LABARIN DRIVER DA KWANDASTAN SA, wani driver ne ya cika mutane a - TopicsExpress



          

LABARIN DRIVER DA KWANDASTAN SA, wani driver ne ya cika mutane a motar sa, toh lodin da yayi yayoshi ne daga neja zuwa maiduguri, toh kwandastan motar gaskiya bai dade da fitowa daga gidan mahaukata ba, sakamakon hauka da yayi, motar tasu irin doguwar nan ce, tana diban mutane kusan 50, nan dai akayi lodi, aka kama hanya, ana cikin tafiya, sai fasinja su mikowa kwandasta kudi, suce ungo kudin mota, sai yace dasu, a,a ku rike bai ce na amsaba, kowa acikin motar saida yamiko masa kudi, amma yaki ansa, akaje maiduguri kuwa, kowa ya sauka daga cikin motar, aka rage daga driver, sai kwandasta, driver yacewa kwandasta, yawwa, nasan kudinnan sun haura dubu 100, ko? Banisu, kwandasta yana budar baki sai yace, kudin me? Driver yace wadanda ka ansa mana, kudin mota, kwandasta yace, to kace na ansane? Ai bakace na amsaba, sunbani nace su rike, bakace na amsaba, gashi kowa na cikin motar yayi tafiyar sa, wai idan kaine driver nan me zakayiwa kwandastan naka??? Admin prince abubakar sadeeq.
Posted on: Thu, 05 Sep 2013 12:27:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015