LABARI: Mutane 453 Sun Ki Yarda A Diga Wa Yayansu Rigakafin Polio - TopicsExpress



          

LABARI: Mutane 453 Sun Ki Yarda A Diga Wa Yayansu Rigakafin Polio A Sokoto Adadin mutane 453 ne suka ki yarda a diga wa yayansu maganin rigakafin cutar polio cikin kwanaki biyu a zagaye na 10 na shirin diga maganin a karamar hukumar Illela dake jihar Sokoto. Daraktar lafiya ta karamar hukumar, Hajiya Amina Jibril ce ta bayyana hakan ga manema labaran da suke duba aikin bada maganin a yankin. Wannan adadin mun same shi ne tsakanin ranakun Asabar da Lahadi, a gidaje 347 dake yankin, iyaye da dama sun ki amincewa a diga wa yayansu maganin. In ji Hajiya Amina. Ta ci gaba da cewa, sama da yara 46,000 yan kasa da shekaru biyar a yankin ake fatan diga wa maganin a yankin cikin kwanaki hudu, inda ta ce zuwa yanzu an yi nasarar diga wa sama da rabin yaran. Sannan ta yi fatan za a samu nasarar diga wa kaso casain da biyar cikin dari kafin kammala shirin a gobe Talata. Daraktar ta ce karamar hukumar ta samar da kayayyakin da suka hada da: farantan cin abinci na roba, kofuna, taliya, sabulai da kayan wanke bandakuna, da za a raba wa iyaye don jan hankalinsu su yarda a diga wa yaransu maganin. Sannan kuma yaran ana basu alawa da abubuwan wasanni. Kamar yadda shugaban karamar hukumar ta Illela, Alhaji Garba Sabon Gari ya bayyana, an fitar da kudi har naira dubu dari tara don samun nasarar shirin a yankin.
Posted on: Mon, 18 Nov 2013 22:25:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015