Lallai manzon Allah (S.A.W), ya bayyana mana cewa: Allah ba ya - TopicsExpress



          

Lallai manzon Allah (S.A.W), ya bayyana mana cewa: Allah ba ya dauke ilimi daga cikin al’umma, daukewa, (kawai a wayi gari a ga malami ya koma jahili, a’a, sai dai) Yakan dauke ilimi ne ta hanyar dauke malamai, har a wayi gari ba sauran malami sai tarin jahilai, wadanda za su dinga batar da kansu kuma suna batar da al’umma, a duk lokacin da wata matsala ta addini ta taso. A wayewar garin Juma’a, 21 ga Safar 1431, daidai da 5 ga Fabrairun 2010 ne al’ummar musulmin wannan jaha ta Kano suka wayi gari cikin alhini da jimamin rasuwar babban malamin nan, mai tsoron Allah, wanda ya tafiyar da rayuwarsa a bisa koyi da koyarwar sunnar manzon Allah (S.A.W), malamin da bai dauki kansa komai ba. Mutum na Allah, mai kankan da kai, mai karantar da sunnar fiyayyen halitta, watau Sheikh Abubakar Husein Fagge. Allah Ya yi masa rahama. A safiyar wannan rana ne da misalin karfe goma, dubban masoya da daliban wannan bawan Allah suka sallaci jana’izarsa, cikin jimami da alhinin wannan gagarumin rashi, wanda Allah ne kadai zai iya maye gurbin abin da aka rasa. An binne malamin a babbar makabartar dorayi, bayan an sallace shi a wannan wurin. An haifi Sheikh Abubakar Husein a wajen shekarar 1963, a garin Dawakin Kudu da ke Kano. Inda daga baya ya dawo hannun kakanninsa da ke Unguwar Fagge a garin Kano. Malam ya taso a wannan unguwa ta Fagge inda ya yi karatunsa na allo a hannun Malam Ahamad da ke layin Mai kashin rago. Daga baya kuma ya koma layin Famfon Kurma wajen Malam Abdullahi Danzarmo. Ta bangaren ilimin boko kuwa, marigayi Sheikh Abubakar Husein ya halarci makarantar GATC Gwale, daga nan kuma ya sami Higher Islamic Diploma, sannan ya sami matsayin kammala digirinsa na farko da na biyu a Jami’ar Bayero da ke Kano. A wannan lokaci na rasuwarsa har an kammala shirye- shiryen tafiyarsa zuwa birnin Sudan domin kammala karatun digirinsa na uku watau Dokta. Har ila yau ba da jimawa ba ne, Malam Abubakar Hussein ya fara koyarwa a makaranta LEGAL da ke Kano. Haka kuma Malam tun a lokacin da yake karatunsa na farko-farko, ya yi kokarin samun damar zuwa babban Jami’ar Musulunci da ke Madina, amma Allah bai ba shi dama ba, watakila saboda rashin lafiyar da yake da ita a idonsa. Marigayi Malam Abubakar Husein, kusan a iya cewa yana daya daga cikin malaman da suka fi kowa yawan karantarwa a tafarkin sunnar manzon Allah (S.A.W). Domin kuwa duk ranakunsa na mako yana koyar da wani littafin a daya daga cikin wuraren da yake gabatar da darussa. A wata takarda da babban amininsa Dokta Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo, ya rubuta a kan rayuwar marigayin, takardar da aka rubuta da harshen Larabci mai taken WADA’AN ABA MUHAMMAD WA INNA ALA FIRAkIKA LAMAHZUWNUN, wanda za a iya fassara ta da cewa: Ban kwana da baban Muhammad, kuma mu game da rabuwa da kai masu bakin ciki ne, ya bayyana shi da cewa bai san wani wanda ya fi shi yawan karantarwa ba a cikin malaman sunna. Har ta kai yakan karantar sama da sau daya a rana. Kamar yadda Dokta Sani ya bayyana a takardar, “hatta a ranar Alhamis (jajiberen rasuwarsa), kafin rasuwar tasa da ‘yan awanni ya gabatar da darasi a unguwar Fagge bayan sallar La’asar, sannan ya je masallacin Juma’a na dorayi ya yi sallar magariba, ya kuma gabatar da wani darasin, domin ya yi ban kwana da dalibansa, ban kwana na karshe” “Ranakun da yake koyarwa har sun handame gaba daya ranakunsa na sati. A ranakun Asabar da Lahadi yana da darussa a masallacin Dokta Habibu Gwarzo inda yake karantar da littattafai da yawa, daga cikinsu akwai littafin Bulugul Maram na Hafiz Ibn Hajar, da Tamamul Minna na Sheikh Nasiruddinil Albani da Sharhin Arba’una Hadis na Sheikh Ibn Usaimin da littafin Kashfush Shubuhat na Sheikh Muhammad dan Abdulwahab da littafin Alwajiyz fi fikhis Sunnati wal kitabil aziz, na Sheikh Abdul’azim Badawi, da Usulus Salasa na Sheikh Muhammad dan Abdulwahab. A ranar Litinin, yana da darasi na littafin Bulugul Maram a masallacin Juma’a na Markaz Imamil Bukhari a Rijiyar Zaki. Ranar Talata kuma a unguwar Fagge a majalisin Ansarus Sunnah yana karantar da littafin Akidatul Wasidiyya, na Shehin Musulunci dan Taimiyya. Sannan a ranar Laraba a wannan majalisin dai yana koyar da littafin Aslu Siffati Salatun Nabiy, na Sheikh Nasiruddinil Albani. A ranar Alhamis kuwa, yana da darasi a majalisin da aka ambata bayan sallar La’asar na littattafan Annahwul Kafi da Assarful Kafi na Ayman Amin Abdul Ganiy, sannan da wani darasin kuma bayan sallar magariba a masallacin Juma’a na dorayi a littafin Bulugul Maram da Akiydatul Wasidiyya. Ranar Juma’a kuwa yakan yi wani darasin a unguwar Fagge, a majalisin Ansarus Sunnah a littafin Al-ibana fi Usulud diyana na Imam Abil Hasanil Ash’ariy da kuma littafin Al’usul min Ilmil Usuwl, na Sheikh ibn Usaimin. Haka kuma dai a wannan ranar yana da wani darasin bayan sallar Magariba a majalisin Tirayam na littafin Al-wajiyz fi fiqhu Sunnati wal Kitabil Aziyz”. Haka nan duk bayan wadannan, yana bayar da karatu ga daidaikun jama’a a lokuta mabambanta, duk lokacin da ya ga yiwuwar hakan. Koyaushe a rayuwarsa a cikin karatu da karantarwa yake. Harila yau, yakan yi tafsiri da azumi a masallatai daban-daban, kamar a Hotoro da Fagge, watau majalisin Triumph. Bayan haka ga shi kuma limamin Juma’a a masallacin Markaz Imamil Bukhari da ke Rijiyar Zaki a kan titin BUK da ke Kano. Kai! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, lallai an yi babban rashi! Wannan kawai zai iya bayyana wa mai karatu irin wawakeken gibin da aka samu wanda zai yi matukar wahalar cikewa wanda marigayin malamin ya bari. Malamin ya rasu ya bar mahaifiyarsa da matan aure uku da ‘ya’ya goma sha biyu, shida maza, shida mata, sannan kuma da dubban masoya da dalibai. Daga cikin daliban mallam akwai Mallam Inuwa Abubakar Juji, shugaban makaranta(headmaster) a daya daga cikin makarantun Musulunci (Islamiyya) dake Fagge, tare da bada karatun Hadisi a majalisin Zamfara dake unguwar Fagge duk Ranar litinin bayan sallar magriba. Haka akwai Mallam Abdulkadir Hussain mai tafsir a massallacin Thaqafa, Sheik Sale Hadisi a Massallacin Hotoro, Aminu hotoro Mkarantar Hotoron Arewa, Anas Inuwa(Salafi). Allah muke roko Ya jikan marigayi Sheikh Abubakar Husein, Ya alkinta bayansa. Ya Allah muna rokonKa da sunayenKa tsarkaka, a kan Ka jikan wannan bawa naKa , Ka daukaka darajarsa, Ka sa shi a aljanna, Ka ba shi ladan sadaukar da rayuwarsa da ya yi a tafarkin sunnar manzon Allah (S.A.W). Ya Allah ka yafe masa kurakuransa Ka gafarta masa zunubansa, Ka ba ‘yan uwa da iyalai da dalibansa hakurin jure rashinsa, amin, amin. Share
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 19:21:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015