MAHADI SHA JIRA (A) [1] HAIHUWARSA TA ZO TUN SHEKARU 255 BAYAN - TopicsExpress



          

MAHADI SHA JIRA (A) [1] HAIHUWARSA TA ZO TUN SHEKARU 255 BAYAN HIJIRA A CIKIN LITATTAFAN SHIA DA SUNNA • Manzon Allah (S) yana cewa: Da zai kasance bai rage ba sai kwana xaya a tashi qiyama – Allah ba zai tashe ta ba – sai Allah maxaukakin Sarki ya turo wani bawansa daga Ahalin gidana ya cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci. Malam Abu Daawud ya fitar da wannan Hadisin a cikin Sunan xinsa (Sunan Abiy Daawud: 6/241), kuma yace sanadin Hadisin ingantacce ne. • Daga Ummu Salamah tace; na ji Manzon Allah (S) yana cewa: Al-Mahdiy daga zuriyyata yake, daga Yayan Faximah. Abu Daawud ya fitar da shi a juzuinsa na 2, a shafinsa na 509 – Albaniy yace wannan Hadisin INGANTACCE ne. HAIHUWAR IMAMUL-HUJJAH AL-MAHDIY (AJJALALLAHU TALAALA FARAJAH) Abu bayyananne ga wanda yake bibiyar litattafai na Tarihi da Hadisai a tsakanin Shia da Sunna cewar babu wani kokonto a cikin haihuwar Imamul-Mahdiy sha Jira (Al-muntazar – ajjalallahu taala farajahu) cewar ta faru ne tun sama da shekaru dubu da suka wuce. Kuma lallai haihuwarsa ta kasance ne daren Jumaa, wato ranar Alhamis da daddare, 15 ga watan Shaban a shekara ta 255 ko 256 bayan Hijira, a cikin garin Saamura wacce take a Qasar Iraqi, kuma shi (A) Xa ne na Imamul-Hasan Al-askariy (alaihis-salam). Masana da daman gaske daga masu ilimin Tarihi da Hadisin Sunna ba ma Shia ba sun bayyana haihuwar Imamul-Mahdiy (A) cewar ta faru ne tun fiye da shekaru dubu da suka wuce, kuma har yanzu yana nan a raye kamar Annabi Isah (A). Wanda idan muka koma cikin littafin Allaamah Ash-shaikh Luxfullah As-Saafiy mai suna Muntakhabul-athar fiil-Imaamil- Mahdiy Ath-thaaniy Ashar, a hamishin shafi na 327, bugu na biyu a shekara ta 1403H, wanda Muassatul-wafaa, Beirut Lebanon ta buga, ya ambaci sunayen mutane 65 daga cikin Malaman Sunna waxanda suka bayyana haihuwar Imamul- Mahdiy alaihissalam, kuma dukkansu suna tabbatar da haihuwar tasa ne tun fiye da shekaru dubu da suka wuce. Don haka zamu kawo kaxan daga cikin maganganun Malaman Sunna a yanzu akan haihuwar Imamul-Mahdiy (A). MALAMAN SUNNAR DA SUKA BAYYANA HAIHUWAR IMAMUL-MAHDIY (A) 1) Aliyyu bn Al-Husain Al-Masuudiy ya kawo a cikin littafin Muruujuz-zahab a babin Yaqub As-saffaar, juzuinsa na 2, shafinsa na 124, ko a bugun Masar na shekara 1377H, 4/199 cewa: A shekara ta 260 an kama Abu Muhammad Al-Hasan bn Aliy bn Muhammad bn Aliy bn Muusa bn Jafar bn Muhammad bn Aliy bn Al-Husain bn Aliy bn Abiy Xaalib, (Radhiyallahu anhum), a Halifancin Al-mutamid, kuma a lokacin yana shekaru 29 ne, kuma shine dai Baban Mahadi Sha Jira. 2) Malam Shamsuddeen Al-Khalkaan ya faxa a cikin littafinsa na Tarihi wato Taarikh Ibn Khalkaan da Wafayaatul-aya an a juzuinsa na 3, shafinsa na 316, ko a wani bugun juzuinsa na 4, shafinsa na 176, a babin Abul-Qaasim, wanda aka buga shi a Masar, a Maktabar An-nahdhah Al-masariyyah cewa: Abul-Qaasim Muhammad bn Al-Hasan Al- Askariy bn Aliy Al-Haadiy bn Al-Jawaad, Imami na goma sha biyu daga cikin Imamai goma shabiyu, abisa matafiyar Imamiyyah, wanda aka fi sani da Al- Hujjah, kuma shine wanda Shia suke xauka Sha Jira (Al-muntazar) da Al-Qaaim da Al-Mahdiy ………. Haihuwarsa ta kasance ne a ranar Jumaa a tsakiyar watan Shaaban shekara ta 255, yayin da Mahaifinsa ya yi wafati shekarunsa biyar (5) ne, kuma sunan Mahaifiyarsa Khamx wasu kuma suka ce Narjis. 3) Shaikh Abdullah Ash-Shabraawiy a cikin Al-Ittihaaf Bi-hubbil-Ashraaf wanda aka buga a Masar a shekara ta 1316H, shafi na 175, ya kawo cewa: Imami na goma sha xaya daga cikin Imamai shine Al-Hasanul-Khaalis, ana yi masa laqabi Al-Askariy, an haifeshi a Madinah kwanaki takwas da suka wuce daga Rabiiul-awwal 232H (wanda mu anan akwai savani, an haife shi ne a Rabiiuth-thaaniy) kuma yayi wafati (A) a ranar Jumaa kwanaki takwas da suka wuce daga Rabiiul-awwal shekarata 260H, kuma yana da shekaru 28. KUMA LALLAI YA ISHE SHI XAUKAKA CEWAR IMAMUL-MAHDIY AL-MUNTAZAR YANA DAGA CIKIN YAYANSA. An haifi Imam Muhammad Al-Hujjah xan Imamul-Hasan Al-Khaalis, a Saamuraa, daren tsakiyar watan Shaban, shekarar 255H, kafin wafatin mahaifinsa da shekaru biyar. KUMA MAHAIFINSA YA VOYE SHI TUN LOKACIN HAIHUWARSA KUMA YA VOYE LAMARINSA DOMIN RINTSIN LOKACIN DA TSORONSA DAGA HALIFOFIN ABBASIYAWA DOMIN A LOKACIN SUN KASANCE SUNA NEMAN HASHIMAWA, KUMA SUNA SANYA SU A KURKUKU KUMA SUNA KASHESU, kuma suna ganin sun yiwa Gwamnatinsu tawaye, kuma hakan domin kisansu ga wanda yayiwa gwamnatin zaluncinsu tawaye ne. Kuma shine Imamul-Mahdiy (A) kamar yadda hakan sananne ne a cikin Hadisan da suka zo musu daga Manzon girma (S). 4) Ash-Shaikh Abdul-wahhaab Ash- Sharaaniy shima a cikin littafin Al- yawaaqiit wal-Jawaahir a shafinsa na 145, wanda aka buga shi a Masar, a shekara ta 1307 Hijiriyyah ya kawo cewa: Al-Mahdiy (A), shine wanda yake daga cikin Yayan Imamul-Hasan Al-Askariy (A), kuma an haife shi ne a daren taskiyar watan Shaban, a shekara 255, kuma shine zai saura har sai ya haxu da Isa Ibn Maryam (A). 5) Ash-Shaikh Sulaiman Al-Qanduuziy Al- Hanafiy ya faxa a cikin littafin Yanaabiiul- mawaddah a juzuinsa na 2, shafinsa na 276 cewa: Labarin da yake sananne kuma tabbatacce a wajen thiqaat cewar haihuwar Al-qaaim (A) ta kasance ne daren 15 ga watan Shaban a shekara ta 255, a garin Saamura. 6) Hakanan dai Ash-Shaikh Sulaiman Al- Qanduuziy Al-Hanafiy ya kawo a cikin littafinsa Yanaabiiul-mawaddah juzuinsa na 3, shafinsa na 255 ya kawo cewar: Daga Ibn Abbaas, yace: wani Bayahude da ake ce masa Nathal ya zo, sai yace da Manzon Allah (S) : Ya Muhammad zan tambayeka akan wasu abubuwan da suke kai kawo a zuciyata tun da daxewa ……. Har inda yace: ka bani labari akan Wasiyyinka – wanda zai gaji Halifancinka – wanene shi? Domin babu wani Annabi face yana da Wasiyyi, domin Annabinmu Musa bn Imraan yayi wasicin Yushau bn Nuun. Sai yace – wato Annabi (S) – Wasiyyina shine Aliyyu bn Abiy Xaalib, kuma bayansa jikokina Al-Hasan da Al-Husain, wanda sauran Imamai Tara daga Tsatson Al-Husain zasu biyo bayansu. Sai yace: Ya Muhammadu faxa mini sunansu? Manzo (S) yace: Idan Al-Husain ya shuxe – maana yayi shahada – to sai xansa Aliyyu, idan shima Aliyyu ya shuxe sai xansa Muhammad, idan shima Muhammad ya shuxe sai xansa Jafar, idan shima Jafar ya shuxe sai xansa Musa, idan shima Musa ya shuxe sai xansa Aliyyu, idan shima Aliyyun ya shuxe sai xansa Muhammad, idan shima Muhammad ya shuxe sai xansa Aliyyu, idan shima Aliyyu ya shuxe sai xansa Al-Hasan, idan shima Al-Hasan ya shuxe sai xansa Al-Hujja Muhammadul-Mahdiy, to waxannan sune su goma shabiyu …… har dai zuwa qarshen Hadisin. Waxannan kaxan ne daga cikin Hadisan da suka zo a cikin litattafan Sunna akan Haihuwar Imamul-Hujja (A), wanda kuma Shia litattafansu cike suke da bayanin haihuwar Imamul-Mahdiy filla-filla. ABIN LURA Dukkanin waxannan Hadisan a cikin litattafan Sunna suke, kuma daga cikin Manyan litattafansu muutabarai, kuma Magabatansu. Duk mai hankalin da yake saalimi ya duba waxannan Hadisan zai taras cewar lallai Imamul-Mahdiy (A) an haife shi tun fiye da shekaru dubu da suka wuce, kuma yana daga cikin Jikokin Annabi Muhammad (S) da suka fita daga tsatsaon Imamu Husain (A), sannan yana daga cikin Imaman Shia goma shabiyu. Hakanan dai abu ne bayyananne a cikin waxannan Hadisan zamu ga bayan bayyana haihuwarsa da aka yi babu wani Malami da ya kawo wani Hadisi da yake nuna ko Imamul-Mahdiy yayi wafati, abin da ma yake a fili valo- valo shine samun tabbaci daga waxannan Hadisan akan Imamul-Mahdiy zai haxu da Annabi Isah (A). Don haka a cikin waxannan Hadisan da suka zo daga Manyan Malaman Sunna zamu sami abubuwa kamar haka akan Imam Al-Mahdiy (A): 1- An haifi Imamul-Mahdiy tun shekaru 255 ne a bayan Hijirar Annabi Muhammad (S), don haka yanzu Imam Mahdiy shekarunsa 1180 kenan a duniya kuma da haihuwa. 2- Imamu Mahdiy (A) daga cikin zuriyyar Annabi Muhammad (S) yake, kuma daga tsatson Imam Husain (A), kuma yana daga cikin Imamai shima. 3- Samun tabbaci akan lallai Imam Mahdiy (A) gaibah ya shiga irin gaibar da Annabi Isah (A) ya shiga. 4- Lallai Imamul-Mahdiy zai bayyana nan gaba tare da Annabi Isah (A). 5- Samun tabbacin Imamul-Mahdiy (A) zai zo nan gaba ya cika duniya da adalci bayan wannan zaluncin da take ciki. Saboda haka idan mun sami tabbacin waxannan abubuwan a cikin litattafan Sunna, to ina ga irin Jahilan Malaman Wahabiyawa da suke izgili suke cewa wai Duna na Kogo, ko wannan xan Yaron, da dai sauran maganganu na izgili da suke faxa akan Imamul-Hujja (A)?! Lallai ta sauqi sai mu fahimci cewar jahilci ne da taassubanci yayi musu katutu wanda ba inda zai kaisu sai ga yin da-na- sani, wanda kuma qarshensa shine Halaka. Don haka ne da yawa muke cewa; Ahalus- sunna – musamman Wahabiyawa mafi yawansu tamkar Jakuna suke, jakunan da suke xauke da tarin litattafai amma basu san menene a ciki ba, wani lokacin sai mun ce Sunna sun ruwaito kaza da kaza, sai kaga Sunna musamman Wahabiyawa sun fusato da bakinsu na xoyi da wari sun qaryata, nan take idan mu kawo musu littafin da Malamin da juzui da komai sai kaga sun yi tsuru-tsuru sun koma kallon sama kamar xalibin da ya sha bugu a xakin jarrabawa idea taqi zuwa, to daga sannan sai kaga sun zamo Fabuhitallazii kafara! Zamu ci gaba in shaa Allah.
Posted on: Mon, 27 Jan 2014 06:58:19 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015