LABARI DA DUMI-DUMINSA: DanAbacha Ya Koma APC Labarin da - TopicsExpress



          

LABARI DA DUMI-DUMINSA: DanAbacha Ya Koma APC Labarin da muka samu a wannan dare Muhammad Sani Abacha, ya canja sheka daga jamiyyar PDP zuwa APC. Majiyar # HAUSA24 ta sheda mana cewa dan Abacha a daren yau ya ziyarci Janar Muhammadu Buhari a gida, inda ya jaddada goyon bayansa ga takarar neman shugaban kasa da yake yi. Wata majiya ta daban dake da kusanci da Abachan ta ce ya yanke hukuncin ficewa daga PDP ne, saboda wani talla da Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya sanya a wasu jaridu, inda ya ci mutuncin shugabannin kasa da suka fito daga yankin Arewa maso Yamma, wadanda dukkan su suka mutu a kan mulki ciki har da mahaifinsa, Janar Sani Abacha. Gabadai gabadai APC Allah ya taimake mu Ameen
Posted on: Fri, 23 Jan 2015 23:45:16 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015