MARTABOBIN ABUBAKRIN ====================== Hakika acikin wannan - TopicsExpress



          

MARTABOBIN ABUBAKRIN ====================== Hakika acikin wannan alummar ta Annabin Qarshe, babu wani mutum Guda daya wanda ya samu tarin Martabobi irin na Sayyiduna Abubakrin Assiddeeq (rta). Ga wasu daga cikin martabobin kamar haka: 1. Shine wanda Allah ya zabeshi ya fara yin Imani da Manzon Allah (saww). 2. Shine wanda Allah ya zabeshi domin yin rakiyar Annabinsa Fiyayyen Halittu (saww) alokacin hijira. 3. Shine wanda ya sadaukar da dukiyarsa baki daya domin hidimar musulunci. fiye da kowa. kuma tun kafin kowa. 4. Shine yafi dukkan Sahabbai (rta) acikin TSANANIN SON ANNABI (saww). 5. Shine wanda yafi kowa Zurfin Imani da gaskatawa. kamar yadda Allah da Manzonsa (saww) yayi masa shaidar haka. 6. Shine kadai wanda ya bama Manzon Allah (saww) yarsa BUDURWA ya aura. 7. Manzon Allah (saww) yace mai KAI YANTACCE NA DAGA WUTA (ba zaka shigeta ba). 8. Manzon Allah (saww) yayi masa bushara da cewar SHI DAN ALJANNAH NE. 9. Manzon Allah (saww) yakan yi fushi mai tsanani idan an taba Sayyiduna Abubakrin (rta). 10. Manzon Allah (saww) yayi musu bushara dashi da Sayyiduna Umar (ra) cewar sune SHUGABANNIN DATTIJAI NA GIDAN ALJANNAH. 11. Shine Farkon Khaleefan Manzon Allah (saww). zanci gaba daga nan insha Allahu. Ya Allah ka Qara yardarka ga Sayyiduna Abubakrin (rta).
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 10:09:48 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015