LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN .. Dagan an Qai yace, sai na kasa - TopicsExpress



          

LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN .. Dagan an Qai yace, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta.Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali. Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa: “abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka baiwa mahaifin Majnun wato Qais shawara da ya daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce shi da ya roqi Allah ya cire masa son Laila! Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . ataqaice haka majnun ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi! Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni said a rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta. Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa! Haka fa Allah yake jarabtar wasu da soyayya, dan haka idan kaji .............. na sambatu akan ................ kada ka zarges hi. KARSHEN LABARI
Posted on: Wed, 29 Jan 2014 08:48:15 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015