LABARI: Rikicin PDP Na Kara Zafi Bayan jamiyyar PDP bangaren - TopicsExpress



          

LABARI: Rikicin PDP Na Kara Zafi Bayan jamiyyar PDP bangaren Bamanga Tukur ta sanar da dakatar da Kawu Baraje, Olagunsoye Oyinlola, Sam Sam Jaja da Ambasada Ibrahim Kazaure bisa zargin mutane su da yi wa jamiyyar zagon kasa, duk kuwa da kotu ta tabbatar da halalcin Mr. Oyinlola a matsayin halattaccen sakataren jamiyyar na kasa. A martaninsa, Mr. Olagunsoye Oyinlola ya ce dakatarwar da aka yi musu ta sabawa doka tunda babu wanda ya tuntube su don su kare kansa daga zargin da ake yi musu kafin ace an dakatar da su. Ya kuma ce idan da gaske ne don me mahukuntan PDP suka kasa dakatar da gwamnoni da yan majalisu na jamiyyar da suka balle suka kafa sabuwar PDP. Shi kuwa, Ambasada Ibrahim Kazaure, ya ce babu mamaki don shugabannin PDP sun karya doka don kuwa halinsu ne. A cewarsa, PDP ba ta so a sasanta rikicin da ke cikinta kuma su sun daura aniyar rigima da jamiyyar.
Posted on: Tue, 12 Nov 2013 16:46:36 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015