Labaran Soyayya #Abul Adfal Da Mai Tambaya #Kashi na 2 - TopicsExpress



          

Labaran Soyayya #Abul Adfal Da Mai Tambaya #Kashi na 2 (Maimaitawa) Yawancin amsoshin da samarin suke bayarwa sun hada da cewa: 1. Akan yi amfani da ido wajen kallon masoyi/masoyiya, wajen kallon soyayya, ido yana qarawa masoyi/masoyiya kyan gani. 2. Hanci yana taka rawar gani wajen shaqar qamshin turaren da masoyi/masoyiya tasa/yasa, wajen gane ko mutum yana da tsafta, wajen ganin kyawun masoyi/masoyiya da kuma wajen qara fito da siffar masoyi/masoyiya. 3. Da baki ne ake fara soyayya wajen furta cewa ina sonki/sonka, dashi ne ake fadawa juna kalamai masu dadi, baki yake qara fito da kyawun masoyi/masoyiya; wasu sukan qara da cewa akan yi amfani da baki wajen sumba*ar masoyi/masoyiya. 4. Da kunne ne ake karbar saqonnin baki daga bakin masoyi/masoyiya, sannan kunne yana qara fito da sura da kyawun masoyi/masoyiya. 5. Zuciya itace matattarar soyayya, itace take yarda da bada umarnin cewa a so masoyi/masoyiya, a cikin zuciya ne ake jin haushi, farin ciki, qiyayya da kuma SOYAYYA. A cikin zuciya ne ake ajiyar soyayyar masoyi/masoyiya da so da qaunarsa gaba daya. Haka dai Yasmeen taci gaba da samun baqin samari kala-kala; duk da dai bata samu wanda ya bata gamsassun amsoshin da suka dace da tambayarta ba, amma hakan yasa ta qara sanin halayen maza mabanbanta da kuma yadda suke bi wajen ganin sun sace zuciyar mace da kalamai masu dadi, abinka da wacce ta saba, hakan baisa koda da wasa taji tana son wani daga cikinsu ba, sai dai kawai tasan lallai akwai mazan da suka cika akira su da maza, masana soyayya, masana kuma qwararru wajen farantawa mace rai da kyautata mata, maza wadanda suka san tarairaya da shagwaba mace, mazan da lallai duk macen da ta same su a matsayin mazan aure, to tayi dace! Yau ranar litinin ne ya cika sati na biyu dai-dai da bada sanarwar tambayoyin Yasmeen a gidan rediyon Muryar Masoya. Kamar kullum Yasmeen ta fito falon taryar baqin samari dan sauraron amsoshin daza su bayar. “Yau kuma wa muke dashi akan layi?”, Yasmeen ta tambayi Haleema wacce ke zaune a gefe daya, Haleema ta dauko takardar jerin sunayen wadanda za’a gana da su ayau, “Abul Adfal, shine akan layi”, “Abul Adfal? Wannan wanne irin sunane?”, Inji Yasmeen. Abul Adfal ya shigo falon ya zauna yana jiran fitowar Yasmeen a yayin da yake tunani a cikin zuciyarsa, “ita kuwa wannan yarinyar menene matsalarta? Irin wannan katafaren gida haka? Mai zai hana…”, tunaninsa ya katse lokacin da siririyar muryar mai zaqi tayi sallama, Abul Adfal ya amsa sallamar tare da daga kai ya kalli Yasmeen. Yanzu ne ya gane cewa lallai da gaske ne sai dai a kwatanta makamancin yadda kyawun Yasmeen yake kamar yadda mutane suke fada, amma inba haka ba lallai ne kyawunta ya wuce misaltuwa! “Malam Abul Adfal kafin ka fara bada taka amsar zanso in san menene ma’anar wannan suna naka”, Yasmeen kenan take tambayar Abul Adfal. “Abul Adfal sunan larabci ne wanda yake nufin ‘Baban Yara’, “ok, to ina saurarenka, menene amsar tambayoyin nawa?” Yasmeen ta tambayi Abul Adfal. “Malama Yasmeen a nan qasar kika girma?”, Abul Adfal ya tambaya, “ban gane ba, kaida ya kamata ka bani amsoshin tambayoyina kuma zaka zo kana tambaya ta?” Yasmeen ta bashi amsa. “Eh hakan ne, amma ina ganin ai babu laifi dan nayi shimfida ga bayanin nawa ko?”, “ok, to a qasar nan na girma, amma ba’a nan nayi karatun gaba da sakandire ba” inji Yasmeen. “Kinsan wani littafin Hausa da ake kira Magana Jari Ce?”, “Wannan wacce irin tambaya ce? Wanene bai san Magana Jari Ce ba a qasar Hausa?”, “Kamar yadda na gaya miki ina son inyi shimfida ne kafin in baki amsarki, misali nake so in kawo miki. Akwai wani labarin wata ‘yar sarki da tayi tambaya makamanciyar taki, tace duk wanda ya amsa mata tambayar shi zata aura, daga qarshe ta samu wani dodo daga cikin dodanni ya amsa mata kuma dole ta cika alqawarinta na aurenshi, duk da dai cewa babu dodo a gaske; amma bakya tsoron wani mutumin da bai dace dake ba yazo ya bada amsar? … jama’a na gaji da rubutu mu hadu a kashi na 3
Posted on: Tue, 23 Jul 2013 16:13:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015