LABARI: Gwamnoni Sun Yi Wa Matasa 17 Da Suka Musulunta Ruwan - TopicsExpress



          

LABARI: Gwamnoni Sun Yi Wa Matasa 17 Da Suka Musulunta Ruwan Kudi Wasu matasa su 17 sun karbi addinin Musulunci a jiya, a babban masallacin Jumaa na birnin tarayya Abuja, matasan wadanda guda 15 daga cikin su duk yan kabilar Igbo ne, yayin da sauran biyun, daya Bayerabe ne, dayan kuma bahaushe. Gwamna Aliyu Wamakko na Sokoto da takwaransa Gwamna Malam Isa Yuguda na Bauchi kowannen su ya bada naira miliyan 5 ga matasan. Gwamna Rochas Okorocha na Imo ya basu naira miliyan 2, haka shi ma tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu ya bada gudunmawarsa ta naira miliyan guda. Matasan sun ce sun karbi addinin Musulunci ne saboda yadda suka fahimci aminci da rikon gaskiyar da yake ciki. Muhammad Kabir Orjiegbulam, mai gabatar da shiri kan addinin Musulunci a gidan telebijin na NTA Owerri ne ya jagoranci matasan zuwa babban masallacin Jumaar na kasa.
Posted on: Sat, 16 Nov 2013 21:11:46 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015