LABARI: Sojojin Nijeriya Za Su Yi Hadin Guiwa Da Na Kasashen - TopicsExpress



          

LABARI: Sojojin Nijeriya Za Su Yi Hadin Guiwa Da Na Kasashen Turai Don Yakar Ta’addanci Sojojin kasar nan za su yi hadin guiwa da sojojin kasashen Ingila, Amurka, Spain da Netherland don yakar ta’addanci. Tuni wasu daga cikin sojojin kasashen sun iso kasar nan don fara atisayen hadin guiwar da rundunar sojojin ruwa na kasar nan. Admiral Babalola Ogunjimi, shugaban kula da atisaye na rundunar sojojin ruwan kasar nan ne ya bayyana hakan jiya a Abuja, inda ya ce sojojin kasar nan guda 150 ne za su shiga cikin shirin, wadanda aka zabo daga sojojin kasa, na ruwa da na sama, sannan sojoji guda 739 ne za su zo Nijeriya don gudanar da shirin. #bashir_idrees
Posted on: Mon, 07 Oct 2013 18:49:38 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015