LABARI: An Gano Matashin Da Ya Yanka Tsohon Shugaban Karamar - TopicsExpress



          

LABARI: An Gano Matashin Da Ya Yanka Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ingawa Hukumar yan sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da cafke wani matashi mai shekaru 17 da laifin yanka tsohon shugaban karamar hukumar Ingawa, Alhaji Samaila Magaji. Idan ba a manta ba #RARIYA ta kawo muku labarin kisan tsohon shugaban karamar hukumar a gidansa dake rukunin gidaje na Barhim a cikin birnin Katsina, sai dai bayan binciken da rundunar yan sandan jihar ta gudanar ta bayyana wani matashi mai suna Abba Lawal, dan asalin garin Daura, a matsayin wanda yake da alhakin yin kisan. A lokacin da yake jawabi ga manema labarai, kwamishinan yan sandan jihar Katsina, Alhaji Muhammad D. Hurdi ya bayyana cewa matashin ya hallaka mamacin ne bayan sun aikata aikin ashsha (luwadi) a tsakanin su. A cewar mai laifin ya hallaka mamacin ne sakamakon alkawuran da ya daukar masa a baya, ya kuma kasa cikawa. Wanda a cewarsa an kore shi daga makaranta sakamakon mummunar dabiarsa ta luwadi, amma tsohon shugaban ya yi masa alkawarin zai maida shi makarantar, wanda hakan kuma bai tabbata ba. Sannan ya bayyana cewa kafin ranar da abin zai faru mamacin ya dade yana gayyatarsa gidaje a Kano da sauran wurare suna aikata mummunan aikin, daga karshe kuma ya gayyace shi gidansa, shi kuma ya tafi da wuka yanka shi, saboda bakin cikin kasa cika masa alkawari. A cewar kwamishinan yan sandan a lokacin da suka gano wukar da aka yanka mamacin suka nunawa Abba Lawal, wanda ake zargi, nan take ya fadi sumamme, sai bayan da ya farfado a asibiti sannan ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana duk yadda abubuwan suka kasance.
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 15:30:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015