yabata rai mekikaxomin. Bata amsaba saidata dauki wayar sannan tagyara zaninta yadda zataji dadin gudu. Sannan tace naxo dubawa ne don natabbatar ko waazin danamaka yashiga ne. Kaikam dai karako maza a duniya ne kawai. Habawa yabiyota dagudu tafito aikuwa caraf suka hadu da yaya . Harzai koma yace wuce kaxo kaci abinci. Yaya nakoshi! Zan bata makarai inbaka shigeba. Dole simi simi yahau kan dinning. Bakin ciki bai isheshiba saidayaga afrah ce mai serving. Dataxo kansa bata tambayeshiba tacika mar plate. Kuma tasan cewa abinda yaya ya tsana kenan kace zakaci abinci kabarshi a plate to inyana gun saikacinye tas. Yamanta shikam yahauci can yaji yakoshi yamike zaifita yaya yace zonan. Dawo kacinye. Dakasan bazaka cinyeba kace tazubamaka, ? Laa yaya wlh bata tambayeniba. Karya kakeyi mu ta tambayemu balle kai. Afrah ta sunne kai dariya kamar ta cinyeta. Yanaci yana guna guni yana turamata sakon harara da zagi………… Kukasance tare dani a part 21
Posted on: Thu, 09 Oct 2014 16:34:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015