KWAMITIN TATTAUNAWA NA KASA: Makiyan Arewa Sun Samu Wuka Da Nama - TopicsExpress



          

KWAMITIN TATTAUNAWA NA KASA: Makiyan Arewa Sun Samu Wuka Da Nama Daga Wakilanmu Ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban kasa Goodluck Jonathann ya kafa kwamitin bayar da shawara dangane da taron tattauna makomar kasa, wato National Conference. Kwamitin wanda ke karkashin shugabancin Dr. Femi Okurounmu. An kuma nada Akilu Sani Indabawa a matsayin sakataren kwamitin. Sauran mambobin kwamitin sun hada da: Farfesa George Obiozo, Farfesa Ben Nwabueze,Sanator Khairat Gwadabe, Sanata Timothy Aduda, Kanar Tony Nyiam, Farfesa Funke Adebayo, Dr. (Mrs) Mairo Ahmed Amshi da Dr. Abubakar Sadik. Sauran mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Dauda Birma, Malam Buhari Bello, Mr. Tony Uranta, sai Dr. Akilu Sani Indabawa wanda zai zama sakataren kwamiti. An bai wa wannan kwamiti makonni hudu ya kammata rahoton sa. Taron wanda za a gudanar da nufin cimma wata matsaya daya a wasu batutuwa da ke haifar da cece-ku-ce tare da kawo rashin fahimtar juna a dorewar tarayyar anaijeria. An dade ana neman gudanar da taron daddale makomar Kasar nan, inda kowane yanki ke korafin dannewa. Amma an fi nuna tsangwama ga Arewa, ana yi mata gorin cewa ita ce cima-zaune a kasar nan. Tun bayan hawan Arewa cewar tana amfana da kudin fetur a bagas, wanda ake hakowa a yankin Neja Delta. #RARIYA ta bi diddigin yan kwanitin nan domin tantance ko haduwarsu a wuri daya zai iya zama wata barazana ga Arewacin kasar nan ko a’a. 1. Dr. FEMI Okurounmu: Bayaraben Jihar Ogun ne, kuma daya daga cikin jiga-jigan Afenifere, kungiyar nan masu kare muradun Yarabawa wacce ta yi kaurin suna wajen tsanar ‘yan Arewa da duk shugabanni ‘yan Arewa da suka taka mulkin Nijeriya. Ya kuma yi fice wajen goyon bayan gudanar da taron daddale makomar Nijeriya. 2. FARFESA GEORGE OBIOKO: Ya taba zama jakadan Nijeriya a Amurka, kuma ya taka yin darakta janar na Cibiyar Nazarin Harkokin Kasashen waje. A lokacin da yake matashi, ya yi wa Biafra hidima sosai yana kaiwa da komowa ga dakarun Biafra a lokacin da yana matashi. 3. FARFESA BEN NWABUEZE: Babban lauya ne wanda ya yi kaurin suna waje hakikicewa a yi zaman yiwuwa ko rashin yiwuwar dorewar kasar nan tare da juna.Ya taba yin minister.Yana a sahun gaban masu fitar da maitarsu a fili wajen nuna kiyayya da Arewa.Shi da Farfesa George ne ke wakiltar Kudu-maso- Gabas. 4. Khairat GWADABE: Asalinta daga jihar Kwara, ta yi sanata daga 1999 zuwa 2003, inda ta wakilci babban birnin tarayya, Abuja. ’Ya ce ga Abdulrazak, babban lauya, SAN, na farko a Arewa. Khairat ba gogaggiya ba ce a siyasa. 5. SANATA PHILLIPS TANIMU ADUDA: Babban abin mamaki, Sanata Aduda ne kadai aka dauko daga Majalisar Tarayya. A yanzu shi ne sanatan da ke wakiltar babban birnin tarayya Abuja. Ya taba yin mamba mai wakiltar Bwari da AMAC. Tunda ya zama sanata sai ya dauki rigar addini ya rataya a wuyasa. Majiya ta tabbatar wa cewa a kowace rana sai Aduda ya shiga fadar Shugaban kasa kasancewar sa babban yaron Patience Jonathan. Dan aikenta ne, wanda a ko da yaushe yana tare das u a cikin Aso Rock Villa, kuma majami’ar cikin gidan ce yake yawan shiga. Shi da Kairat ke wakiltar Arewa ta Tsakiya, jihohin da suka hada da Niger, Kogi, Kwara,Nassarawa, Benue, Plateau da FCT. 6. KANAR TONY NYIAM: Tsohon soja ne, wanda a ka taba kamawa dumu- dumu da hannu a yinkurin yi wa Janar Babangida juyin mulki, wanda su Nyiam da su Gideon Orkar suka shirya. Ya shahara wajen nuna kiyayya arewa.a juyin mulkin ne suka bayyana cewa sun cire wasu jihohi daga Arewacin Nijeriya, sun tura su Nijar. 7. TONY URANTA: Uranta wani marubuci ne, da ke nuna goyon baya ga shugaba Jonathan da jam’iyyar PDP. Shi da Nyiam ke wakiltar Kudu maso Kudu. 8. Dr. Abubakar Sadiq: Malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria. Makusanci ne sosai ga Mataimakin Shugaban Kasa, Namadi Sambo. Can baya ya yi abubuwan da suka nuna yana da kishin Arewa. 9. BUHARI BELLO: Ya taba yin sakataren hukumar zake ta kasa, kuma ya yi Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa. 10. DAUDA BIRMA; Dattijo ne da ya shafe sama da shekaru saba’in. Dan kasuwa ne, kuma ya taba yin Ministan ilmi a zamanin mulkin Abacha.ya yi neman takarar zama shagaban kasa a karkashin ANPP, da bai samu ba, sai ya yi daura zuwa PDP. Yana da tsatstsauran ra’ayin Jonathan ya zarce. 11. FARFESA FUNKE ADEBAYO: Kifin rijiya ce, ba mu san ta ba. 12. Dr. MAIRO AMSHI:’Yar jihar Yobe ce, ba a santaasiyasa da hidimar ayyuka na kasa ba. Dr. ALIKU SANI INDABAWA: Mutumin da yake da kima da cancanta da kishi, kuma zai iya kare mutunci, matsayi da bukatun arewa, Dakta Akilu Sani Indabawa, sai aka wayi gari an yi masa takunkumi da matsayin magatakarda maimakon ya kasance ‘yantaccen dan kwamati mai cikakken ikon bayyana ra’ayinsa da bukatunsa ta hanyar mallakar kuri’a kamar kowane mamba. Da akwai alamun bukatar hada Akilu fada da mazavarsa da jama’arsa, idan yunkuri da kokarinsa suka kasa gamsar da jama’a da masoyansa.
Posted on: Sun, 06 Oct 2013 05:56:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015