LOKACI SHINE RAYUWAR ‘DAN ADAM - TopicsExpress



          

LOKACI SHINE RAYUWAR ‘DAN ADAM Bismillahir-Rahmanir-Rahim...... Jiya ta wuce, yau itace taka, gobe kuma gaibu ce! Ma‘ana: Duk abinda ka gabatar a jiya, ita jiyan ta wuce, ba zata dawo ba! Yau ko da kake rayuwa a cikinta itace kad‘ai damarka, inka ribace ta da ayyukan alkhairi to, ka rabauta. Gobe ko ba ka da tabbacin kaiwa gare ta, shin zaka wuce yau har kakai goben? Don haka yau d‘innan itace damarka ta guzuri domin tafiya gidan gaskiya wato. Abdullahi Bin Mas‘ud (RA) yana cewa: (Ban ta‘ba nadama a yinin da rana ta fad‘i ba, irin yinin da gashi ina kusantar ajalina, amma ban Qara komai cikin aiki na ba). ‘Dan‘uwa kana lissafin irin awannin da kake tozartawa a wurin aikin kawai ba tare da anfanu da shi ba? Yaushe ka ta‘ba yin tunanin muhimmancin lokaci a rayuwarka? Kasan cewa nunfashinka a Qididdege yake? Ya zo a Adabul Mufrad cewa: A kullum muna yin nunfashi dubu ashirin da hudu (24,000). Allah yasa muyi anfani da lokutanmu wajen aikata alkhairi. (Ameen)
Posted on: Sat, 14 Sep 2013 20:50:41 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015